Sunday, September 9, 2012

Kaunar Manzon Allah Salallahu Alahi Wasallam



Kaunar Manzon Allah Salallahu Alahi Wasallam


Sheikh Jafar Mahmoud Adam

Bayan haka, Ya ‘Yan uwa, Hadisi ya tabbata daga Nana A'isha bint Abi Bakr (R.A), tana hakaito wani yini da Manzon Allah (s.a.w) ya tsaya a tsakanin sahabbansa yana mai basu labarin wani abu daga cikin abubuwan mamaki daga cikin abubuwa na gaibu, wanda Allah (M) ya nuna masa daga cikin abin da zai zo a gaba har abinda yake cikin Aljannah da wuta. Yana cewa :

"Babu wani abu wanda ban taba ganinsa ba, face yanzu dinnan ina ganinsa har ma abin da yake cikin wuta da Aljannah".

Wannan daya ne daga ukun manyan dalilai da hujjoji da suke tabbatar da Manzancinsa da kasancewarsa badadi na Allah, ta yanda Allah (M) ya kebance shi da sanar da shi, da sanar da shi wani ilmi na gaibu irin wanda ba a saninsa sai ta fuskar wahayi ga wani wanda Allah (M) ya kebance shi ya zabe shi. Allah (M) ya nuna masa Aljannah da wuta ya kuma nuna masa dangin ni'imomin da ke a cikin ita Aljannah din, sannan kuma ya nuna masa irin dangogi na azabobi da wahalhalu da ke a cikin wuta. Duka wannan an nuna masa ne alhali yana a farke ba a cikin barci ba wato (mafarki).

Hakika wannan mu'ujiza ce cikin mu'ujizozin da Allah ya yi masa. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: 

" Hakika an yi mani wahayi cewa lalle, ku, za a fitine ku a cikin kaburburanku, irin, ko kusa da fitinar masihul Dajjal".

Abin da ake nufi da fitinar kabari a nan ita ce tambayoyin da za a yi wa kowane daya daga cikinmu (mazanmu da matanmu). Ita kuwa fitinar Dajjal ba karamar fitina ba ce domin irin yadda tasa da yawa daga cikin mutane suka halaka; ta hanyar nuna musu irin abubuwan da ido bai saba da ganinsa ba; ko kuma bai taba jinsa ba. Misali kamar ya tashi idon makaho ya warke, ko ya tayar da matacce daga kabarinsa, da sanya abubuwa su faru, sannan ya yi da'awar Allantaka, wasu mutane kuma su bishi. Kuma ya zagaye duniyan nan a cikin kwanakin da ba su wuce arba'in ba, ya shiga ko wane gari in ban da Makka da Madina, wadanda Allah (M) zai kiyaye su da Mala'iku wanda suka zagaye su ( Makka da Madina). Sai dai wanda duk zai bi Dujjal zai fito wajensu domin ya bishi.

Daga Hadisin za mu iya fahimtar cewa Manzon Allah (s.a.w) yana buga misalin yawan wakanda za su fitinu a kaburbura cewa sun kai kwatankwacin yawan wadanda za su bi Dujal. Ya ci gaba da cewa za a tayar da mutum a tambaye shi cewar : Me ka sani game da wannan mutumin (Watau Manzon Allah (s.a.w) ). Amma mumini sai ya ce shi ne Muhammadu Manzon Allah (s.a.w) ya zo mana da hujjoji da shiriya, sai muka amsa, muka yi imani da shi, kuma muka yi masa biyayya". A cikin duka abin da shi mumini zai ambata akwai imani da biyayya, ko da kuwa bai taba yin kasida ko guda daya ba ga Manzon Allah (s.a.w). Abin da kawai aka bukata shi ne cika zuciya da kaunarsa ta hanyar yi masa biyayya, da ganin mutumcinsa, da girmansa fiye da dukkan wani dan Adam da aka yi a da ko za a yi a nan gaba. Saboda haka ba ya bin wasu tafarki, hanyoyi ko dariku da dokokin da basu da asali, face tafarkin shiriya ta Manzon Allah (s.a.w) a nan za mu iya fahimtar cewa imani kadai ba ya wadatarwa sai da aka yi masa biyayya. Biyayya a cikin akida, ibada, dabi'u da ma'amalolinka duka su kasance yadda ya koyar ne a cikin hadisansa ingantattu, ba irin wanda aka kirkira ba, hadisai raunana, da maudu'ai ko Isra'iliyyat ba. Dukkan nau'ukan ibadarka kamar sallah, zakkah, zikiri, istigfari su kasance irin wanda Manzon Allah (s.a.w) ya yi ne ko ya yi umarni a yi, ba irin wadanda wasu mutane suka kirkiro ba ne bayan mutuwarsa (s.a.w). Ya kasance dukkan dabi'unka, halayenka, cin abincinka, kwanciyarka, tafiya, magana da sauransu kana kwaikwayon irin na Manzon Allah ne (s.a.w). wanda duk ya kasance ya yiwa Manzon Allah (s.a.w) irin wannan son, biyayya, da imanin sai mala'iku su ce da shi:

"Kwanta (ka huta) kana salihi muna da masaniya (ta fuskar takardunka dake a wurinmu) cewa dama kai mai yakini ne da Manzon Allah (s.a.w).
Manzon Allah (s.a.w) ya ce :

"Amma munafiki ko mai shakka (mai raba kafa) sai ya ce: Ban sani ba, na ji kawai mutane suna cewa kaza sai na ce" .

Watau a nan duk abinda ya ji mutane suna yi ko cewa sai ya yi misali idan sun yi kida, ko waka, da sauransu sai ya yi ba tare da ya tsaya ya yi bincike ba ya samu wayewar kai daga Ayar Alkur'ani ko Hadisi ingantacce a kan yadda zai bi tafarki na gaskiya na Manzon Allah (s.a.w) ba. Shi dai kawai "mukalladi" ne watau mabiyi ne kawai ga malamai da shehun nai ba a kan hujja ko gaskiya ba, saboda haka ya kamata ‘yan uwa mu fahimci cewa Alkur'ani da hadisai ingantattu su ne ma'auni da ake gane akida ta gaskiya, da ibadoji, halaye da dabi'u na gari. Abin da duk ya yi daidai da su wannan shi ne shiriya, abin da duk kuwa ya saba masu shi ne bata, kuma shirme, komai girman ilmin wadanda suka yi riko da shi suna kiran mutane a kan su wajibi ne mu nisance shi.

Ya ‘yan uwa lallai Allah (M) ya zabi Manzon Allah (s.a.w) ya sanya shi ya zama shi ne karshen Annabawa, kuma karshen Manzanni. Babu wata shiriya sai wadda ya zo da ita, haka kuma babu wani alkhairi sai ga wanda ya yi riko da abin da ya zo da shi. Kuma Ubangiji ya lamuncewa wadanda suke yi masa biyayya cewa:

" Idan har ku ka yi masa da'a to za ku shiryu".

Ya ‘yan uwa! Da yawa daga cikin mutane suna tsammanin cewa tsira tana samuwa ne ga wanda kawai ya furta yana son Manzon Allah (s.a.w) wasu kuma suna tsammanin cewa za a samu matsayi da martaba a Aljannah gwargwadon baitoci na wake da mutum ya shiryawa Manzon Allah (s.a.w) da kida ko babu kida, a tsammaninsu ko da kuwa mutum bai yi riko da sunnarsa ba, ko da mutumin ya saba masa a addini, watau a ibada, dabi'u, aiki da mu'amaloli da sauransu. Alhali ita soyayya bata tabbata ta hanyar kudurtawa a zuci kawai face an gauraya ta da wasu abubuwa masu muhummanci, wadanda idan babu su to, soyayyar za ta zamo ba ta gaskiya ba ce, kuma ta shirme ce kawai. Wadannan abubuwa kuwa su ne :

1- Imani da shi (Manzon Allah (s.a.w)) da imani da manzancinsa

2- Aiki da sunnarsa tare da koyi da shi

3- Gabatar da zancensa a kan na kowa, komai girmansa, waliyantakarsa, ko malantakarsa.

4- Takaituwa ga hujjarsa. Ba zai taba yiwuwa mutum ya ce yana sunnarsa, kuma yana darikar wani shaihi ko waliyi ba. Domin duk wani wanda ya samu shi ne gwargwadon yadda ya yi riko da sunnar Manzon Allah (s.a.w) ; ba tare da garwayata da shirkoki, bidi'o'i ko al'adu ba.

5- Riko da wasiyyarsa (s.a.w) inda yake cewa : " Ku bi tafarkina da tafarkin sahabbaina". Saboda haka dole ne mu yi ko yi da abin da suka aikata, ko suka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w). Amma duk abin da ba su yi ba, mu kuma muka kawo shi muna kokarin sai mun mayar da shi addini, to ba komai muke yi ba, face kokarin cin gyaran ko tuhumar Annabi (s.a.w) da sahabbansa cewar ga wani abin alheri a addini wanda su suka ki yi, ko suka manta ba su yi ba.

6- Biyayya gare shi (s.a.w) da sallamawa cikakkiya ga duk wani abu, ko kaso shi ko da kuwa kana kinsa. Ya kasance hujjarka kawai ita ce shin ya inganta daga gare shi ko kuwa? Ba tare da cewar kuma wane ai yace kaza (daga shaihinnai ko waliyyai ba) domin idan ana maganar Manzon Allah (s.a.w) wane ne kuma za a yi maganarsa?

7- Sannan ya kasance kuma mutum bai samu wani kaikayi ba a zuciyarsa a yayin da ya yi da'a ko biyayya ga Manzon Allah (s.a.w). Domin fadarsa Madaukakin Sarki :

" Na rantse da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai yin hukumci a cikinsu ga abubuwa da suka gudana tsakaninsu na sabani, sannan basu samu wani kaikayi ba ga abin da ka yanke (na hukumci) kuma su mika wuya, iyakar mika wuya".

Ya kamata mu sani cewa a duk duniya babu wanda yake da adadin masoya irin Manzon Allah (s.a.w), domin in dai so ne kawai ba tare da da'a ko biyayya ba, hatta da yawa daga cikin kafirai na duniya a yanzu da kuma a da sun so Annabi (s.a.w). Na nesa da na kusa, wanda ya ganshi da wanda bai ganshi ba. Mu sani cewa da a ce ita soyayya kadai tana wadatarwa ga shiga Aljannah (ba tare da da'a da biyayya ba) lalle da Abu Talib yana cikin wanda suke cikin wanda za su zama na farkon a shiga Aljannah, domin a tarihi da wuya ka samu wanda ya nunawa Manzon Allah (s.a.w) soyayya irinsa, har ma tare da ba shi kariya.

Hakanan da yawa daga cikin kafiran kuraishawa, wadanda domin tsananin soyayyarsu gare shi har suka sanya masa suna " Al Amin" wataun amintacce. Saboda haka ba su tabSa shakkar gaskiyarsa ba. Allah Madaukaki Sarki ya ce:

" Lalle su ba su karyataka, sai dai su, azzalumai da ayar Allah ce suke musu". Wannan ya sanya soyayyarsu kawai ta zuci ce wacce ba za ta amfanar da su ba, domin ba su garwayata da yi masa da'a da biyayya a cikin addinin ba.

Haka kuma idan muka duba cikin Alkur'ani za mu ga cewa ayoyin da suke umarni kan yin da'a ga Manzo (s.a.w) kamar :

"Kuma ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa".

"Wanda duk ya yi da'a ga Manzo (s.a.w) hakika ya yi da'a ga Allah".

" Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo (s.a.w) kar ku yi jayayya".

" Wanda duk ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a gare su, daga cikin Annabawa da masu gaskatawa, da shahidai...".

Wadannan ayoyin da kuma wadanda suka yi magana a kan yin imani da bin Manzon Allah (s.a.w) misali:

" Ku bi abin da aka saukar zuwa gareku".

Wadannan ayoyi sune suka fi yawa a cikin Alkur'ani fiye da wadanda suke nuna soyayya gareshi. Dalilai kuma, idan ance da'a, biyayya da imani wasu abubuwa ne da so baya tabbata sai da su, shi ya sanya aka maida hankali wajen yin bayaninsu. Haka kuma, da an ce so ne tsuransa, sai ya kasance musulmi ya yi tarayya da kafirai ne na da da na yanzu a cikinsu, domin kuwa har yanzu akwai kafirai na duniya da suke jinjinawa Manzon (s.a.w). Misali akwai "Micheal Hart" wanda ya rubuta littafin mutane dari (100) da suka ci nasara a duniya, ya sanya Manzon Allah (s.a.w) cewar shi ne na daya, wannan ba zai sa shi ya samu aljannah ba, domin bai yi imani da shi ba ta hanyar yi masa da'a da biyayya.

Wannan abu shi ne da yawa daga cikin mutane a yau suke da bukatar a wayar musu da kai. Lalle mu fahimci cewar ko yake akwai ayoyi da hadisai da suka yi umarni da soyayya ga Manzon Allah (s.a.w) za mu iya fahimtar cewar ayoyi da hadisai wadanda suka yi umarni da yi masa da'a da biyayya a (cikin addini) sun ninninka na soyayyar sau tarin yawa. Saboda haka samun tsira yana tattare da imani biyayayya da da'a a gare shi, bayan tabbatar da kaunarsa (s.a.w). Allah ya sa mu da ce.

Wannan khuduba ce da Babban Malaminmu Sheikh Jafar Adam Kano ya gabatar a lokacin Rayuwarsa, a masallacin Juma’a na Dorayi. Allah ya jikan Mallam ya gafarta masa ya sanya al-jannar firdausi ta zama makoma a gareshi.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



No comments:

Post a Comment