Mallam Nuhu Ribadu Waliyyi Ne
Sunan Mallam Nuhu Ribadu ya fara bayyana ne a lokacin da ya
jagoranci hukumar yaki da yiwa tattalin arzikinsa zagon kasa da kuma yakar
cin-hanci da rashawa a Najeriya, wadda akafi sani da EFCC, hakika ya nuna kwazo
sosai lokacin da ya shugabanci wannan hukuma, domin ya kama tare da gurfanar da
mutanan da ake ganin baza su iya tabuwa ba a kasarnan, bisa zarginsuko kama su
da yin almundahana da dukiyar kasa. Misali bayan da sashi na 308 na kundin
tsarin mulkin kasar nan ya baiwa masu rike da mukamin shugaban kasa da
mataimakinsa da gwamnoni kariya daga gurfana gaban kowane irin kwamitin bincike
ko kotu, wanda wannan sashi ya taimakawa Muggan barayin gwamnoni Jidar dukiyar
kasarnan suna kaiwa kasashen Turai da Amerika suna jibgewa, duk da haka Ribadu
ya kafa musu tarko, shakka babu wannan ba karamin aiki ya yi ba, ko iya nan ya
tsaya, kwalliya ta biya kudin Sabulu.
Bayaga damke tsohon gwamnan jihar Bayelsa DSP Aliemieghsigha, ya
kuma kama takwaransa na Jihar Delta Mista Jame Ibori wanda ake ganin babu wanda
ya tallafawa takarar marigayi Umaru YarAdua da kudi irinsa, Ribadun karkashin
hukumarsa ya zargesu da zambar kudi kusan dubban miliyoyin daloli, rahotanni
sun nuwa cewa Mista Ibori ya yi kokarin baiwa Ribadu toshiyar baki ta kusan
Dala miliyan goma sha biyar ($15) kimanin Naira Biliyan Uku (N3B) amma Ribadun
yaki karba. Sannan kuma ya fallasa irin adadin kudaden da gwamnoni sukayi
rubdaciki da su a yayin da suke kan mukamansu, misali inda ya bayyana tsohon
gwamnan Jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki ya yi almundahana da kusan Naira
Biliyan 36, da sauran gwamnoni da daman gaske ya yinda wasu kuma suka arce suka
bar kasarnan wanda suka hada da tsohon gwamnan Jihar Edo Mista Locky Igbinideon
da Adamu Mu’azu na jihar Bauchi da sauransu da dama a wancan lokacin.
Mallam Nuhu Ribadu dai shi ne mutumin da ya sa aka sauyawa
Najeriya suna daga ta sahun gaba akan cin-hanci zuwa ta kasas-kasa. Wannan ce
ma ta sanya majalisar dinkin duniya ta zabeshi a matsayin wanda zai binkito
badakar cin-hanci da rashawa da ta mamaye gwamnatin Afghanistan. Hakika aikin
da EFCC ta yi karkashin Jagorancin Ribadu na kokarin tatse mista James Ibori da
mayar da abinda ya sata zuwa asusun gwamnati, aiki ne gagarumi kuma irinsa na
farko a tarihin Najeriya, amma sai dai wannan yunkuri na Nuhu Ribadu ya gamu da
cikas lokacin da Marigayi Umaru Musa ‘YarAdua ya zama shugaban kasa, domin
zamansa shugaban kasa ke da wuya aka fara takawa Nuhu Ribadu birki sakamakon
taba Ibori da ya yi, wanda a lokacin nan yake da uwa a gindin murhu. Dan
shugaban kasa Umaru ‘yarAdua ya sakawa Ibori, ya nemi ya bayarda wadan da yake
son a nada mukamai, inda shi James Iborin ya bayar da sunan babban yaronsa
Mista Micheal Kaase Aoandoakaa a matsayin wanda za’a nada Babban Antoni Janar
kuma Ministan Shari’ah domin ya binne badakar da Ribadu ya bankado ta Ibori,
hakan kuwa aka yi Inda Aoandoakaa ya zama ministan Shari’ah kuma ya lalata
binciken da Hukumar EFCC ta yi karkashin Ribadu, akan me gidan na Ibori.
Wannan ne dalilin da ya sa Shugaba ‘YarAdua Allah ya jikansa a
wancan lokaci da Mista Ibori suka yi ta yiwa Mallam Nuhu Ribadu bita da kulli
kawai dan ya ce a dawo da dukiyar da Ibori ya sata, Ribadu dai yaga takansa,
domin bayan da aka ce ya koma makaranta kuma aka rage masa mukamin da yake da
shi a rundunar ‘yansanda, sannan ma aka ce karatun da ya yi a Kuru dake Jos
haramtacce ne, haka dai Mallam Ribadu ya samu ya sulale ya bar kasarnan domin
tsira da rayuwarsa daga barazanar su Ibori da ‘YarAdua.
Sai ga shi a ‘yan watannin da suka gabata Majalisar kasa karkashin jagorancin kwamitin
Hon. Farouk Lawal ta gudanar da binciken cin-hanci mafi girma a tarihin
kasarnan, inda aka kama manyan mutane da kamfanoni da ci-da gumin talakawa na
kusan sama da Naira Tiriliyan daya, hakika ‘yan Najeriya sun yabawa Farouk
Lawal bisa yadda ya gudanar da wannan bincike kuma ya kama mutane da yawa da
ake ganin bazasu tabu ba. Kwatsam kuma sai gashi daya daga cikin mutanan da aka
zarga Mista Femi Otedola yana ikirarin cewar ya baiwa Farouk Lawal din toshiyar
baki ta kusan dala dubu dari shida da ashirin ($620) kimanin Naira Miliyan tasa’in
da uku (M93), har kuma ya ce yana da faifan bidiyo da yake tabbatar da wannan
ikirari nasa. A karshe dai ta bayyana cewar Lawal ya karbi wannan toshiyar
baki, inda Jaridun Najeriya suka yi ta ya-madidi da wannan batu.
Idan har za’a ce Farouk Lawal da ya jagoranci wancan binciken
cin-hanci mafi girma kuma ya karbi toshiyar baki ta Naira Miliyan 93 kacal ko
$620, to Lallai zamu kwatanta Mallam Nuhu Ribadu da cewar waliyyi ne, domin
kamar yadda muka fada Ibori ya baiwa Ribadu cin-hancin kimanin Naira Biliyan
Uku amma Ribadun yaki karba, inda ya sanar da Babban bankin Najeriya akan
wannan batu. Hakika Najeriya tana bukatar mutane irinsu Ribadu wadan da za’a
basu irin wadan nan makudan kudi da sunan cin-hanci amma su tsallake.
Sai gashi a kwanakinna kuma wata sabuwa ta bulla, inda Andy Uba,
yake ikirarin wadan nan kudi da aka baiwa Ribadu ya ki karba mallakarsa ne. Shi
dai Andy Uba wani irin mugun uban gida ne, domin idan zamu iya tunawa shine
mutumin da ya hana Jihar Anambara zama Lafiya lokacin tsohon gwamna Ingige. Inda
har ya taba sanyawa aka sace gwamnan sukutun saboda yaki yarda da muguwar
manufarsa ta raba kason jihar gida biyu a bashi rabi. Koma dai me ye, wannan ya
tabbatar da cewar Ribadu bai ci wannan kudi ba, kuma indai Farouk Lawal zai
karbi hancin Miliyan 93 kacal to tabbas Ribadu waliyyi ne idan ka kwatanta shi
da farouk.
Lallai Najeriya tana
bukatar shugaba wanda zai yaki cin hanci da rashawa da gaske, irinsu Mallam
Nuhu Ribadu.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment