ZABEN 2015 BABU SAURAN CI-DA-BUGUZUM
An dade ana magana akan
irin yadda wasu 'yan siyasa ke fakewa da farin jinin wasu mutane dan
samun nasarar zabe, kuma su kasa tabuka wani abin kirki bayan sunci
zabe, sai dai ga dukkan alamu wannan ci-da-buguzum yazo karshe a wannan
zaben. Domin kuwa Idan muka duba batun kaddamar da takarar da GMB yayi a
Jihar Ribas, ya isa ya zama ishara ga duk masu jiran ci-a-bagas cewa
wannan lokacin na kowa tasa ta fishsheshi ne, dan kuwa shi, GMB ya gabatar
da kansa gaban dumbin jama'ar da suka taru ya gaya musu sunansa
Muhammadu Buhari yana neman takarar Shugaban kasa, kuma yana rokon su
zabe shi, dan kawo sauye-sauye a harkar tafiyar da Gwamnati a najeriya.
Abinda hakan ya nuna a wannan karon, shi ne cewar Siyasar GMB ta
sauya, domin kuwa a Ribas GMB bai daga hannun kowa ba, abinda yake nuna
sai dai kowa tasa ta fishsheshi, dan haka wannan babban albishir ne GMB
ya yiwa masu jiran ci-a-bagas cewa babu hannun wanda zai daga dan ya
rabu da shi yaci zabe, dole kowa tasa ta fishsheshi, wadan da suka
kwanta a gida suna jiran GMB yazo jihohinsu ya daga hannunsu dan
ci-da-buguzum wannan lokacin ya wuce.
Ina kuma jinjinawa GMB akan wannan mataki da ya dauka, ba shakka wannan abin yabawa ne, kuma wani cigabane a Demokaradiyya. Babu sauran shiga rigar Buhari a ci zabe, mun san GMB na kowa ne, yana da mutane a ko wace Jam'iyya.
Yasir Ramadan Gwale
07-01-2015
Ina kuma jinjinawa GMB akan wannan mataki da ya dauka, ba shakka wannan abin yabawa ne, kuma wani cigabane a Demokaradiyya. Babu sauran shiga rigar Buhari a ci zabe, mun san GMB na kowa ne, yana da mutane a ko wace Jam'iyya.
Yasir Ramadan Gwale
07-01-2015
No comments:
Post a Comment