Friday, January 9, 2015

Da Buhari Dan kano Ne Ba Shakka Takai Zai Zaba


TABBAS DA BUHARI A KANO ZAI YI ZABE TAKAI ZAI ZABA

Ba ko shakka akan cewa idan da GMB dan Kano ne kuma a kano zai yi zabe, to la shakka Malam Salihu Sagir Takai zai zaba a matsayn gwamnan kano na gaba. Mun kwana da sanin cewa GMB mutum ne dan kishin kasa mai kaunar cigaba, da kaunar aiki tsakani da Allah ba cuta ba cutarwa, GMB mutum ne da bai yadda da kashe mu-raba ba, GMB bai yadda da aikin Baba-Rodo ba, dan haka idan GMB zai yi zabe a kano to ba shakka zai bakace tsakanin 'yan takarar Gwamnan Kano guda biyu sannan ya zabi Takai a matsayin gwamnan kano na gaba, domin shi kansa GMB ya san da cewa yanzu lokaci ne da yake bukatar mutane masu gaskiya da zai iya yin aiki da su ko da kuwa bai hada jam'iyya daya da su ba.

Idan ka Dauki Malam Salihu Sagir Takai yayi Shugaban Karamar Hukuma, yayi Kwamashinan kananan hukumomi, sannan yayi kwamashinan ruwa, wanda ya cimma gagarumar nasara a duk inda yayi aiki. Domin yana Shugaban Karamar Hukumar Takai a APP Gwamnatin Kano karkashin PDP ta yaba da dukkan irin ayyukan da yayi, a saboda haka ma gwamnatin ta gayyaci Shugaban Kasa na lokacin Olushegun Obasnjo yaga ayyukan raya kasa a karamar Hukumar Takai a lokacin.

Haka kuma, lokacin da Takai yana Kwamashinan Kananan Hukumomi, duniya ta shaida cewa karkashin kulawarsa ba'a taba yiwa wata karamar hukuma kwangen kasonta na wata-wata ba, hasalima an gudanar da zaben Kananan Hukumomi a Kano inda kowaanne zababben Ciyama yake karbar kudinsa ba tare da anyi musu wani gibi ba. Malam Takai ya tsaya ya kula da aikinsa na Kwamashina tsakani da Allah tare da tabbatar da cewar kowacce karamar hukuma na karbar kasonta cikin lokaci, wadannan bayanan na nan aje a ma'aikatar Kanan hukumomi inda Takai yayi aiki.

Haka zalika, Malam Salihu Sagir Takai yayi Kwamashinan Ruwa na Kano, inda karkashin Jagorancinsa aka samu gagarumar Nasarar gina Matatar Ruwa irinta ta farko a fadin Najeriya. Takai ya tsaya anyi aiki bilhakki da gaskiya a ma'aikatar Ruwa ta kano dan ganin an samar da Ruwan da zai iya kaiwa zuwa bukatunjama'ar Kano. Haka kuma, an gyara tare da inagnta matatun Ruwa na Watari da Guzu-guzu a lokacin. Wannan wata gagarumar Nasara ce da Takai Ya samu a lokacin da ya jagoranci Ma'aikatar Ruwa a matsayin kwamashina.

Idan kuma muka koma bangaren Mataimakin Gwamna na Yanzu Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ne Kwamashina na ma'aikatar Kananan Hukumomi a zamanin da suka yi gwamnati a Zango na farko da wannan Zango na biyu. Gwamantin Kano Karkashin Jagorancin Gwamna Rabiu Musa Kwankwanso tare da dafawar mataimakinsa Abdullahi Umar Ganduje bata yi zaben Kananan Hukumomi ba sai da ta shafe shekaru uku akan karagar Mulkin, Sannan a iya tsawon wadannan Shekaru da Gwamnati tayi babu zababbun Shugabannin Kananan Hukumomi, Gwamnatin Jiha ce ke karbe kudadan Kananan hukumomi da suke zuwa daga Aljihun Gwamnatin Tarayya, Bayanai sun tabbatar da cewar wannan Gwamnati tayi Mursisi akan kudin Kananan Hukumomin Kano da suka kai har Naira Biliyan 255 a tsawon Shekaru uku babu zababbun shugabanni kananan hukumomi.

Haka kuma, Mataimakin Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana Kwamashinan Kananan Hukumomi, Gwamnatin Kano tayi alkawarin Gina Tituna masu tsawon Kilomita Biyar a kowacce karamar Hukuma, amma sama da kashi 75 na wannan aiki babu shi babu dalilinsa. Anan Facebook na karanta kamar wattani huddu da suka wuce, Hamza Ibrahim Baba dan asalain Karamar Hukumar Dawakin-Tofa  kuma daya daga cikin masu tallata Ganduje, wadda karamar hukumar Abdullahi Umar Ganduje ce, yana kalubalantar rashin yi musu aikin titin karamar hukumarsu, inda yayi korafin cewar an fara an dakatar da aikin, a daidai wannan lokacin ne Mu'azu Magaji Sarauniya wanda shima dan karamar hukumar Dawakin-Tofa ya mayarwa da Hamza martani da cewar laifin Ma'aikatar kananan Hukumomi ne da shi mataimakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke jagoranta na rashin cin-nasarar wannan aiki.

Daga nan aka bude sabon babin muhawara inda nan take Hamza Ibrahim Baba ya kare abin da cewar ai aikin gina wadannan hanyoyi yana karkashin ma'aikatar kasa ne (Land), daga nan shi Muaz Magaji ya sake kalubalantar Hamza cewa ai Kwamashinan Kasa na yanzu shi Ganduje ne ya kawo shi akai masa Kwamashina, domin haka kowanne irin kasawa aka samu laifin na ma'aikatar Kananan Hukumomi nekarkashin jagorancin Mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a cewar Muazu Magaji Sarauniya.

A saboda haka, tayaya GMB zai zabi Abdullahi Umar Ganduje mutumin da ya kasa cimma nasarar gina tituna masu tsawon Kilo Mita Biyar a cikin Shekara Hudu duk kuwa da irin makudan kudaden da aka antayo kananan Hukumomin Jihar Kano daga Gwamnatin Tarayya amma Gwamnatin Jiha karkashin Gwamna da mataimakinsa Abddullahi Umar Ganduje na tare kudin. Dan haka ne, Ya zama wajibi GMB ya zabi cancanta, ya zabi Malam Salihu Sagir Takai mutumin da ya cimma nasarar sama da kashi 90 na aikin gina sabuwar matatar Ruwa ta Tamburawa ta  da babu irinta a Kano, ya tabbatar an baiwa ko wacce karamar Hukuma kasonta ba tare da an rike musu kudade ba. Ba shakka da Buhari dan Kano ne Takai zai Zaba. Dan Haka Al'ummar Jihar Kano Ku Zabi Malam Saluhu Sagir Takai dan Zama Gwamnan Jihar Kano Na gaba.

YASIR RAMADAN GWALE
09-01-2015

1 comment: