SARKIN SAUDIYYA NA 6: ABDALLAH YA KWANTA DAMA
Yau juma’a daya daga cikin manyan ranaku a Musulunci, Allah ya karbi
rayuwar Sarki Abdullah Ibn AbdulAzizi Al-Saoud na Saudiyya. Allah yayi
Sarki Abdullah rasuwa bayan ya sha fama da jinya ba mai tsanani ba,
kamar yadda rahotanni suka nuna Sarki Abddullah ya jima yana fama da
cutar Numoniya har zuwa lokacin da hukumomi a Riyad suka bayar da
labarin kwantar da shi a wani asibii dake Riyar a makwannin da suka
wuce. Abdullah Ibn AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya, ya
rasu yabar ‘ya ‘ya da jikoki masu yawa, haka kuma, Sarki Abdullah shi ne
Sarki na Shida (6) tun bayan kafa daular Saudiyya a Shekarar 1930.
Marigayi Sarki AbdulAziz Ibn Abdulrahman Ibn Muhammad AlSaud wanda ake
yiwa lakabi da Abu-Turki Akhu-Noura, shi ne ya jagoranci Jihadin kafa
Daular Sa’udiyya a yankin Hijaz. Bayan rasuwar Sarki AbdulAziz Alsaud a
shekarar 1953, yarima mai jiran gado wanda shi ne babban dansa Sa'ud
Ibn AbdulAziz ya gajeshi a matsayin Sabon Sarki na biyu bayan kafa
Mamlakatul Araabiyat Ass-Sa’udiyya.
Sarki Saud Ibn AbdulAziz ya
karbi Sarauta daga mahaifinsa har zuwa shekarar 1964 lokacin da Allah
yayi masa rasuwa. Kafin rasuwarsa Saud Ibn AbdulAziz shi ne wanda ya
fara samar da majalisar ministoci a masarautar da suka hada da Ilimi,
lafiya da kuma kasuwanci. Haka kuma, Sarki Sau’d ya zabi Gwamnan Riyad
na lokacin wanda shi ne kaninsa Faisal Ibn AbdulAziz a matsayin Yarima
mai jiran gado, inda bayan rasuwarsa Yarima Faisal Ibn AbdulAziz ya zama
sabon sarki na uku.
Sarki Faisal shi ne mutumin da ake ganin har
yanzu Sa’udiyya bata yi shugaba kamarsa ba, ana ruwaito Sarki Faisal a
matsayin wani mutum mai ra’ayin bin addini sau da kafa, mutum ne mai san
yin abu da gaggawa, bai cika wasaba, an bayyana shi a matsayin mutumin
da bai cika yin dariya a bainar jama’a ba. Kullum maganarsa itace yadda
za’a ciyar da addinin Musulunci gaba da kasashen.
A lokacin Sarki
Faisal ne Masarautar Sa’udiyya ta fara samar da kamfanoni da kulla
alaka da kasashen Gulf dan habaka tattalin arzikin yankin. Sarki Faisal
ne ya jagoranci kafa kungiyaar kasashen Musulmi ta OIC, haka kuma, shi
ne Sarkin da ya kafa garin Jeddah a matsayin cibiya ta kasuwanci. Sarki
Faisal ya damu da harkokin addini ainun a zamanin Mulkinsa.
Sarki
Faisal ya rasu a shekarar 1975, inda bayan rasuwarsa ne Yarima na
lokacin kuma Gwamnan Riyadh, Khalid Ibn AbdulAziz ya zama sabon Sarki na
hudu. Sarki Khalid shi ne Sarki na Farko da ya fara tsallaka Hijaz zuwa
kasar Amurka domin yin ziyara da kuma bude ido. Sarki Khalid yayi
kokari wajen kulla alakar kasuwanci tsakanin kasashen yankin Gulf inda
ya samar da kungiyar GCC da ta hada Qatar, Kuwait, Bahrain, Oman,
Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya.
Bayan da Allah ya
yiwa Sarki Khalid Rasuwa a shekarar 1982 ne Fahad Ibn AbdulAziz ya zama
sabon sarki. Sarki Fahad shi ne Sarki mafi dade a kan karagar Mulkin
Saudiyya domin ya shafe Shekaru 23 a matsayin Sarki. Sannan kuma, shi ne
mutum na farko da aka fara yiwa lakabi da Khadimul Haramain
Ash-Sherifain (Custodian of the two holy mosques), Sarki fahad ya kawo
sauye sauye masu yawa a kasar Saudiyya ta fuskar lafiya da ilimi da gina
kasa da habaka tattalin arziki.
Haka kuma, Sarki Fahad shi ne
mutumin da ya tsaya kai da fata wajen ganin an samu ‘yantacciyar kasar
Palasdinu, da kuma tsayawa wajen warware mamayar da Iraqi ta yiwa
Kuwaiti, haka kuma ya tsaya kai da fata wajen ganin an warware rikicin
kasashen Bosnia-Herzegovina, Kosovo, Checniya, Afghanistan, Somaliya da
kuma yankin Kahsmir. Bayan haka, a lokacin Sarki Fahad ya maida hankali
wajen taimakawa kasashen Musulmi matalauta da suka hada da Somaliya da
Bosniya da Afghanistan da sauransu. Allah ya yiwa Sarki Fahad rasuwa a
shekarar 2005, inda Yarima mai jiran gado Marigayi Abdullah ya gajeshi,
Abdullah shi ne mutumin da yafi kowa daukan lokaci a matsayin Yarima mai
jiran gado.
Bayan zamansa Sarki na shida ne Abdullah Bin
AbdulAziz ya zabi kaninsa Nayef a matsayin Yarima mai jiran gado, sai
dai cikin kaddararSa Subhanahu Wata’ala, Yarima Nayef ya riga Sarki
Abdullah rasuwa, inda aka maye gurbinsa da Yarima Salman a matsayin
sabon yarima mai jiran gado. Sarki Abdullah za’a jima ba’a manta da shi
ba, domin ya cigaba da amsa sunan Khadimul Haramain Ash-Sherifain inda
ya kawo sauye sauye masu yawa a Masallacin Makkah da Madina da ba’a taba
gani ba a tarihin Saudiyyah. Yayi aiki tukuru wajen ganin ya hidimtawa
Masallatan Allah masu alfarma. Ya taimaki addinin Allah gwargwadan iko.
Sarki Abdullah ya samar da manya-manyan jami’o’in kimiyya da fasaha da
kere-kere guda biyu da suka hada da Jami’ar King AbdulAzizi da kuma
Jami’ai Noura ‘yar uwar mahainsu. Kafin zamansa Sarki Abdullah ya rike
mukamai da yawa na Minista inda ya rike ministan tsaro da kasuwanci da
cikingida sannan ya zama Gwamnan Riyadh. Sarki Abdullah Bin AbdulAzizi
ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya a lokacin da Saudiyya ta cika
Shekaru 84 da kafuwa. Za a jima ana tunawa da Sarki King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud wajen tsayawarsa kai da fata akan kasar Bahrain wajen ganin bata fada hannun 'yan Shiah ba.
Yanzu dai Yarima Salman Ibn AbdulAziz dan shekara 79 shi ne zai zama
sabon Sarki na bakwai (7), inda shima ya zabi wani matsahi Yarima Mukrim
a matsayin mai jiran gado, kuma shi ne ake zaton mutum na karshe daga
‘ya ‘yan AbdulAziz da zai rike Sarautar Mahaifinsu. Yau in sha Allah
bayan kamala Sallar Juma’ah za ayi jana’izar Sarki Abdullah. Muna yi
masa adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya sa Aljannah ce
makomarsa, Allah ya biyashi ladan hidimar da yayi dakunanSa masu alfarma
a Makkah da Madina, Allah ka yafe masa kurakuransa. Allah ya kyauta
bayansa. Allah ka jikan Musulmi.
22-01-2015
No comments:
Post a Comment