Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki!
Kamar yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji
Atiku Abubakar ya taba fada a wata hira da ya yi da Jaridar This Day, cewar
tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya buka ce shi da ya zabo masa mutum
mai jini a jika kuma wanda ba shi da tsoro, wanda idan ma ta kama zai iya yin
akuya ga mahaifiyar obasanjon don ya bashi mukamin ministan babban birnin
tarayya Abuja saboda ya dai-daitawa mutane sahu daga karkacewar da ya yi. Atiku
ya shaidawa Obsanjo cewar Nasan wasu mutane guda biyu abokai da Allah bai sanya
sun taba hada hanya da tsoron wani mahaluki ba a fadin tarayyar kasar nan, daya
daga cikinsu kuwa shi ne Nasiru el-Rufai, wanda a lokacin shine shugaban
hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa (Director General Bureau of Public Enterprises (BPE) and the Secretary
of the National Council of Privatisation).
Tabbas Mallam Nasiru el-Rufai ya nuna cewar shi ba
matsoraci bane, lokacin da majalisa ta zo tantance shi a matsayin mutumin da za’a
nada minister. Domin idan zamu iya tunawa anyi dauki babu dadi da el-Rufai
kafin a nada shi minister, inda aka nemi ya bayar da cin-hanci shi kuma ya yi
kememe ya ki bayarwa, wanda wannan ta sanya wasu da yawa daga cikin shugabannin
majalisa a wancan lokacin jin kunya ciki kuwa harda Mataimakin Shugaban
Majalisar Dattawa Sanata Nasir Ibrahim Mantu, inda el-Rufai ya bayyana a
majalisa dauke da al-qur’ani a hannunsa ya yi rantsuwa cewar an nemi hanci daga
wajensa, kuma shi Mantu ya karyata, inda el-Rufai ya bukaci Mantu shima da ya
rantse da Al-qur’ani amma hakan ta gagara inda ya ce shifa bashi da tsarki duk
kuwa da cewar akwai makewayi a majalisar, kusan zamu iya cewa tun a wannan
lokacin el-Rufai ya nuna jarumtaka da tabbatarwa da duniya cewar shifa ba
mutumin banza bane. Wannan namijin kokari da bajinta da el-Rufai ya nuna, shi
ya sa jihar Georgia da ke kasar Amerika ta bashi izinin zama dan wannan jihar,
wanda yanzu haka el-Rufai yana daga cikin ‘yan Najeriya da suke zuwa kasar
Amerika ba tare da anyi musu binciken kwakwaf ba.
Lokacin da Mallam Nasiru el-Rufai ya zama babban
ministan babban birnin tarayya ya nuna babu sani babu sabo. Domin ya kau-da duk
wasu gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba, ciki kuwa harda gidan matar shugaban
kasa marigayiya Stella Obasanjo da gidan shugaban PDP na wannan lokacin Sanata
Amadu Ali da wasu manya manyan kusoshin gwamnati a wancan lokacin. Haka dai
el-Rufai ya ringa sanya gireda yana ma-ke duk wani gini da aka gina shi ba bisa
kai’da ba a Habuja. Mallam Nasiru el-Rufai kusan shine ministan Abuja mafi
dadewa a tarihin wannan birni tun daga 1999 har zuwa 2007, kuma ya yi aiki
dai-dai nasa.
Tun da Marigayi Mallam Umaru Yar’Adua ya zama shugaban
kasa el-Rufai ya tsallake yabar kasar nan inda ya tafi kasar Amerika ya koma
makaranta, ya halarci kwasa kwasai da dama a fannoni daban daban, ciki kuwa
harda katafariyar Jami’arnan ta Harvard, kadan daga Makarantun da el-Rufai ya
halarta sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, Najeryia, Jami’ar London ko
University of London a Burtaniya da Harvard Business School, Arthur D. Little School of Management a birnin
Massachusetts da Georgetown University da School of Foreign Services a birnin Washington
dukkaninisu a kasar Amerika da kuma D.C. da John F. Kennedy School of
Government da Harvard University duk dai a can Amerika. Sannan el-Rufai yana da
babbar Lambar yabo ta kasa wadda ake kira OFR (Officer of the Order of
the Federal Republic of Nigeria) wadda aka bashi tun yana BFE, kuma yana da digirin girmamawa wanda Jami'ar Abuja ta Bashi a 2005 wato Doctorate Degree.
Bayan da el-Rufai ya dawo gida Najeriya,
ya fada Jam’iyyar adawa ta CPC inda ya mara baya ga takarar tsohon shugaban
kasa Gen. Muhammadu Buhari duk kuwa da ana kallon zai goya baya ne ga takarar
babban abokinsa wato Mallam Nuhu Ribadu. A halin yanzu dai Mallam Nasiru
el-Rufai shi ne babban bakaniken jam’iyyar ta CPC wadda Buharin ya dora masa
wannan nauyi na dai-daita sahun jam’iyyar kamar yadda a yiwa birnin tarayya
Abuja, saboda fama da matsaloli da jam’iyyar ta ke yi a kusan daukacin jihohin
kasarnan.
Bayan haka kuma, el-Rufai shi
ne kusan mutum daya tilo wanda tauraruwarsa ke haskawa wajen adawa da gwamnati
mai ci ta Goodluck Jonathan da kuma Jam’iyyar PDP. Mallam Nasir el-Rufai ya
dauki lokaci yana sharhi akan kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012 inda ya
yi kaca-kaca da wannan gwamnatin ya nuna ma basu san me suke yi ba. Hakan ta
sanya el-Rufai ya dinga daukan hankalin jama’a a ciki da wajen kasarnan wajen
yadda yake fashin baki a harkar tafiyar da wannan gwamnatin musamman a harkar
da ta shafi tattalin arziki, wannan ta sanya jami’an SSS suka ringa sanya masa
tarko suna kamashi a kusan duk lokacin da zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje,
haka nan yake tsallake irin wannan turaku da ake sanya masa.
Bahaushe ya ce al-kalami ya fi
Takobi, lallai wannan magana haka ta ke, domin shakka babu wannan gwamnati mai
ci babu wani alkalami da ta ke jin tsoro a kullum kamar na el-Rufai, domin sun
san cewar mai ilimin gaske ne kuma masani ta fannoni da daman gaske. Mallam Nasiru
el-Rufai dai idan ka ganshi irin mutanan nan ne da zaka gansu ‘yan tsirit
wato ba shi da wani cika ido, wannan ce ma ta sanya abokansa suke masa lakabi
da sunan GIANT wato wani babban mutum kamar dai yadda Bahaushe yake ce wa gajere
malam dogo. Lallai kam ya zuwa yanzu babu wani daga cikin ‘yan Adawa wanda
tauraruwarsa take haskawa kamar el-Rufai ba, kuma duk wannan ya faru ne ta
sanadiyar al-kalaminsa da yake caccakar wannan gwamnati da shi. Tabbas maganar
Bahaushe gaskiya ce da ya ce Alkamai ya fi takobi, domin idan da fada za’a iya
da takobi watakila da farat daya za’a gama da el-Rufai amma da yake fadan na
alkalami ne, babu yadda aka iya da shi sai dai a kayar da shi da hujja idan ana
da ita.
Lallai Najeriya tana bukatar
mutane masu gaskiya wadan da zasu iya yakar cin-hanci da rashawa da gaskiya
kuma hazikai irinsu Mallam Nasiru el-Rufai.
Yasir Ramadan
Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment