NIGERIA-ISRAELI: DUK WANDA YACI LADAN KUTURU...
A makon da ya gabata ne, Najeriya karkashin Shugabancin Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan
ta hannun jakaddiyar najeriya a majalisar Dinkin Duniya ta aikata
babban abin kunya a majalisar dinkin duniya, inda ta zabi marawa Israeli
baya akan goyan bayan samar da 'yan tacciyar kasar Palasdinu a matsayin
cikakkiyar kasa kamar kowacce. Kasancewar Najeriya kasa ce mai rinjayen
Musulmi duniya tayi zatan cewa Najeriya zata kasance tare
da Palasdinu duba da cewa akwai tsohuwar alaka da dangantaka tsakanin
Najeriya da Palasdinu, domin kuwa Marigayi Shugaban Palasdinawa Mallam
Yassir Arafat ya taba kawo ziyara Najeriya zamanin Gwamnatin marigayi
Gen. Sani Abacha.
Najeriya
ta lalata waccan tsohuwar dangantaka ne ta hanyar kasancewa tare da
Israeli dake zaman haramtacciyar kasa a idon Musulmi da dama. Amma ga
dukkan wanda yake bibiyar abubuwan da ke faruwa tsakanin Najeriya da
Israeli a 'yan kwanakinnan ba zai yi mamaki wannan mataki da Najeriya ta
dauka ba, domin kuwa dangantaka ta kullu tsakanin Shugaba Jonathan na
Najeriya da Piraministan Israeli Benjamin Netanyahu - בנימין נתניהו,
duba da yadda ake cewa kamfanonin Israeli na samun kwangiloli a
Najeriya da kuma irin ziyarar da shugaban Najeriya ke kaiwa Israeli da
sunan Ibada.
Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan yana cikin tsaka mai wuya, ta yadda manyan kasashen duniya da dama irinsu Amerika da kasashen turai basa tare da gwamnatinsa, inda ake masa ganin mugun shugaban kasa wanda ya kasa yin wani katabus dan ceto 'yan matan Chibok, domin kuwa an jiyo Shugaba Obama da mukarrabansa na gwabawa Najeriya a kan batun 'yan matan Chibok, haka manyan sanatoci a majalisar dattawan Amerika irinsu John McCain duk suna yiwa Shugaba Jonathan shagube akan batun matan Chibok da aka sace.
A tunani na wannan ce ta sanya Shugaban kasa Jonathan kasancewa tare da Israeli, domin kuwa muddin Dr. Jonathan yana yana tare da Israli kuma tana agoyon bayansa, to kuwa babu wani dalilaai da zai sanya Amerika da kasashen turai su ki goyawa Mr. Jonathan baya, domin duk wuya duk runtsi mun san Amerika da turai sunaa tare da israeli. Daman duk wanda yaci ladan kyuturu dole ya yi masa saisaye, domin kuwa da jonathan da netanyahu duk sunci ladan juna.
Daga karshe muna barrantar da kanmu daga wannan mara baya da Najeriya ta yiwa Israeli. Na tabbata babu wanda zai ji dadin wannan abin da Najeriya ta yi sai 'yan SHIAH masu bautar son rai. Wa Makaru Wa Makarullah...!
Yasir Ramadan Gwale
03-01-2015

No comments:
Post a Comment