Musulmi Allah Ya
Bamu Hakuri
Ya ‘yan Musulmi a
cikin alkur’ani mai tsarki a sura ta 29 aya ta 2, Allah maigirma da daukaka
yana cewa “shin tsammaninku dan kunyi Imani bazamu jarrabeku ba” hakika Allah
ya jarrabi wadan da suka gaba cemu da tsanani da musiba da tashin hankali, har
sai da sahabbai suka ringa tambayar Manzon Allah shin yaushe ne nasarar Allah
zata zo? Manzon Allah ya ce ku sani Nasarar Allah a kusa take.
Ya ‘yan uwa
wannan abin da ya faru ba sabo bane, sannan kuma ba abin mamaki bane. Idan zamu
iya tunawa a shekarar 1988 wani marubuci dan Asalin kasar Indiya mazaunin kasar
Burtaniya mai suna Ahmed Salman Rushdie ya taba rubuta wani littafi mai suna THE
SATANIC VERSES wai shaidanun ayoyi a cikin al’qur’ani. Wannan littafi da wannan
la’anannan mutum ya yi ya tayar da kura a daukacin kasashen Musulmi a wannan
lokaci, inda da yawa daga cikin manyan malaman musulunci suka fitar da fatawar
da take halasta jinin Salman Rushdie.
Wannan littafi
karara karyata manzon Allah ne cin-fuska ne wa Musulmi baki daya. Amma saboda
turawa makiya Allah ne makiya gaskiya wai ta dalilin wannan aka karrama Salman
Rushdie da lamabar yabo mafi girma a duniya ta SIR, inda kuma aka bashi
cikakkiyar kulawa a kasar Burtaniya, Allah ya la’anci Rushdie da ire irensa.
Daga cikin
abubuwa na tashin hankali da suka samu Musulmi a wannan makon shi ne wayar gari
da akayi da samun wani fim da yake nuna surar Manzon Allah Salallahu Alaihi
wasallam, wanda wasu shedanu makiya Allah makiya zaman lafiya suka shirya,
wanda kuma suka samu goyon baya daga muguwa annamimiya kasar Amerika. Ya Allah
ka La’anci Dukkan masu cin-zarafin Musulunci da Musulmi. Haka nan tarihi ke
maimaita kansa dangane da irin yadda wadan nan makiya Allah suke cin zarafin
Musulunci.
Ya ‘yan uwa mu
tuna Sahabin Manzon Allah mai daraja AMMAR BIN YASSIR. Shifa Ammar ba wai zagin
manzon Allah akayi dan ya ji haushi ba, a’a kama shi aka yi aka ce shi da kansa
ake son ya zagi manzon Allah! Ya ‘yan uwa shin akwai abinda ya kai wannan
tashin hankali da firgici! Shin idan da kaine Ammar a wannan lokacin ya zaka ji
a ranka? Haka nan Ammar ya aikata zuciyarsa tana cike da damuwa da bacin Rai da
tashin hankali, ya zo ya Baiwa manzon Allah labara, manzon Allah ya tambayeshi
shin ya kaji a Ranka? Ya shaidawa manzon Allah cewar yaji tashin hankali da
damuwar da bait aba ji ba a rayuwarsa.
Shakkak babu
wannan abinda ya faru abin bakin ciki ne da damuwa da tashin hankali. Ya ‘yan
uwa wannan ba zai zama sanadiyar da zamu afkawa mutunan da basu jiba basu gani
ba, mu sani cewa Allah ya riga ya bamu hakuri, Manzon Allah ma ya bamu hakuri.
Mu nuna fushi da damuwarmu ta hanyoyin da suka dace da shari’ah.
Allah ya huci
zuciyarmu
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment