Gwamnan Jihar Plateau Jonah Jang Ya Aikata Laifukan Yaki Da Ya Cancanci Hukuncin Kisa
Rahotannin baya bayan nan da suke fitowa daga jihar Pilato suna nuna irin yadda al’amuran tsaro ke kara dagulewa. Rahotannin sun bayyana cewar sojojin JTF da suke aikin samar da tsaro a jihar Pilato kusan yanzu sune babbar matsalar wannan jihar domin sun hada kai da kabilar Berom, irin yadda bayanai suka nuna cewa sojojin sun shiga garuruwan Fulani dake karamar hukumar Barikin Ladi da Riyom suna cinnawa ardon Fulani wuta babu gaira babu dalili, saboda kawai su dadadawa ‘yan kabilar Berom da gwamna jang. A lokacin da yake zantawa da sashen Hausa na Gidan Radiyon BBC sakataren Miyatti Allah na Barikin Ladi Mallam Ado Muhamma ya kara da cewa “yanzu haka da nake Magana da kai sojoji suna kunnawa gidajen mutane wuta a song II da wuro Bello da Gure Dangere da Dyola da Rakweng da Sharu da kuzeng da Luggel da Rachi Matse” ance sun kona sama da gidaje 160, abin mamaki a lokacin da yake maida martini kakakin rundunar JTF ta jihar pilato sai yake shaidawa BBC Hausa cewar ba sojoji bane suke aikin sanyawa gidajen mutane wuta. Abin tambaya anan shi ne a ina sojojin JTF suke har wasu suka zo suke kona gidajen mutane babu ji babu gani?
Kamar yadda rahotanni suka nunar cewar an kashe wani jami’in ‘yan sandan kwantar da tarzoma kuma akayi awon gaba da bindigarsa. Wanda rahotanni sun tabbatar da cewar shi wannan jami’in tsaro da aka kashe, dauko gawarsa akayi zuwa unguwannin Fulani domin a gogamusu kashin kaji. Wannan ta sanya sojoji karkashin jagorancin Sabon kwamandan rundunar JTF Major Henry Ayoola suka yiwa garuruwan da ke Bangwai a karamar hukumar barikin Ladi inda babu wani bincike aka afkamusu tasa da ta kasa ana harbi da manyan makamai da kuma rowan bomabomai ta sama. Abin tambaya a nan me ya sa yanzu abin ya sauya salo Berom ne kawai ke kashe Hausa-Fulani? Shin Berom ne kawai kabilar da ta ke zaune a Jihar Pilato? Shin me ya sa wannan fada ya takaita ga yankunan da Berom suke da rinjaye? Me ya sa JTF suke hana Fulani komawa gidajensu da aka kona?
Sannan kuma, duk wannan abinda yake faruwa a Jihar Pilato na kashe talakawa bayin Allah, bai ja hankalin gwamnati ba sai da aka bayar da rahotannin mutuwar Sanata da shugaban masu rinjaye na jihar pilato dukkansu ‘yan kabilar Berom, abin tambaya akwai wani rai da yafi wani rai ne? duk wadan da ake kashewa basu damu gwamnati ba sai yanzu aka taba mutane ko? Irin yadda Berom ke kokarin shafe Hausa-Fulani daga yankunan Sabon Gidan danyaya da Dorawar Babuje da Barikin Ladi duk bai ja hankalin hukumomi ba, wannan fa shi ne irin tsabar rashin adalcin da hukumominmu suke yi a jihar pilato ta hanyar fifita kabilar Berom sama da kowacce kabila dake wannan jihar. Kamar yadda General Jeremieh Useni ya shaidawa sashen Hausa na BBC cewar Gwamna Jang shi ne kanwa uwar gamin a duk wadan nan abubuwan da ke faruwa, kuma bad a gaske yake son kawo karshen wadan nan tashe-tashen hankula ba.
Tarihi ya nuna cewa fiye da shekaru 400 Hausawa da Fulani makiyaya suke zaune da dabbobinsu lafiya lau da sauran kabilun da ke zaune a wannan jiha ta pilato suna kiwo tare da samar da arziki ga wannan yanki, domin babu wanda zai iya kididdige shanun Fulani da madarar su da Berom suka ci ko suka sha a iya tsawon wadan nan shekaru, sai gashi yanzu Jang yana son ya sauya akalar tarihi; haka kuma, Jonah Jang da kansa yake fada cewar asalin rayuwarsa ya taso a hannun Fulani ne, sune suka sanya shi makarantar firamare kamar yadda shima mai martaba Gbong Gwom Jos Da Jocub Gyang Buba ya taba fadar cewar Fulani sunyi masa komai a rayuwarsa don haka ne ma yake amfani da sunan Fulani a cikin sunansa wato “buba”.
Wannan rikici da tashin hankali da ake fama da shi a jihar pilato kusan ya samo asali ne tun shekarar 2001 da kuma 2004, lokacin da tsohon gwamna Joshua Chibi Dariye ya so ya shafe al’ummar musulmi daga karamar hukumar Yalwan Shandam da Langtang da Wase da sauransu, a wannan lokaci abin ya yi kazantar da har sai da gwamnatin tarayya karkashin Obasanjo ta sanya dokar ta baci a jihar, inda gwamnan ya kau daga karagar mulki har na tsawon wata shida kafin daga bisani ya koma karagar mulki kamar yadda doka ta tanada. Tun bayan wannan lokaci ne ake ta samun takun saka tsakanin Hausa-Fulani da kabilar Berom.
Lokacin da wannan gwamnan mai ci a yanzu Jonah Jang ya zama gwamna bayan karewar wa’adin Dariye, al’amuran tsaro sun dan kyautata a wannan jihar wadan da suka gudu sun dawo, harkar kasuwanci ta fara komawa dai-dai, kafin daga bisani su kacame, bayan da Jang ya gama zama daram a kujerar gwamna kuma ya gama fahimtar al’amura, sai suka shirya manakisar zaben karamar hukumar Jos ta Arewa inda nan ne fadar gwamnatin jihar Pilato, kuma Hausa-Fulani suke da rinjaye a wannan karamar hukuma, duk kuwa da hukumomin tsaro a wannan lokacin sun gargadi gwamnati kan gudanar da wannan zabe, makircin da akayi a wannan zabe a shekarar 2008 shi ne sai aka sanya wannan zabe ranar alhamis sabanin ranar asabar da galibi ake sanya ranakun zabe a Najeriya, wato bayan da akayi wannan zabe ranar alhamis washe gari juma’a musulmi zasu fita kwai da kwarkwata domin gudanar da ibadar sallar juma’a, a gefe guda kuma arna sun shirya tsaf da makamansu.
Bayan da aka bayar da sanarwar cewar dan kabilar Berom ne ya yi nasarar wannan zabe. Musulmi suka nuna rashin amincewarsu, inda daga nanne abubuwa suka yi kazantar da basu taba yi ba a tarihin wannan jihar ankashe dubban musulmin da basu ji ba basu gani ba, aka yanka wasu aka zuba a cikin rijiyoyi da shadda wasu kuma aka ringa banka musu wuta da ransu, duk wannan ya faru ne a idon jami’an tsaro a unguwannin Dogo na Hauwa da Unguwar Rogo da Bauci road da Rokkos da sauransu, kusan tun daga wannan lokaci akayi bankwana da zaman salama a musamman Jos ta Arewa, inda kusan kullum sai kaji ankashe mutum ko dai ta kisan kan mai uwa da wabi, ko ta kisan mummuke da ‘yan kabilar Berom ke yiwa musulmi nan da can, duk wannan gwamnatin jonah jang tana da masaniyar hakan. Wannan rayuka kenan, bayan dimbin dukiyar da Allah ne kawai ya san iyakarta wadda ta salwanta a sanadiyar wadan nan fadace-fadace.
Anci gaba da tashin hankali a wannan jiha ta Pilato tsakanin Musulmi Hausa-Fulani da kabilar Berom har kawo wannan lokaci. A shekarar da ta gabata lokacin da Musulmi suka je sallar idi a babban masallacin idi na garin Jos aka afka musu da sara da harbi da bindigogi babu kakkautawa, inda jinin al’ummar musulmi ya ringa kwarara a kasa kamar ruwa, har kawo wannan lokaci babu wani abu da gwamnatin Jonah jang tayi na kokarin binkito tare da hukunta wadan da suka kaiwa musulmi wannan mummunan harin ta’addanci, wannan shi ne cikakken rashin adalci, wanda kuma shine silar dukkan abubuwan da suke faruwa a wannan jihar, domin babu wani mahaluki da zai zauna ana kashe masa mutane a gaban idon hukuma kuma babu wani mataki da ake dauka, sannan ya zauna ya zubawa sarautar Allah ido, ya zama tilar kowa ya nemi hanyar da zai baiwa kansa kariya tunda gwamnati ta gaza.
Haka kuma, Hausa-Fulani da suke sana’ar kabu-kabu da Babura suma ankashe daruruwa daga cikinsu, domin Berom zai hau babur ya sanya a kaishi unguwannin da Berom suke, su kashe me baburdin kuma su gudu da babur din, wannan haka aka ringa yiwa ‘yan acaba irin wannan dauki dai-dai. Duk wadan nan abubuwa da suke faruwa ba wai a boye ake yinsu ba, ana yinsu ne da sanin dukkan bangarorin jami’an tsaro na wannan jihar.
Bayan haka, a kwanakin baya wasu mutane da rahotannin suka tabbatar da cewa kiristoci ne suka kai harin kunar bakin wake a cocin church dake a jihar ta pilato. Inda nanma akayi hasarar rayuka, wannan ta sanya ‘yan kabilar Berom suka dauki doka a hannu inda suka ringa kisan Hausa-Fulani Musulmi da basu san hawa ba basu san sauka ba. Bayan kuma shi wanda ya kai wannan hari ance sananne ne yana zuwa wannan coci dan yin sabis. Gwamnatin da jami’an tsaro duk suna ji suna kallo anata kashe musulmi a wannan jihar, saboda cimma boyayyar manufarsu tabice Hausa-Fulani Musulmi daga wannan jihar ta pilato.
Wani abin da zai sake tabbatar da wannan mugun nufi na kabilar Berom shi ne, a kwanakin baya rundunar ‘yan sanda ta kasa suka kama wani jami’in kwastam dan kabilar Berom da safarar makamai zuwa ga kabilarsa ta Berom don su cigaba da aikin da gwamnatin Jang ta sanya su na kisan musulmi babu kakkautawa a wannan jihar, sai gashi abin kunya kakakin gwamnatin pilato ya fito kafar watsa labarai yana kare wannan mugu azzalumin kwastam da aka kama.
Idan har duniya da gaskiya, kuma adalci ake son tsaidawa a ban kasa to ya kamata kotun duniya ta yi sammancin Gwamnan Jihar Pilato David Jonah Jang saboda ya aikata laifukan yaki. Kamar yadda tsohon mai shigar da kara na kotun duniya Lius Morino Ocampo ya bayar da sanarwar sammacin kamo shugaban kasar Sudan Umar Hasan Al-Bashir a saboda ana zarginsa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur ga mayakan larabawan Janjaweed, to lallai Jonah jang ya yi abinda ya ya dara na el-bashir domin kuwa a karkashin umarninsa aka yiwa garuruwan Fulani rowan bama bamai.
Kamar yadda aka gurfanar da Thomas Lubanga da Tsohon Shugaban Kasar Liberia Charles Taylor shakka babu ya cancanci a gurfanar da Jang kuma a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. Idan har kotun Duniya tana kallo za’a yankewa Marigayi Saddam Hussein tshon Shugaban Iraqi hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda zarginsa da akayi da kisan Kurdawa 34, to kuwa babu abinda zai hana zartas da irin wannan hukunci akan Jonah Jang, domin ko Ojukwu da ya jagoranci yakin Biafara bai aikata ta’addancin da Jang ya aikata ba.
Haka kuma, suma kungiyoyin kare hakkin Bil-adama idan da gaske suke aiknsu to lallai ya kamata su shiga jihar Pilato su ceto dubban al’ummar da busu san hawaba basu san sauka ba, ake ta aikata musu kisan kai babu kakkautawa, kamar yadda aka aikata kisan kiyashi a serebranica ga musulmin Bosniya to lallai irinsa ake aikatawa ga Musulmi a jihar pilatu.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment