Bikin Sallah Ba Bikin Nuna Tsiraici Ba Ne!
Haka Allah yake ikonsa komai yayi farko tabbas koshakka
babu yana da karshe, haka abin yake ga kowane irin lamari na rayuwa, Bayan
kamala azumin watan Ramadan mai dumbin falala da tarin albarka sai kuma ashiga
shagulgulan bikin karamar sallah. Hakika lokacin sallah karama lokacine na farin
ciki da ciye-ciye da lashe-lashe tare da ziyarar dangi da sada zumunci tsakanin
‘yan uwa da abokan arziki.
Haka kuma lokacin sallah lokaci ne da ya halatta
ashariance asanya sabbin tufafi da fesa turare mai kanshi da sabbin takalma da
dukkan wasu al’amura da zasu nuna wal-wala da jin dadi tare da iyalai ammafa
bisa koyarwar sharia. Amma abin mamaki wani yanayi da muke ciki yanzu ko kuma
zamani na nuna waye da kaiwa matuka wajen nuna burgewa da cigaba. Galibi
lokacin bikin sallah samari da ‘yan mata kan fita ko zaga dangi da ziyarar ‘yan
uwa ko kuma zuwa gurare na shakatawa da gwangwajewa ko kuma zuwa wajen wasu
bukukuwa na gargajiya kamar hawan da masu martaba sarakuna kanyi a fadojinsu
koma wani abin da ba wannan ba cikin shiga ta fitina da tashin hankali.
Abin da kamfaru yayin bikin sallah shi ne galibi da
yawa yara ko kuma samari da ‘yan mata kan soma lalacewa ne a ranar sallah domin
kuwa alokacin bikin sallah ne zaka ga mata da dinkuna na tashin hankali duk wai
domin nuna burgewa, abin takaici shi ne iyaye kan sakarwa ‘ya ‘yansu mara
alokacin bikin sallah suyi duk abin da suka ga dama babu kwaba, ba tankawa.
Galibi abin yafi kazanta acikin birane inda zakaga ana bajekolin futsara da
rashin kunya afili, samari anan ina nufin ‘yan mata kan fita cikin ado da
kwalliya mai dauke da janhankalin duk wani baligi mai hankali, ta yadda wani
lokacin sai ka kasa bambance tsakanin budurwa da matar aure, da yawan ‘yan mata
kan fake da zuwa gun samari da sunan karbar goron sallah inda zaka iske budurwa
ta je dakin saurayi cikin shiga mai motsa sha’awa wai da sunan taje karbar
yawan sallah ne wanda shi kuma idan akayi rashin sa’a mara tsoron Allah ne
yafito da kudi ya nuna mata amma ya ja hankalinta sosai kafin ya bata daga nan Allah
ya kiyaye kaji labarai marasa dadi.
Da yawa daga cikin ‘yan mata kanyi dafe-dafe ga
samarinsu da sunan barka da shan ruwa inda zaka ga dukkansu sunsha ado da
kwalliya inda galibi akanyi amfani da wannan lokaci wajen aikata badala, wata
budurwar idan tayi maka wata shigar zakaga batada maraba da tsirara kuma ta
fita gaban iyayanta duk da sunan murnar sallah, haka kuma abin bai tsaya ga
samari ‘yan mata ba harda kana nan yara inda zaka ga an caba musu ado da
kayayyaki masu ban sha’awa da kayatarwa wanda anan ma ana samun bata gari masu
fakewa da daukar yarinya da sunan zasu bata goron sallah su kaita dakinsu daga
karshe kaji labarin aikata badala da ita; lallai Manzon Allah ya yi gaskiya
inda ya ce a karshen lokaci mata za su ringa yawo da kaya amma a tsirara suke
yace kasiyatun ariyatun .
Kamar yadda nace yara da yawa na fara lalace wane
alokutan da ake bukukuwan sallah domin anan ne kanan yara kan koyi zukar taba
sigari samari kuma da suke dan busa taba kan cigaba zuwa busa tabar wiwi, ‘yan
wiwi da shalisho kuma kan kurba ruwan kamru uwar laifi, haka kuma a wannan lokacin
akan motsa sha’awa tsakani samari da ‘yan mata wai da sunan Happy Sallah, wanda daga
nanne yara kan zarce da fitsara da rashin kunya domin kuwa galibi samari da
‘yan mata kowa da dan kudi a kugunsa sukuma mata ga kwadayi da son abin duniya,
zaka ga yarinya bata iskanci amma arudeta da cewa yau kawai akarshe kaga
shaidan yayi rinjaye yarinya ta bada kanta.
Haka abin yake idan kaje gidajen shakatawa inda zakaga
abin ma yafi muni anan gurin domin guri ne inda kowa bashi da mafadi galibi
abubuwa marasa dadin ji kan faru a irin wadannan gurare na shakatawa, musamman
ma idan akace akwai dan karamin kududdufi da zaka shiga kayi linkaya inda zaka
iske karti mata da maza cikin ruwa wai suna wasa ko kuma yana koya mata ruwa
Allah ya kiyaye.
Haka kuma lokacine da ake fitowa kallon sarki akan fito
cikin ado da kasaita da nuna bajinta da iya kwalliya da yawan iyaye kanbar ‘ya
‘yansu zuwa kallon sarki amma basu san irin illar da hakan kan haifarba domin
guri ne da ake cika mata da maza babu wani guri da aka ware na maza daban ko na
mata daban a gwamatse ake tsayuwa irin munanan abubuwan da suke faruwa a yayin
hawan sallah kunne bazai so jinsu ba.
Anan nake son nayi amfani da wannan dama nayi kira na
farko ga samari musamman ‘yan mata da maza da suji tsoran Allah sudaina shiga
mai bayyana tsiraici da surar jiki, kusani mutuncinku shi ne ku sanya sutura ta
gari wadda zata suturce jiki gaba daya, kuma wallahi kisani ko dan iska burinsa
shi ne ya auri tagari ba sai kin nuna albarkar jikin ki zai sa samari su soki
ba, duk wani saurayi daya rudeki da cewa shigarki tayi kyau kisani wallahi
yaudararki yake yi, Don Allah ayi shiga da ta dace da Addininmu da kuma
al’adarmu kisani komabayan tunani ne kiringa kwaikwayon turawa da indiyawa.
Haka kuma ina kira ga tailoli da suji tsoron Allah aduk
al’amuransu kuma su sani cewa zasu kasance ababen tuhuma ranar gobe kiyama a
wajen Allah, domin sune
suke bada wannan damar ga ‘yan mata ta nuna albarkar jiki, ta hanyar yi musu
dinkuna na tashin hankali.
Abu na uku shi ne Iya ye yaka mata su sani ‘ya ‘ya fa
amana ne Allah ya baiwa kowane magidanci kuma zai yi masa tambaya akan yadda ya
gudanar da harkar iyalansa. lallai ne asanya ido sosai akan yara aga ina suke
zuwa kuma wace irin suturace ke jikinsu kuma su wane suke yawo tare dasu idan
har sukayi haka wallahi sunyi abin daya dace kuma zasu kubuta har gaban Allah,
dafatan za’akiyaye da wdan nan ‘yan shawarwari nawa, kuma Allah yasa ayi bikin
sallah lafiya agama lafiya Allah kuma yasa ibadun da mukayi awatan Ramadan
karbabbune.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment