Thursday, January 1, 2015

Karshen Shekarar Miladiyyar 2014


KARSHEN SHEKARAR MILADIYYAR 2014

Alhamdulillah, kamar yadda Allah ya nuna mana farkon wannan Shekara haka yauma ya sake nuna mana karshenta. Mun shafe kwanaki sama da dari uku (300) muna gaganiya a cikin wannan Shekara. Al'amura masu yawa sun faru a gurare da dama. Kadan ne na farinciki da jin dadi suka faru a wannan shekara. Abubuwa munana sun faru da yawa. Muna fatan kada Allah ya kuma maimaita mana su a wannan sabuwar Shekara da zamu shiga.

Mutane da yawa sun shiga cikin Halin kunci da damuwa da takaici. Mata da yawa sun zama zawarawa, an mayar da 'ya 'ya da yawa marayu, mutane da dama sun bakunci lahira ba tare da sun san laifukan da suka aikata ba. An làlata dukiya ta dumbin miliyoyi hatta shanu da awaki sunga ta kansu a wannan shekarar.

Kusan kullum labarin da muke bude ido da shi ba na alheri bane. An kashe... an kone... an sace... an yanka... da sauran nau'ukan miyagun labarai haka kusan duk hudowar rana da faduwarta ake fama da su.

Ba shaka Allah SWT yace da Manzo SAW yayi bushara ga masu hakuri. Ya Allah ka sanya mu kasance cikin masu hakurin da zamu yi adabo da wannan bushara taka Subhanahu wata'ala.

A karshen Shekara irin wannan lokaci ne da ya kamata muyi bitar irin abubuwan da muka aikata a baya, munana mu nemi Allah ya yafe mana sannan ya karemu daga sake afka musu. Kyawawansu kuma Allah ya cika mana ladan ya tabbatar da dugadugannmu wajen aikatasu.

A irin wannan lokaci ya dace mu koyi yiwa juna afuwa mu yafewa juna irin laifukan da muka aikatawa kawukanmu muna sane ko bama sane. Ba shakka ni Yasir Ramadan Gwale nasan na yiwa abokaina laifuka da daman gaske, da yawa suna jin haushi na ko dai akan ra'ayina musamman na siyasa ko kuma akan abinda na fada wanda bai musu dadi ba. Ina rokon duk wanda na batawa kuma yake jin haushina akan haka ya yafe min. In sha Allah duk wanda ya batamin ko yasa naji haushinsa akan duk abinda hannuna ya rubuta na yafe masa. Allah mai ahuwa ne yana san ahuwa. Allah kai mana ahuwa ka yafe mana ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Ya Allah ka shiga mana gaba kai mana jagora a dukkan lamuranmu na rayuwa. Allah ka bamu lafiya da zama lafiya a Najeriya. Allah ka amintar da mu à garuruwanmu. KULLU AMIN WA ANTUM BI KHAIR.

Yasir Ramadan Gwale
31-12-2014

No comments:

Post a Comment