Saturday, January 10, 2015

Akwai Alamun Yiwa GMB Yankan Baya A Wannan Zaben


AKWAI WANI ABU DA KE FARUWA A APC

A wannan karon GMB yayi kokari domin ya nuna gogewa a siyasa kwarai da gaske, idan mutum ya kalli sunayan yan kwamatin yakin neman zaben Buhari zai san cewa GMB ya nuna gogewa domin ya nada kansa Shugaban kwamatin Koli na yakin neman zabensa, sannan ya nada gwamna Amaechi a matsayin babban Darakta, bayan nan kuma ya nada Alh. Atiku Abubakar a matsayin babban mataimaki mai kula da yankin Arewa, a hannu guda kuma ya nada Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin babban Mataimaki mai kula da yankin Kudu.

Siyasar da GMB ya nuna a wannan gabar, ita ce ta dakushe kafafar da shi Bola Tinubu yake yi, idan kullum yake kiran kansa a matsayin JAGORAN APC NA KASA (APC NATIONAL LEADER), anan GMB ya ragewa wancan ikirari na Tinubu karfi, domin shi GMB din ne da kansa ya zama Shugaba, dan haka Tinubu dole yayi biyayya a mtsayin mataimaki babu sauran nuna cewa shi ne APC National Leader a kasa baki daya.

Bayan haka, alamu na nuna cewa akwai wasu al'amura dake faruwa a sha'aninsu Tinubu da suke jin APC tasu ce su yasu, domin, tunda GMB ya kaddamar da yakin neman zabe a Jihar Ribas a kudancin Najeriya, har kawo yanzu da GMB ya halarci jihohi wajen 7, amma ba'a ga keyar Tinubu ba wajen wannan gangamin yakin neman zabe. Dan haka wannan wani siginal ne da yake nuna kodai Tinubu baiji dadin wannan nadin da GMB yayi masa ba, na maida shi mataimaki maimakon kullum ya zama Jagora kamar yadda yake nada kansa, ko kuma akwai wani shiri tsakaninsa da mai-malfa kamar yadda wasu ke dari-dari.

Sannan kuma,  mutane irinsu Gwamna Rochas okorocha da Chris Ngige alamu sun nuna da gaske suke wannan tafiya, domin kuwa tunda aka fara wannan karakaina ta yakin neman zabe dasu ake yi. Bayanai sun nuna cewa, Gwamna Rabiu Musa kwankwaso na Kano da Tsohon Gwamnan Gombe Danjuma Goje da Tsohon Gwamnan Kwara Bukola Saraki da Malam Nasiru el-Rufai duk sunyi kokarin matsawa GMB akan lallai ya dauki Gwaman RIbas Rotimi Fashakin a matsayin mataimakin shugaban kasa, yayinda  shi GMB ya mika wannan dama kacokam ga Tinubu inda ya zabo Osinbajo.

Rashin ganin fuskokin su Kwankwaso, Goje, Bukola, el-Rufai ( duk da cewa el-Rufai shima yana takarar gwamna da take bidar lokacinsa) amma hakan na nuna basu ji dadin rashin daukar Amaechi da ba'ayi ba a matsayin mataimakin Shugaban kasa. Haka kuma, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ba'a ga motsinsa ba a wannan gaganiya in banda ta facebook, watakila ko dan yana Arewa ne ba'a zo yankinsa shi yasa bamu ga fuskarsa aba.

Amma lallai akwai tsoron kada ayiwa wannan tafiya ta GMB yankan baya,a wannan zabe. lokaci dai alkali ne.

Yasir Ramadan Gwale
10-01-2015

No comments:

Post a Comment