Monday, July 16, 2012

Tsakanin Jama'atu Nasrul Islam Da Sarkin Musulmi Sultan Sa'adu Abubakar Wa Ke Jagorancin Musulmi A Najeriya?

Tsakanin Jama’atu Nasrul Islam Da Sarkin Musulmi Sultan Sa’adu Abubakar Wa Ke Jagorancin Musulmi A Najeriya?
Kusan kamar yadda dukkan Musulmin Najeriya mu ke bibiye da halin da Musulmi suke ciki a garin Jos da sauran sassan jihar plateau mun san da cewa halin da suke ciki mawuyacin hali ne ainun. Shakka babu kamar yadda  alamu suke nunawa, kuma bayanai suke kara bayyana shi ne, Gwamnatin jihar Plateau karkashin jagorancin Jonah David Jang tana yin dukkan kokarin kakkabe al’ummar Musulmi daga wannan jiha, ta hanayar amfani da rundunar tsaron Special Task Force (STF) kamar yadda muka ji a makon da ya gabata cewar wannan runduna karkashin jagorancin sabon shugabanta Maj. Gen. Hanry Ayoola sun baiwa musulmi dake zaune a karamar hukumar Reyom da Barikin Ladi wa’adin sa’o’I 48 da su fice daga gidajensu da dukkan abinda suka mallaka ko kuma su hada da fushin wannan runduna. Wannan abu kamar a mafarki, ace a Najeriya ake irin wannan batu, duk da tsarin mulki ya baiwa duk dan Najeriya izinin zama a duk inda ya ga dama.
Wannan abin da Gwamna Jang ya yi, kusan shine karo na biyu da aka yiwa Musulmi irin wannan cinkashin kaji a yankin Arewa, inda alkaluma suka tabbatar da cewa Musulmi sune sama da kaso 75 na al’ummar wannan yanki. Idan bamu manta ba a shekarar 2008 gwamnan jihar Neja Mu’azu Babangida Aliyu ya kori musulmi daga wani kauye da suke zaune a karamar hukumar Mokwa inda suka kira wannan kauye da suna Darul Islam, dukkan bayanai sun tabbatar da cewar mutanan wannan gari ba su da wata barazana ga tsaro, ko kuma tayar da zaune tsaye, gwamnati ta tura jami’an tsaro inda suka ringa caje mutane gida gida da nufin zakulo ko mutanan wannan sabon gari suna da makamai ko wasu abubuwa da zasu iya janyo salwantar rayuka, bayan wannan bincike ba’a samu komai ba. Amma duk da haka gwamnan Neja ya yi gaban kansa wajen tarwatsa al’ummar wannan gari.
Haka nan tarihi ya maimaita kansa a wannan lokaci a jihar Plateau, inda gwamnan Jang yake kokarin sanya takalmi irin na Babangida Aliyu wajen fatattakar Musulmi. Hakika wannan babban abin takaici ne ace haka na faruwa da Musulmi a yankinsu na asali, kamar babu hukuma ko kuma jagororin Musulmi. Dukkan shugabannin Musulmi suna kallo babu wani da ya firo ya yi Magana da kakkausan lafazai akan wannan shiri na Gwamna Jang, sai gashi abin mamaki kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ta ACF ta bakin kakakinta Anthony Sani wanda kirista ne, wai su ne zasu je birnin jos dan ganin hanyoyin da za’abi wajen magance wannan matsala da ke faruwa a wannan jiha, anan sai mu tambaya shin tsakanin kungiyar Jama’atu Nasrul Islam da mai Alfarma Sarkin Musulmi Sultan Sa’adu wa ye yake jagorancin Musulmi?
Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasarnan ya amince da kungiyar Christian Association of Nigeria ko CAN a takaice don ta kare muradun kiristoci a wannan kasa; da kuma kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ko JNI suma dan su kare muradun musulmi a wannan kasa. Ko shakka babu nasan babu wanda yake inkarin cewar kungiyar CAN tana yin iyakar kokarinta wajen ganin sun kare muradun dukkan kiristocin Najeriya ta duk hanyar da suke gani zasu iya, sharri da makirci da kutungwila babu wadda basa yi dan cikir burinsu, duk saboda su kyautata tare da dadadawa kiristocin Najeriya.
Mu kallai irin yadda shugaban kiristocin Najeriya Pasto Ayo Oritsejafor inda ya tsaya kai da fata sai ankamo kabiru sokoto wanda ake zargi da shirya kai harin coci a madalla, sunyi dukkan mai yuwuwa sai da hakarsu ta cimma ruwa, wanda yanzu haka Kabiru Sokoto yana hannu, tabbas bamu ga laifin CAN ba, domin babu wanda zaiso al’ummarsa su shiga matsala matuqar yana da yadda zai yi. Daga zarar wani abu ya faru da kirista sai kaji CAN sunyi ruwa sunyi tsaki, amma kuma idan aka kama kirista da laifi sai su yi ta boye wannan laifi da nuna cewa kuskure ne, ko su yi gum da bakinsu kamar yadda suka yi akan kiristocin da aka kama da yunkurin tarwatsa coci da bamabamai.
Haka kuma, duk lokacin da wani abu ya faru zaka samu shugaban CAN shi ne yake wucewa gaba tare da rakiyar mukarrabansa na wannan kungiya. Wani abin birgewa da wannan kungiya duk wani kirista zaka samu yana mubaya’a ga dukkan manufofinta domin sunyi imani cewar za’a kyautata musu da kuam kare muradunsu, haka kuma inda baka taba tsammani ba zaka samu wannan kungiya tana shiga domin kare muradun kiristoci, suna da sojoji da ‘yan sanda da yalo fifa, da kwastan da gandurobobi da dukkan dangin jami’an tsaro ba dan komai ba sai domin su kare muradun al’ummar kirista. Haka kuma, dukkan wani kirista yana da alaka da shugabannin wannan kungiya kai tsaye, duk wani kirista da yake son shigar da koke zai shigar babu hijabi tsakaninsa da shugabannin wannan kungiya.
Idan muka dawo ta bangaren kungiyar Jama’atu Nasrul Islam da Sarkin Musulmi sai mu kasa gane wanenen ba wanene ba. Don nikam har yanzu na kasa bambance menene aikin Sarkin Musulmi kuma menene aikin wannan kungiya ta JNI. Sarkin Musulmi yana can a fadarsa a sokoto, wanda kamar yadda muka sani tun bayan jahadin shehu Usmanu Dan Fodiya shi ne, Sarkin Musulmi kusan shi ne shugaban sarakunan Arewa, domin dukkan sarakuna suna karbar umarni daga gareshi. Wannan a sarautance kenan. Amma yanzu mun kasa gane shin menene ainihin aikin Sarkin Musulmi shin kare muradun Musulmi kamar yadda shugabannin CAN suke yi? Ko kuwa aikinsa shi ne yana baiwa sarakuna umarnin sanar da ganin jinjirin watan Ramadan ko shawwal? A daya gefen kuma ga kungiyar JNI wadda ke da shalkwata a Kaduna, shin aikinsu kamar na kungiyar kiristoci ne su kare muradun Muslmi a Najeriya ko kuwa ya ya abin yake?
Idan har ya tabbata cewar da Sarkin Musulmi da Kungiyar JNI aikinsu shine kare muradun Musulmi a Najeriya, sai muce ko kusa ba sa yin aikinsu. Domin a ina JNI da Sarkin Musulmi suke akewa Musulmi irin abinda ake yi musu a Jos da sauran sassan jihar Plateau da Zankowa da Zangon Kataf a jihar Kaduna da Tafawa Balewa a jihar Bauchi? Shin sun san abinda yake faruwa da Musulmi a sauran sassan Najeriya? Shin suna shiga lungu da sako domin ganin halin da Musulmi suke ciki a Najeriya da tunanin samar musu mafita? Lallai muna bukatar sanin ainihin aikin Sarkin Musulmi da kungiyar JNI.
Sannan shin sauran Musulmin da suke Kudancin Najeriya suna karkashin jagorancin wannan kungiya ta JNI da Sarkin Musulmi? Ko kuwa muslmin kudu daban na Arewa daban? Shakka babu, musamman mutanan Yamma yarabawa basa kallon JNI da sarkin Musulmi a matsayin jagororinsu, domin da sun yarda cewar suna karkashin jagorancin JNI da Sarkin Musuli da bazamu taba samun matsala da mutanan yamma ba a siyasance ko a addinance, amma a bayyane yake cewar Musulmin yamma daban na Arewa daban. Mun san da cewar akwai kungiyar Yarabawa Musulmi ta NASFAT wadda take aiki ka’in da na’in domin ganin ta kare muradun Musulmi yarabawa, suna da masallatai da makarantu da suke kula da su a kusan dukkan jihohin kudu maso yamma da Abuja, katafaren masallacin juma’a na Abuja na Lababidi da makarantar Lababidi duk yana karkashin wannan kungiya, kuma tabbas a kafatanin Najeriya babu wata kungiyar Musulmi da takai NASFAT kudi da tsari da kokarin ingantawa Yarabawa Musulmi.
Idan muka gangaro Arewa, shin Musulmi nawa ne a Arewa wadan da suka san da JNI da ayyukanta? Na tabbata da yawa daga cikin mutananmu na Arewa musamman wadan da suke zaune a can cikin kurya basu ma san da wannan kungiya ba, daman karkayi maganar birane domin mafiya yawa daga cikin matasa masu so da kishin addini da suke a makarantun islamiyyu a cikin biranen Arewa basu san da wannan kungiya ba. Ada can mun san ana debo matasa daga shalkwatar kananan hukumomi ko gidan hakimai duk juma’a ana rabasu zuwa masallatai da fararen kaya da shudiyar hula domin aikin bayar da agaji a lokacin sallar juma’a, amma yanzu ban san ba ko har yanzu ana yin haka.
Lallai idan har Jonah Jang ya cika wannan mummunan Nufi nasa akan al’ummar musulmi a jihar Plateau, Allah ya kiyaye, to tabbasa mun san babu wasu jagorori na Musulmi a Najeriya. Illa masu rike da sarautar gargajiya irin ta Oba na Ife dake Legas, JNI kuma itama zamu kalleta a matsayin kungiya ce kamar sauran kungiyoyi da suke neman kudi a Najeriya amma ba da sunan kungiyar kare muradun musulmi ba kamar yadda tsarin mulki ya amince. Allah ka zama gatan musulmi a wannan kasa ka shige mana gaba.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

1 comment:

  1. Hakika, JNI da Maigirma sarkin musulmi basu kare hakki da martabar musulman arewa. Addu'a ce mafita musamman a wannan wata mai albarka

    ReplyDelete