Tururuwa! Wata halitta ce daga nau’ukan kwari da Allah
madaukakin Sarki ya halitta bisa hikima da ikonSa. Shi ‘Al-Khaliku’ ya fi kowa
sanin dalilinsa na tsara dabi’un Tururuwa a yadda suke, to amma ba shakka akwai
ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da wasu
mu’ujizozi da Allah ya kebanci tururuwa da su, wanda dole hankali ya yarda cewa
Allah ya yi su ne don su zamo ayoyi, kuma abin lura da tunani ga mutane.
Tururuwa ta
sha bamban da duk wasu halittu na kwari da dabbobin da Allah Ta’ala ya halitta,
domin salonta, hikimominta, tsarin gudanarwarta, zubin siyasa da tafiyar da
al’umarta, ayyuka tukuru da sadaukarwarta, suna bayyana zunzurutun iko da
iyawar Allah ne, a gefe guda kuma suna fassara Mu’ujizozi da fifikonta bisa
sauran kwari da dabbobi da Allah Buwayi gagara misali ya halitta. Da yawa daga
cikin dabbobi suna da wata baiwa ta hali ko dabi’a ta musamman, wanda bisa
nazari dan Adam zai iya daukar darasin rayuwa a cikinta. Misalin hakan shi ne
zuma, malam-buda-man-littafi, kurciya, gara, kiyashi, zaki, kyanwa da sauransu.
A cikin yin hakan kuwa babu wani kaskanci ko fifikon wadannan dabbobi a kan dan
Adam din. “Hikima kayan muminini ce, duk inda ya gan ta sai ya dauki abinsa,”
in ji hadisi.
Kowane
janibi na rayuwar tururuwa akwai darasi abin koyi a cikinsa, to amma bari mu
dauki darasin sadaukarwa mu yi magana a kai, mafi yawan tururuwai sukan kai
dubu 500 zuwa miliyan guda a duk inda suka mamaye a matsayin yankinsu, suna da
tsari na kowa da aikinsa ‘Division of Labour’, suna da ‘Supervisors’ wadanda za
su binciko inda ya dace a kafa gida don yin sansanin zama. Akwai wadanda za su
rungumi aikin gina gidan da tsara shi sashi-sashi. Sukan samar da dakuna da
bangarori sama da 500 a gidan nasu. Akwai masu yanko ganyayyaki da dauko su don
kawo wa masu gini, wato ‘Leaps Scatters’, a tare da su akwai kananan tururuwai
masu ba su kariya daga duk wani farmaki da ka iya zuwa ta sama ko kasa
(musamman na zuma). Wadannan dakaru ’yan-ta-kife ne, a kodayaushe suna cikin
shirin yin ko ta kwana ko shahada.
Babu wanda
zai iya hana kansa yin mamaki saboda ganin shurin tururuwa a gine a kasa, wanda
tururuwai suka gina. Dalili kuwa shine shurin tururuwa gini ne mai ban al’ajabi
wanda tsawonsa ya kai mita 5-6. a tsakanin shurin akwai nagartaccen tsarin dake
kula da dukkan bukatunsu wanda ba zai taba sanyawa su fito cikin hasken rana
ba, saboda yanayin jikinsu. A cikin shurin, akwai tagogi na shan iska, dakunan
haihuwa, gidaje, farfajiyoyi, wurin samar da makarai na musamman, kofofi,
dakunan zama lokacin zafi dana hunturu ; a takaice dai, akwai komai a ciki.
Abin mamaki da wadannan tururuwan da suke gina wadannan shurika shine
kasancewar su makafi, domin duk tururuwar da ka sani ko ka ke gani to bata
gani da ido. Abu na biyu na mamaki game da tururuwa shine, idan muka kwatanta
girman tururuwa da shurinta zamu ga cewa, tururuwan sunyi nasarar gina wani
gini wanda ya nunka su girma sama da sau 500.
Haka kuma,
a cikin al-qur’ani mai tsarki Allah ya saukar da suru sukutum da sunan
Tururuwa, wato Suratul Naml wadda ita ce sura ta ashirin da bakwai (27) a cikin
jerin surorin al-qur’ani; kuma Allah ya bamu labarin cewa Tururuwa ta yi magana
da ‘yan uwanta lokacin da Annabi Sulaimanu ya zo wucewa, inda ta bukaci al’ummar
tururuwai su shiga gidajensu . . . Shakka babu banda ikon Allah babu mai iya
haka, domin ka duba kankantar tururuwa amma ta yi magana. Har ila yau, suna da
wata kasaitacciyar sifa: idan da zamu raba shurin gida biyu, gidan farko shine
na ginin, daga sama hanyoyin, dakunan da titunan sunyi kama da juna. Kuma da
za’a mayar da wannan rabin to zuwa wani dan lokaci hanyoyin da gidajen zasu
koma su hade dai-dai kamar ba’a taba rabasu ba, kuma tururuwan Zasu cigaba da
harkokinsu kamar basu taba rabuwa da juna ba.
Tafiyar saka na tarihin
tururuwa a irin wannan hali, tsari, dabi’a da salo nata, bisa binciken
‘Shatter’ na tsawon shekaru sama da miliyan dari takwas da suka shude, wanda
mahaka tarihin dan Adam suka yi, ya zamo daya daga cikin hujjjoji masu karfi na
karyata akidar ‘Theory of Evolution’ wato Ka’ida juyin halitta da wasu masanan
falsafa ke da shi, kuma da wannan tarihi na tururuwa ne aka samar da wani babi
mai kanu ‘The Evolution misconception’. Wato Jahilcin masana Ka’idar Juyin
Halitta.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment