Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi #3
Ya
yan uwa barkanmu da sake saduwa a wannan lokaci mai dumbin falala na azumin
watan Ramadan. Muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya nuna mana kashin
farko cikin uku na wannan wata, Allah ya sa ibadun da muka gabatar a cikin
wadan nan kwanaki goma da suka gabata karbabbu ne, Muna rokonsa tare da
tawassali da sunayensa tsarkaka madaukaka ( Subahanahu wata'ala) ya sa ba
kishirwar banza mukayi ba! ya Allah kaine kace mu roke ka zaka amsa mana, ya
Allah mamallakin komai, muna rokon kayi mana rahama da iyayenmu da 'yan uwanmu
da abokanmu baki daya, Allah ka amintar da mu a garuruwanmu, Allah ka bamu
lafiya da zama lafiya a kasarmu baki daya, haka kuma 'yan uwanmu da suke cikin
tsanani a kasar Siriya Allah ka kai musu dauki.
Ya
'yan uwa masu giram, kamar yadda muka sani yanzu Azumi kusan ya zama ba bako
ba, zamu ce ya zama dan gari. Yanzu masallatai da guraren karatuttuka sun fara
ja da baya, a farkon Azumi masha Allah, sai kaga dukkan guraren Ibada cike suke
da jama'a amma kuma yanzu abin ya ja baya, da fatan 'yan uwana matasa zasu dage
kada su karaya wajen Ibada.
Ya
'yan uwa masu girma, Ramadan wata makaranta ce, wadda ba wai kawai ta tsaya
iyakar kwanakin Azumi ba, a'a ana son dukkan darasin da muka koya a Ramadan mu
cigaba da dabbaqa shi har bayan azumi, shakka babu yana da kyau mu sani kuma mu
sakankance, cewar dukkan wani wa'azi ko Nasiha da muka ji, tabbas ya zama hujja
akanmu, don haka dole mu dage mu yaki shedan wajen aikata ayyukan da aka
kwadaitar da mu, ya dan uwa, Ba lallai ba ne sai kazama Abdullahi Dan Abbas
wajen sallah da karatun al-qur'ani da kiyamullaili ba, a'a ana son lallai mu
ringa kwatanta irin darusan da muka koya a Ramadan, misali wani yana nan tun
shekarar bara rabonsa da yin sallar Asubahi a cikin Jam'i amma yanzu
alhamdulillah Ramadan ta sa yana fitowa sallah tare da jama'a, to irin
haka ake so mu dore ba kawai Idan Ramadan ya wuce ba shi kenan mun daina Sallah
a jam'i mun daina ciyarwa mun dai sadaqa mun daina zakka mun daina taimako,
lallai ne bayan wucewar Ramadan mu cigaba da dabbaka irin abubuwan da
makarantar Ramadan ta koyar da mu, wannan shi ne yake nuna mana cewar lallaia
mun amfana da lokacinmu a Ramadan.
Ya
'yana uwa, yana daga cikin abinda malamai suke gaya mana cewa idan kaga mutum
ya dore da ibada a bayan watan Ramadan alama ce da ta ke nuna cewar lallai
Allah ya karbi addu'o'insa da kuma ibadunsa, haka kuma yana daga cikin abinda
yake nuna cewar ayyukan bawa iyakacinsu inda ya yi su, shi ne aga mutum ya koma
mummunar rayuwar da yake yi kafin Ramadan kaga wannan ya nuna mana cewa wannan
mutumin bai amfana da lokacinsa a cikin Ramadan ba, illa iyaka ya bata lokaci
ya walar da kansa wajen yunwa da kishirwa, wannan babban abin tashin hankali ne
kwarai da gaske ya 'yan uwa masu girma.
Yau
ma anan zan dakata sai Allah ya kaimu wani makon domin dorawa a inda muka
tsaya, muna rokon Allah ya shiryemu shiriya ta addinin musulunci, Allah ya sa
ibadunmu karbabbu ne, marasa lafiyarmu gida da asibiti Allah ya basu lafiya, mu
da muke da lafiya Allah ya karamana, 'yan kasuwarmu Allah ya sanya albarka a
cikin kasuwanci, ma'aikata kuma Allah ya sanya albarka a cikin albashi, matan
da suke neman mazaje nagari Allah ka basu, mazan da suke neman mataye na kwarai
suma Allah ka basu, muna da dumbin matasa masu son aure tsakani da Allah amma
babu yadda zasuyi muna fatan Allah ya hore mana gabaki daya.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment