Sunday, January 11, 2015

Shugabannin Duniya 50 Sun Hadu A Faransa, Yaushe Ne Shugabannin Afurka 50 Zasu Hadu A Najeriya Dan Jajantawa Mutanan Borno?


SHUGABANNIN DUNIYA 50 SUN HADU A FARANSA, KO YAUSHE SHUGABANNIN AFURKA 50 ZASU HADU A NAJERIYA DAN JAJANTAWA MUTANAN BORNO?

Yau kamar yadda hankalin dukkan manyan kafafen yada labarai ya karkata, Shugabannin kasashen duniya ance yawansu ya kai 50 sun hadu a Paris dan taya Faransa Makokin mutane 12 da aka kashe a makon jiya. Kisan wadannan mutane ya ja hankalinkasashen duniya sosai, ta yadda wasu kasashen da suka shafe Shekara da Shekarau ana kashe-kashe ba ji ba gani, amma sai gasu suna sahun gaba wajen jajantawa Faransa tare da Allah-Wadai da wadannan maharan da suka kashe mutum 12.

Idan ba'a mantaba wannan gidan Jarida da aka kaiwa wannan hari, ita ce Jaridar da ta dinga zana hotunan batanci ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammas Sallallahu Alaihi Wasallam. A lokacin da wannan Jarida take yada wadancan hotuna na batanci tare da bakantawa Musulmi Rai, gani ake 'yancin fadin albarkacin baki ne, da 'yancin bayyana ra'ayi, a lokacin mafiya yawancin Shugabanni sunyi gum da bakinsu, aka bar mutanan da aka kira zauna gari banza sukai ta zanga-zanga suna Allah-wadai. To Allah ba zai taba barin wanda ya taba martabar ManzonSa SAW ya zauna lafiya ba.

Babban abinda ya bani mamaki a wannan gangami na nuna alhini da goyan baya da manyan kasashen duniya sukaiwa Faransa, shi ne haduwar Primamistan Palasdinawa Mahmoud Abbas Abu-Mazin da Piraministan Israeli Benjamin Netanyahu - בנימין נתניהו. Inda dukkansu suka hadu a Paris suna Allah wadai da kisan da akayi. Sun manta da dukkan rayukan da Israeli take kashewa na Palastinawa, wannan ya tabbatar da shi kansa Mahmoud Abbas Abu-Mazine makaryaci ne mara kishi ne kamar yadda aka jima ana masa zargi. Duniya Mai Abin Mamaki!

Tambayar da nayi it ce, mu anan Afrika yaushe ne Shugabannin wannan Nahiya zasu hadu a Abuja dan taya Najeriya zaman makokin hare-haren da ake kaiwa Borno da Yobe da sauran jihohin Arewa babu kakkautawa? Ana kashe al'umma ba kakkautawa amma Shugabannin Afrika basa nuna wata damuwa. Yaushe ne SHugaban Nijar Mouhammadou Isoufou da IBK na Mali da suka ja faransa zaman Makoki zasu maida hankali wajen kula da rayukan al'ummarsu.

Yaushe ne Shugaban kasar Najeriya zai je katse dukkan hidndimun Gwamnati dan taya al'ummar Borno da Yobe alhinin abinda ke faruwa? Allah yana bamu shugabanni daidai da irin halayyarmu, idan mun sauya Allah zai sauyamu, idan bamu sauya ba, zamu jima muna zargin juna akan halin da muke cikin na rashin shugabanci na gari.

YASIR RAMADAN GWALE
11-01-2015

No comments:

Post a Comment