Wannan Tashin Hankali Ne Kuma Bala’i Ne
Wani bawan Allah ne, ya kamala karatunsa na jami’a
akan abinda ya shafi harhada sinadarai kuma ya yi sa’a ya fita da saka mako mai
daraja ta daya. Bayan da ya yi hidimar kasa ya gama, ya mika takardunsa na
neman aiki zuwa gurin wani mutum dan siyasa wanda yana ganin zai iya yi masa
hanya ya samu aiki a daya daga cikin manyan kamfanonin mai na kasa, aka yi sa’a
kuwa wannan dan siyasa ya karbi takardunsa ya gani ya ce masa lallai ka samu
sakamako mai kyau, ya ce masa ka zo gobe office din aka sameni.
Bayan da ya koma gida yana mai alla-alla gobe ta yi,
da gari ya waye ya kama hanya zuwa ofishin wannan mutum, yana zuwa kuwa ya yi
sa’a ya taras da shi, wannan mutum ya dauko irin dan karmin katin nan ya yi
rubutu a bayansa, ya dauko ambulan ya saka a ciki, sannan ya sa sitefula ya
matse, ya bashi ya ce ka je Abuja ofishin kaza ka nemi wane kaza ka bashi, ni
zan masa Magana daga nan.
Bawan Allah ya kama hanya zuwa Abuja, ya yi sa’a daman
anbayar da sunansa a wajen masu gadi, nan da nan aka barshi ya isa har zuwa
wajen wanda aka tura shi, bayan ya yi jira wannan mutum ya fito ya mika masa
wannan ambulan, da ya bude ya gani, ya tashi ya gaida wannan matshi ya yi masa
iso cikin ofis, da suka zauna ya karbi takardunsa ya duba ya gani, ya ce lallai
ka samu sakamako mai kyau, sannan ya kawo bandir din dari biyu ya bashi ya ce
ka koma gida bayan sati daya ka dawo. Bayan sati daya da ya koma Abuja, sai aka
yi masa iso ya shiga ofis sai ya tarar da wannan mutum shida wani abokinsa suna
hira, sai ya ce wa abokin nasa ai wannan yaron shi ne wanda nake baka labari,
ya mike tsaye ya gaida shi. Nanma dai suka bashi bandir na dari biyu suka ce ya
koma zuwa wani makon.
Ya dawo gida yana jiran karshen sati ya kama hanyar Abuja,
da lokaci ya yi sai ya kama hanya, yana zuwa ya samu wannan mutum da abokin nan nasa, nanma
dai aka ce masa ya jira kwana uku masu zuwa, inda aka bashi masauki, bayan
kwana uku yana kwance a masaukinsa sai aka buga masa waya cewa ya zo ofis
yanzu, nan da nan ya kama hanya, yana zuwa sai ya tarar da wannan mutumin da
abokinsa da ya tarar da su kwana ki, suka mika masa hannu suka gaisa, suke ce
masa albishirinsa ya yi murmushi ya ce goro, suka dauko Offer aka bashi ya karanta
ya gani sunansa ne, murna da farin ciki basu iya buya daga fuskarsa ba, nan ya
yi hamdala yana godiya ga Allah, ashe bai sani ba tashin hankali ne zai biyo
bayan wannan albishir.
Abokin mutumin ya ce masa muga Ofar ya karba, ya ce
masa ina taya ka murna, ya amsa masa da cewa na gode. Ya ce kaga wannan takarda,
ya ce, e, naganta, ya ce to taka ce, kaine zaka yi aiki a nan, amma kuma fa da
sharadi LALLAI ne zaka bada kanka, ya ce ban gane ba, suka ce masa zaka maida
kanka mace kuma za’a yi tarayya da kai, nan ya ji gumi ya karyo masa hankalinsa
ya tashi, ya ji abin kamar a mafarki, suka ce masa kaga Yaro ba wai zabi muke
baka ba abun da muka gaya maka Tabbas ne sai anyi tunda yake anbuga takarda da
sunanka, amma yanzu abinda muke so da kai ka koma gida zuwa sati mai zuwa ka
dawo idan ka yanke hukunci, suka kawo bandir din dari biyar suka bashi.
Nan fa ya kamo hanya zuwa gida hankalinsa a tashe,
bayan da ya dawo gida kai tsaye ya wuce wajen wannan dan siyasa da ya tura shi
wajensu, ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya gaya masa bai boye masa komai
ba, da wannan mutum ya bude baki sai ya ce SAU DAYAN KAWAI! Nan hankalinsa ya
kuma tashi, ya ce wannan maganar taka tafi tayar min da hankali sama da wadda
suka gayamin. Atakai ce dai wannan bawan Allah yana can yana more
katafaren Albashinsa da sabon gidan da ya mallaka a babban birnin tarayya! Abin
tambaya shi ne shin ya bayar da kansa kamar yadda aka nema ko bai bayar ba . .
. . . . . . . Sanin gaibu sai Allah.
Ya ‘yan uwa wannan fa shi ne bala’I ko masifa da take
zaune ta ke jiran da yawa daga cikin ‘yan uwanmu musamman masu neman aiki a
gwamnatin Tarayya da manyan kamfanoni na gwamnatin tarayya . . . wannan batu ko shakka babu kada ka ji ko dar
haka yake faruwa a kusan Dukkan ma’aikatun da suke da maiko na gwamnatin
tarayya wadan da ake kudancewa dare daya. Ya Allah ka kiyayemu ka karemu daga
wannan tashin hankali, Allah ka yi mana katangar karfe daga fadawa wannan
mummuna lamari, Lallai abin akwai ban tsoro kwarai da gaske Allah ya kiyaye mu
ya kiyaye al’ummarmu.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment