Mallam Mudi Sipikin: Anya Najeriya
Tayi Maka Halacci Kuwa?
Duk wanda ya san
tarihin gwagwarmayar siyasa da akayi a najeriya ya san da cewa mudi sipikin
yana daga sahun gaba na masu wannan fafutuka. Su mallam Mudi kusan su ne
wadan da sukayi gwagwarmaya tun zamanin turawa, lokacin da Bature yake sawa a
daukeshi aka yana karanta jarida, hakika wadan nan bayin Allah sunyi
gwagwarmaya da turawa musamman ta nemawa Talakawan wannan kasa ‘yancin kai da
‘yancin walwala. Su mallam mudi sipikin sunyi gwagwarmaya tare da su Marigayi
Mallam Aminu Kano Allah ya jikansa da irinsu mallam Lawan Dambazau da
marigayi Sa’adu Zungur da sauransu.
Mallam Mudi sipikin
yana daya daga cikin mutum 56 da akaje London comperence da su
domin tattauna yadda za’a bada ‘yancin wannan kasa. Ta sanadiyar wannan taro
na Landan Najeriya ta samu Mulkin kai daga hannun Turawan Burtaniya. A duk
cikin wadan nan mutane da suka je wannan taro na Landan Mallam Mudi Spikin
shi ne kadai mutumin da yake a raye yanzu haka. Amma haka aka yi bikin cikar
Najriya shekaru hamsin da Samun mulkin kai, aka raba kyaututtuka ga Mutanan
da suka nuna hazaka wajen dorewar wannan kasa, amma babu ko daya daga cikin ‘yan
Siyasarmu da ya tuna da wannan bawan Allah, abin da zai iya zama abin kunya
ga ‘yan siyasarmu musamman na Arewa. Bayan ita kanta gwamnati su kansu
Talakawa basu kyautawa wannan dan tahaliki ba, domin duk gwagwarmayar da suka
yi, ba sunyi ne dan kashin kansu ba, a’a sunyi ne domin amfanin Talakawa,
andoke su an dauresu, duk dan saboda nemawa talakawa ‘yanci amma yanzu
talakawa basa bukatar shawarwarin irinsu.
Duk wanda ya je Fagge
gidan Mallam Mudi Spikin dole ya tausayawa wannan dan tahaliki dattijo mai
halin dattako. Kaga gidan da yake a zaune, ba wani gida ne na kuzo mu gani
ba, bayan kuma ga ‘yan siyasa can da basu tsinanawa kasar nan da komai ba,
suna kwana a tafka tafkan Gidaje a Legas da Abuja da Kaduna. Bari mu kalli
irin gwagwarmayar Siyasar da su Mudi Spikin suka yi tundaga kafa Jam’iyyar
NEPU da sauran gwagwarmayar Siyasa.
|
Bari mu
fara da tarihin kafuwar Jam’iyyar NEPU, kamar yadda tarihi ya bayyana an kafa NEPU
ne a ranar 8-8-1950. Haka kuma, mutum takwas ne suka kafa ita wannan jamiyya
wadanda suka hada da Bello Ijumu da Abba Maikwaru da Mudi Sipikin, da
Magaji danbatta da Baballiya Manaja da Musa Kaula da Abdulkadir
danjaji da kuma Garba Bida. Wadannan sune mutum takwas da suka kafa
wannan jam’iyya gwagwarmayar ‘yanto talaka daga kangin bautar sarakuna da
Turawa, bari mu sake komawa baya
kadan domin mu kalli tarihi.
Asalain wannan guguwar sauyi ta fara ne tun lokacin
da aka kafa jam’iyyar NCNC (National Council of Nigeria and the Camerroun) a
ranar 26 ga watan Augusta a shekarar 1944. Ita ce jam’iyyar
siyasa ta farko da za a iya kiranta ta kasa baki daya, domin kuwa ta
watsu ko ina a Najeriya. Kuma itace jam’iyyar siyasa da ta fara kokarta wa
wajen wayar da kan talakan Najeriya domin ya san ‘yancinsa da kuma kokarin
samar musu da muryar gabatar da koke-koken da suke da su ga Turawan mulkin
mallaka.
A zaben da jam’iyyar NCNC ta yi wa malam Sa’adu
Zungur a cikin shekarar 1948 a matsayin sakatarenta na kasa da kuma kokarin
da ta yi kokarin ganin cewa kowane bangare na kasar nan ya samu wakilci
acikinta, wannan kuma wani gagarumin sauyi ne na siyasar kasar nan. Wannan
wayon ‘yan mulkin mallaka ya mayar da hankali wajen jaddada bambance-bambance
marasa masalaha da suke tsakanin ‘yan Kudu da ‘yan Arewa a siyasar Najeriya.
Bayan kafa NCNC acikin shekarar 1944 sai aka
yi yajin aiki na kasa baki daya, wanda kuma wannan yajin aiki shi ne na
farko a tarihin Najeriya wanda aka share kwanaki 44 ana yi.
Wannan yajin aiki bayan girgiza tattalin arziki karkashin ‘yan
mulkin mallaka da ‘yan barandansu wato sarakuna, ya kuma nuna afili inda
mulkin mallaka yake da rauni da kuma nakasa.
Cif Makel Imoudu dan majalisar gudanarwa na
NCNC ne ya jagoranci wannan yajin aikin da ya gurgunta tattalin arzikin
kasa karkashin Turawan mulkin mallaka. A karkashin wannan fafutuka da
NCNC ta yi ne aka dinga ganin jama’a a birane daban- daban suna shirya
gangami da aka ringa Allawadai da Bature a fili balo-balo babu tsoro.
Bayan gama wannan gwagwarmaya ne kuma aka samu
bullar Northern Elements Prograssibe Association wato NEPA a Kano wadda aka
kafa a ranar 1 ga watan Disamba a shekarar 1946, wannan kusan ita ce
jam’iyyar siyasar farko daga Arewacin Najeriya. Kafa wannan jam’iyya keda
wuya ya bayyana cewa tsatstsauran ra’ayi shi ne mafarinta, wanda kuma
shugabannin ta sune irinsu Habib Raji Abdalah da Abubakar Zukogi wadanda kuma
alakarsu da Zik ba boyayya ba ce.
Ana cikin irin wannan hali ne kwatsam sai aka wayi
gari da bullar sabuwar jam’iyyar Northern elements Prograssibe Union NEPU,
kamar yadda muka fada a baya ita wannan jam’iyya ta kafu ne da mutum 8 kuma
ranar 8 ga watan 8 a shekarar 1950.
Marigayi Alhaji Abba Maikwaru shi ne ya zama
shugaban NEPU na farko kuma Bello Ijoumu shi ne sakatare. Don haka NEPU
ta fara ne amatsayin Jam’yyar siyasar Arewa mai sigar kishin kasa. Kasancewar
NEPU ruhinta yana cikin talakawa da manoma da ma’aikata da sauran al’umma da
ake dannewa kuma ake zalunta, don haka ne wannan jam’iyya ta sadaukar da
manufofinta wajen gwagwarmaya domin ceto al’ummomi da aka danne da kuma
kokarin tabbatar da ‘yancin dan Adam da dimokuradiyya.
A shekarar 1976 ne lokacin da aka samu zababbun
shugabannin kananan hukumomi wanda aka raba su da sarautar gargajiya. Amma
ba’a rabu da bukar ba domin galibi ‘yan mulkin mallaka sun gadar da
mulkin ne zuwa ga ‘yan barandansu na wannan lokaci wato ‘yan boko da sojoji
marasa imani da kishin kasa, wadda a yanzu sun shirya komai sai su suke iya
zama komai domin daga cikin shegantakar da suka fara yi shi ne cewa babu
wanda zai iya tsayawa zabe a zabe shi sai mai takardar shedar gama makarantar
sakandare wanda wannan lokaci kaso 90 duk talakawane da ba su yaki jahilci
ba, ta hakane bayan mulkin mallakar Turawa kuma aka fuskanci mulkin mallaka
karkashin bakake wadanda su kadai ne ke iya zama gwamna ko ciyaman ko
kansila, har ila yau kuma sun mai da karatun boko sai mai kudi ne zai iya
yinsa, kuma sai tajirine zai iya biyan kudin shiga zabe.
Bayan wannan hali ne da ake ciki sai aka samu yakin
basasar da ya kusan wargaza kasar nan wannan shi ne ya kawo cikas ga cimma
nasarorin da NEPU ta sa a gaba ana cikin wannan hali ne sai aka samu bullar
jam’iyyar ceton Al’umma wato PRP karkashin jagorancin Malam Aminu Kano wadda
kuma aka kaddamar a ranar 28 ga watan Oktoba 1978, a Kaduna. Wannan ta baiwa
malam Aminu Kano damar gwagwarmayar ceto talakwa.
To ko me yabiyo bayan wannan gwagwarmaya? Kusan idan
zamu amsa wannan tambayar sai mu ce babu abinda ya biyo bayan wannan
gwagwarmaya face Butulci da cin-amana daga shugabanni Na siyasa wanda da
gudunmawar talakawa mai yawa aka yi wannan wa-kaci-ka tashi.
Duk da kokarin da jam’iyyar Nepu da PRP suka yi na
fitar da talaka daga halin talauci da kangin bauta, amma abin haushi da
takaici shi ne haryanzu muna nan a gidan jiya. Talaka ya zama dan maula da
tumasanci, baya kishin kansa sannan shugabanni basa kishin kasa, sun sace
dukiyar kasa tare da Jahiltar da talakawa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
|
Tabbas na ji dadi da naga wannan rubutu kasancewa ta dalibi mai nazarin harshen Hausa,amma na kasa karanta shi yadda ya kamata saboda wani rubutun ya hade da hoton wasu litattafai da ke a wannan shafi naka.Dan Allah ka taimaka ka turo man wannan bayani a email di na.mustaphasalmanu00@gmail.com
ReplyDelete