Wednesday, July 18, 2012

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci A Watan Azumin Ramadhan

Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan Azumi

Dukkan dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah ubangijin halittu tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam, da alayansa Alu Akilu, Alu Abbas, Alu Jafar, Alu Aliyu da sahabbansa wadan da sune sukayi mana tsuwurwurin wannan addini har ya kawo garemu, Allah ya yarda da su baki daya, da kuma wadan da suka bi tafarkinSa har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad bawanSa ne kuma manzonSa ne, dukkan wanda Allah ya shiryar shi ne hakikanin shiryayye, dukkan wanda Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.

Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani lokaci na kara turawa gaba, muna kara kusa ga wata mai alfarma wato Ramadhan. Kuma ga mai hankali yasan da cewa kwanakinmu muke cinyewa a hankali, lokutanmu ne suke tafiya, hakika dukkan lokacin da ya tafi to ya riga ya shiga kundin tarihi, lallai mun kasance al’umma masu hasarar lokutanmu masu tsadar gaske bamu sani ba ko kuma muna gafale.

Kamar yadda Allah yake fada a cikin sura ta 2 aya ta 164 an sanya dare da rana masu shudewa, wanda yake nuna mana cewa wucewar dare da rana alama ce ta tafiyar lokaci a garemu, kuma muna kara kusa ga ajalinmu ne bamu sani ba, muna ta addu’a “Allahumma Balligna Ramadan” amma kuma muna kara kusanta kanmu ya zuwa ga ajalinmu ne ashe. Lallai lokaci abu ne mai tsadar gaske a cikin rayuwarmu, a saboda muhimmancin lokaci ne Allah ta’ala da kansa ya yi rantsuwa da lokaci a cikin sura ta 103 dan ya nuna mana muhimmancinSa subahanahu wata’ala, tsarki ya tabbata a gareshi.

Ya ‘yan uwana, kamar yadda Allah ya bamu labari acikin al-qurani mai tsarki; wannan wata da yake tun karomu na Ramadhan shi ne watan alqurani kamar yadda Allah ya shaida mana a cikin sura ta 2 aya ta 185, Allah ta’ala da kanSa ya yi kira a garemu cikin wannan aya da cewa duk wanda ya halarci wannan wata ma’ana duk wanda ya riski kansa a wannan lokaci to ya azumceshi. Haka kuma har ila yau Allah ya cigaba da shaidamana acikin wannan sura aya ta 183 cewa shi wannan wata kwanaki ne kididdigaggu, kamar Allah yana cewa ne muyi amfani da lokutanmu ta hanyoyin da suka dace a cikin wannan wata.

Ya ‘yan uwa masu Girma, kamar yadda muka sani, mun bata tare da hasarar lokuta masu yawa muna barci da da shagaltuwa da wasu abubuwa wadan da ban a larura ba a kusan watanni 11 da suka gabata. To lallai yana da kyau a wannan watan muyi dukkan mai yuwuwa wajen ganin mun ribaci wannan lokaci. Wannan wata na Ramadhana kamar yadda malamai suke ta bayani yana daga cikin watanni masu dimbin falala kuma kwanakinsa guda 29 idan ya yi tsawo ya cika kwana 30, darensa da wuninsa duka cike suke da dimbin falala, kamar yadda ya zo a cikin ingatattun hadisai cewa ana bude dukkan kofofin alkhairi a wannan watan haka kuma ana kulle dukkan kofofin sharri a wannan watan. Haka kuma acikin wannan wata ne ake da dare guda daya wanda ya dari watanni dubu alkhairi(lailatul Qadri).

Kamar yadda muka sani wannan watan yana da makwanni 4 da kwanaki 29, acikin kowace rana akwai awanni 24, haka kuma acikin kowace sa’a muna da dakika 60, don haka idan muka hada lissafi muna da awanni 696 a cikin wannan wata, lallai akwai bukatar mu tsaya mu kalli wadan nan awanni mu tsara lokutanmu da kuma kokarin kiyaye ka’idar da muka sanyawa kawunanmu.

Sauda yawa wasu daga cikinmu sukan dauka watan azumi lokaci ne na aci kayan dadi a more kawai. Lallai akwai bukatar muci daga cikin abinda Allah ya hore mana, amma kuma mu zage dantse wajen yin idaba karatun al’qur’ani dare da rana safe da yamma, zikirin safe da na yamma, sallolin farilla cikin jam’I da kuma sallolin Nafila da kiyamullaili. Idan aka ce maka watan Ramadan ya kama a farko-farko idan kaje masallatanmu abin gwanin ban sha’awa domin duk masallacin da kaje zaka ga ya cika da jama’a wani zubin mutane har a waje suke sallah, masallacin da akeyin sahu biyu a sallar asuba sai ka tarar ya cika makil a farkon Ramadan; amma daga zarar ance maka an tsallake goman farko sai ka fara ganin karancin mutane a masallatai, da guraren karatuttuka.

Haka kuma, a cikin sahihin hadisi Manzon Allah  yana cewa ku fanshi kanku daga wuta ko da da barin dabino ne. lallai wannan babbar Magana ce, muyi kokari wajen yawan aikata alkhairi da ciyarwa a wannan watan gwargwadon hali, idan kana da ikon sayan dabino na Nera goma yi gaggawa ka siya domin ka fanshi kanka kamar yadda manzon Allah ya fada salallahu Alaihi Wasallam. Lallai hanyoyin amfani da lokuta a wannan wata suna da yawa, kamar yadda nasan ‘yan uwana da suke gabatar da shirye-shirye a filaye daban daban zasu yi bayani, mai gamsarwa.

Zan dakata a wannan gaba sai mako mai zuwa idan Allah ya kaimu, zamu dora daga inda muka tsaya. Kuma wannan fili namu na MATASA JIYA DA YAU zai ringa kawo mana tsokaci kan azumi a tsawon wannan watan gabaki daya, Allah ya sa mu dace, Allah kuma ya sanya muna daga cikin wadan da zasu sami rahama a wannan wata.

Yasir Ramadan Gwale

Yasirramadangwale@gmail.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

www.facebook.com/yasirramadan.gwale

No comments:

Post a Comment