Hukuncin Wanda Ya Yi Kisan Kai Bisa Ganganci
Tare da
Shiekh Ja'far Mahmoud
Adam
Ya yan uwa musulmi, yana daga cikin manufofin shari'ar musulunci
tsare rayukan bil'adama tsare jinin su, don haka ne nassoshi suka zo
acikin alkurani mai girma da abin da ya inganta na hadisan manzon Allah
salallahu alaihi wasallam, wadan da suke nuna haramcin jinin bil'adama mu
samman dan adam musulmi.
Ubangiji ta'ala ya yi wannan bayani ta hanyar salon zance
da ban da ban, ta hanyar nau'ikan magana da ban da ban, Salon zan ce na
farko. Ubangiji ta'ala ya wajabta kisasi (ramuwar gayya) ga dukkan wanda ya kashe
musulmi da ganganci, hukuncin sa shi ne a kashe shi, dukkan wani mutum da ya
kashe musulmi da ganganci ya yi amfani da wani abu wanda ya iya zare rai, ya
nufi dan uwan sa musulmi ya aiwatar da wannan makamin akan sa har ya kashe shi,
to shi ma akamashi a kashe shi ko shi kadai ne, ko su da yawa ne, sai dai fa
idan dangin wanda aka kashe musu dan uwan su suka ce sun yafe, zasu karbi diyya,
to sai a basu diyya.
To amma idan ba hakaba hukuncin su da Ubangiji Ta'ala ya
nassanta shi ne kisasi, ko da mutum daya ne, ko biyu, ko uku, ko sama da haka,
sukayi taron dangi suka kashe mutum daya, kuma hakan ya tabbata, ta hanyara
tabbatar da laifi a addinance, a musulunce, hukuncin su shi ne akamasu a
kashe su gaba dayan su; Kamar yadda aikin Umar bin Khaddab ya nuna lokacin
da wani adadi na wasu mutane suka yi taron dangi suka kashe wani mutum
daya su kadai, Umar ya ce a kashesu su duka, wadansu suka yi masa inkari da
cewa ya ya za a yi ace a kashe rayuka da dama bayan rai daya suka kashe, Umar
ya ce wallahi inda mutanan birnin san'a za su hadu su kashe rai daya to wallahi
da na kashe su gaba daya.
Hikimar hakan cikin shari'ar musulunci, shi ne in da ace ana yin
kisasi ne kadai idan mutum ya kashe mutum daya za'a kashe shi, sai wanda
zai yi kisan ya raba goran gayyata ga abokansa, ko yan uwansa, su je, su kashe
wane, don sun san insunyi baza a kashe suba, gobe kai ma idan kana jin
hashin wani sai karaba goran gayyata ga wadan da zasu taya ka fada domin
kuje ku kashe wane. Wannan sai ya bayu zuwa ga hasarar rayuka, amma idan mutum
biyu ko uku ko sama da haka sukayi haka aka kashe su,wannan zai sa dukkan wani
da da wani ya rabawa goron gayyata cewa zaka rakani in kashe wane to bazai je
ba saboda yasan idan ya aikata hakan to zai bayu zuwaga akashe shi, don haka
sai rayukan mutane su zauna cikin aminci. Allah ta'ala yana cewa "lallai
kuna da tabbatacciyar rayuwa a cikin kisasi matukar an tabbatar da kisasi a
bankasa, wanda duk ya kashe wani da ganganci da kowanne irin dalili cikin
dalilai to shi ma za'a kama shi a kashe shi" to wannan sai ya bayu zuwa ga tsare rayukan
mutane, kisa ba zai yaduba a bankasa da kowanne irin dalili cikin dalilai.
wannan salon magan na farko kenan.
Salon magana na biyu, Ubangiji Ta'ala ya
saukar da narkon azaba da firgitarwa da rudarwa da kidimarwa ga dukkan
mutumin da ya kashe mumini da ganganci yana ji yana gani sakamakon sa wutar
jahannama, zai dawwama a cikin ta ubangiji ta'ala ya yi fushi da shi, ya tsine
mashi, sannan yayi masa tanadin azaba maigirma. kaji irin wannan firgici, ka ji
irin wannan razani, ka ji irin wannan tsawa, da ya sauka cikin suratul Nisa'i
domin aja hankalinka aja hankalina kada kayi dukkan wani yunkuri na zubar da
jinin dan uwanka musulmi bisa ganganci.
Salon magana na uku, Ubangiji Ta'ala ya nuna
cewa duk wanda ya kashe mumini da ganganci, to baya cikin siffofin muminai
nagari, wadan da ubangiji ta'ala ya jero siffofin su a cikin suratul furqan a
inda Allah ta'ala yace "sune wadan da basa kiran wani tare da Allah, suna
kiran Allah ne kadai dan jawo amfani ko dan ko dan dauke musu wata cuta, sannan
ba sa kashe wata rai da Allah ya haramta kisan ta sai ta hanyar gaskiya da
adalci”. Sannan kuma cewa mumini baya kisan kai, wannan dalili
ne da yake nuna cewa idan kuna son kalmar adalci ta tabbata a kanku to kuyi
iyakar kokarinku na tsare jinin yan uwan ku musulmi.
Sannan salon magana na gaba, Ubangiji ta'ala
ya danka amana ko ya bayara da iko a hannu wadan da aka kashe wa dan uwa da
ganganci, dangin duk wanda aka kashe bisa ganganci. Haka ya ce ya basu iko duk
wanda aka kashe bisa ganganci ya bada dama ga yan uwan sa, a hannun dangin sa
ko makusantan sa, wannan iko kodai su nemi a basu diyya, ko su nemi a kashe
wanda da ya kashe musu dan uwansu, Allah ya basu kowacce daya daga cikin biyun
nan a matsayin zabi in suka zabi na farko ya yi in suka zabi na biyu ya yi.
Bayan haka ubangiji subahanahu wata'ala,
ya nuna tsare jinin mumini, tsare jinin musulmi, kare jinin dan uwanka musulmi,
wannan daya ne daga cikin wasiyyoyi guda goma da Allah ya kebanci al-ummar
manzon Allah dasu, wadan da suka zo a jere cikin "suratul An'am" Ya ‘yan
uwa musulmi! Manzon Allah sallalahu
alaihi wasallam, ya labarta mana cewa dukkan wani mutum da ya kashe dan uwansa
da ganganci, to za a zo dasu, ranar alkiyama sai wanda aka kashe ya rike wanda
ya kashe shi, hannun sa yana kan zankonsa ya ja shi sutafi gaban Ubangiji
Ta'ala ya ce ya ubangiji tambayi wane, me nayi ya kasheni? Alokacin da zai fadi haka jijiyoyin wuyan sa
suna furzar da jini domin a halartowa da makshin munin hotan abin da
ya akata a gidan duniya, yace tambayi wane me nayi ya kashe ni akan wanne
dalili? banbancin siyasa, ko addini, ko manufa, zai ce ya ubnagiji
tambayi shi me nayi ya kashe ni. Haka hadisi ya tabbata acikin Sinanu
Nisa'i wanda ya ke hadisi ne sahihi.
Ya yan uwa musulmi, addinin musulunci a
lokacin da yake haramta kisan kai, ba wai yana haramta zubar da
jinin muminai ba kadai! a a hatta daga cikin kafirai wanda shariar musulunci ta
kare masu jinin su da dukiyoyinsu, to in ya zamto dokokin Allah da ya saukar ta
haramta zubar da jinin wanda bai furta kalmar shahada ba, jinin wanda ya
ce Allah uku ne, wanda ya ce Uzairu Binullah! To ya ya kima da
daraja da tsada ga jinin wanda ya ce ya shaida babu abin bautawa bisa cancanta
da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzan Allah ne.
Haka kuma, kafiri wanda kuka yi yarjejeniyar zaman lafiya tsahon
wasu shekaru kan cewa ba za ku yaki juna ba a iya wannan sheakarun na
yarjejeniya, to haramunne ka kashe daya daga cikin su ko ka kwace dukiyar sa,
sai wadan da kuka yi yarjejeniyar basu rushe ko wanne irin sharadi ba
na yarjejeniyar, kuma baku tallafawa
wasu ko wani akan ya yake su ba. To, irin wannan, ku tsare masu alkawarin su na
tsahon lokacin da kuka yi alkawarin da su, alokacin inda zaku kashe wani kafiri
to wanda yayi kisan, Manzan Allah ya ce tsakanin sa da Al-jannah tshon tafiyar
shekara dari biyar, haka ya bayyana acikin hadisi sahihi, ga shi kuma arne ka
kashe ba musulmi ba, to ina ga dan uwanka musulmi! Ka dauki bindiga da kowanne irin dalili cikin
dalilai ka rabashi da rayuwar sa, to kai kuma kayi me a bankasa? kuma mu duba
muga "Al-mu'utamalun" wadan da yaki tsakanin ku da kasar su wanda
akace inda daya da ga cikin su ya nemi izinin zuwa kasar ku, kuma ku ka bashi
dama ya zo yayi iya ka kwanakin da zai yi, to wajibine ku tsare masa jinin sa
da dukiyar sa har ya gama iyakar kwanakin da zaiyi, kuma ku yi masa rakiya har
sai kunje inda zai ji ya amintu daga gare ku. Wannan ya na nuna kulawar shari’ar
musulunci da dokokin Allah dangane da tsadar rayuwar biladama, ko da ya ki da aka
shar’anta mana ba wai an halarta mana shi ne kawai don malalar da jinin kafirai
ba, manufar shar’anta yaki ne idan kafirai suka furta kalmar shahada bisa ga
zabin su sai a kyale musu jinin su, wannan tasa idan kafirai sukaki su furta
kalmar shahada amma zasu shiga cikin "amman dinku" wato karkashin
gwamnatinku, ku kyale su akan addinin su, baza ku kashe su ba. Ashe da manufar
itace kisa to da idan amfito sai an kashe mutum koda ya yi kalmar shahada, sai
ace ai anriga anfito lokaci ya kure me yasa yaki yi kafin a fito, da manufar
itace kisa to da babu yadda za'a ce an samu wasu kafiran amana wadan da zasu
zauna karkashin daular musulunci, kuma a tsare musu jinin su da dukiyar su ba
tare da anribace su ba.
To wannan ya nuna cewa addainin musulunci addini ne da
yake kare rayuwa, ba na salwantar da rayuwa bane, duk wanda dokokin
addini suka ce a salwantar da rayuwarsa, to idan ka duba zaka ga babu abin da
yafi dacewa sama da a salwantar da ratuwar sa, shi yasa kafirai duk kafircin su
duk barnar da sukayi a bankasa, Allah ya ce idan sun tuba ta hanyar furta
kalmar shahada sun bayar da zakkah, kar a kashe masu rayukansu kar a
ribace su, to ina ga dan uwanka musulmi wanda ba tuba ya yi ba, dama can shi
musulmi ne, bawai tuba yayi ba, yana sallah, yana zakkah, yana karatun
al-qurani, da salati da istigfari gwargwadon iko, yana yi, tare da haka kace zaka
rabashi da rayuwar sa da wanne dalili cikin dalilai.
Ya yan uwa dalilan da suke sanya mutane kisan kai suna da yawa,
amma ga misali, yan fashi da makami wanda zasu kashe mutum don su kwace dukiyar
sa sawa'un a cikin gidan sa ko akan hanya lokacin da yake tafiya a kashe shi
don a kwaci dukiyar sa, to wadannan Allah ya fadi sakamakon su acikin Al-qurani
hukuncin su shi ne akashe su ko a tsire su ko a yan ke musu kafar dama da
hannun hagu ko kuma akore su daga kasar musulmi.
Haka kuma, ‘yan ta’adda wadan da su ba dukiyarka suke da bukata
ba, rayuwarka kawai suke son dauka, saboda kawai wata manufa ta duniya da suke
fatan samu, sannan da tunanin watakila kana iya zamar musu barazana wajen samun
abinda suke son samu.
Wannan dai Khudba ce da Marigayi Shiekh Jafar Adam ya gabatar a
masallacin Juma’a na Dorayi a lokacin da yake raye. Muna addu’ar Allah ya kai
rahama gareshi, ya kyauta makwancinsa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment