Tsokaci Kan Azumi: Muhimmancin Lokaci a Watan
Azumi #2
Ya ‘yan uwa barkanmu da sake
saduwa a wannan makon domin cigaba da bayanin da muka somo a makon da ya gabata
akan muhimmancin amfani da lokaci a cikin wannan wata mai dumbin falala na
Ramadhan. Ya ‘yan uwa masu girma kamar yadda muka sani, yanzu tuni azumi ya
fara samun waje yana baje kolinsa, gari tuni ya gama daukar haramar karbar
wannan bako, alhamdulillahi bako ya sauka lafiya, kusan duk inda ka shiga
acikin garuruwanmu zaka ga alamun cewar lallai akwai azumi a bakin mutane,
domin yawan ciye-ciye da lashe-lashe da akeyi da rana kusan yanzu babu,
masallatai sun cika da ambaton Allah, duk inda ka zaga sautin karatun Tafseer
ne ke tashi, gidajen Radiyo da Talabijin kusan duk sun maida hankulansu kacokan
akan wannan wata, muna fatan Allah ya sa muna daga cikin ‘yan tattun bayi.
Ya ‘yan uwa masu girma, ya
zo a cikin ingantaccen Hadisi wanda Bukhari ya fitar da shi a cikin littafinsa,
wanda sahabin Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam Huzaifa Ibnul Yaman Allah
ya yarda da shi ya ruwaito cewa, naji Manzon Allah sallalahu alaihi wasallam
yana cewa “Fitinar mutum ga iyalansa, da dukiyarsa, da makwabcinsa yin sallah
da Azumi suna kankare wannan fitina”. Ya ‘yan uwa kamar yadda muka sani yana
daga cikin fituntunun wannan zamani, Allah ya jarrabi mutum da muguwar mata, ko
kuma Allah ya jarrabi mutum a cikin dukiyarsa ko kuma Allah ya jarrabeka da
mummunan makwabci. To idan Allah ya sanya ka tsinci kanka a irin wannan hali ka
sani Manzon Allah ya riga ya baka mafita.
Lallai wannan lokaci na
Azumi lokaci na da ake bukatar mu zage dantse wajen yin Ibada. Ibada ta Azumi
da Sallah da kyauta da Sadaqa da sada zumunci, wadan nan sune abubuwan da ya
kamata mu baiwa muhimmanci a cikin wannan wata, alhamdulillahi kusan yanzu idan
ka je masallatanmu a lokacin sallar tarawihi ko kuma Asham zaka samu masallatai
sun cika makil da jama’a, hakika wannan babban abin farinci ke ne kwarai; amma
wani kuma abin mamakin da yake cikin wasu daga cikin matasanmu zaka samu suna
tozarta sallar farilla, misali zaka samu wani tunda Allah ya wayi gari babu
sallah ko daya da ya halarta a cikin Jam’I amma kuma yana gaggawar zuwa jam’in
sallah Asham, kaga ko shakka babu wannan ya tozarta sallar farilla, domin ita ce
ahakku akan ya yi ta cikin jam’I amma ya ki yin haka, lallai wannan babban
kuskure ne ya ‘yan uwa lallai mu dage da yin dukkan salloli cikin jam’i.
Sannan kuma, akwai wani Nau’I
na matasanmu wadan da su kuma suna Azumi amma ba sa yin sallar kwata-kwata. Wannan
ma wani babban tashin hankali ne, ace mai azumi baya kiyaye sallah, lallai mu
sani tozarta Azumi ne, mutum ya ki yin sallah dagangan, wasu sun dauka lokacin
Azumi lokaci ne na a shafe tsawon dare anata kallon tashoshin Zee Aflam ko
MBC2, MBC MAX, MBC Action, domin a shagaltar da idanu, wai saboda a samu damar
yin dogon bacci da rana, wannan babban kuskure ne ya ‘yan uwa masu girma, lallai yadda muke rayar
da rana da Azumi da karatun al-qurani da zikiri, to haka ya kamata mu rayar da
dare, domin samun dacewa da rahamar Allah acikin wannan wata
Yan ‘yan uwa masu girma,
yana daga cikin kuskuren da muke aikatawa a cikin azumi da kuma bata lokacinmu
shi ne, a duk lokacin da aka ce maka yamma tayi jama’a kowa na hanzarin ya koma
gida domin buda baki tare da iyali, sai ka samu mutane suna warware ladan
azuminsu ta hanyar zage-zage da cin mutuncin juna akan hakkin amfani da hanya,
dan hakuri kalilan da mutane zasu yi, amma sai ka samu ana ta tayar da jijiyar
wuya da maganganu marasa dadi, lallai wannan babban kuskure ne, kuma hasarar
lokaci muke yi mai daraja, domin gab da faduwar rana, ko lokacin faduwar rana
wannan shi ne lokacin buda baki, a kuma wannan lokacinne ake son mutum ya yi
addu’ar buda baki bayan ya sanya wani abu a cikinsa, amma sai kaga muna hasarar
wannan dama. Ya ‘yan uwa lallai mu guji aikata dukkan wasu ayyuka da zasu iya
kaiwa zuwa ga warwarar azuminmu.
Ya ‘yan uwa, masu girma
lallai ya kamata mu sani cewa lallai azumi garkuwa ne, a cikin wani hadisi da
sahabin Manzon Allah Mu’azu bin Jabal ya ruwaito wanda turmizi ya fitar da shi
yana cewa, wata rana Manzan Allah ya ce min Ya Mu’az shin bana nuna maka
kofofin alkhairi ba, sai n ace e ya manzon Allah, sai ya ce Azumi garkuwa ne.
lallai idan muka kalli wannan hadisi zamu gane cewar lokacin da muke dauke da
Azumi a bakinmu ba lokaci bane da zamu tsaya muna bata lokaci ko cacar baki
akan wani abu kankani ba.
Yauma zan dakata anan sai
Allah ya kaimu mako mai zuwa zamu ci gaba da wannan bayani. Allah ya karbi
wannan ibada tamu, Allah ya sa ba kishirwar banza muke yi ba. Allah ya sa muna
daga cikin wadan da zasu samu rahamarsa subahanahu wata’ala.
Yasir
Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
No comments:
Post a Comment