NIJAR: SHUGABA MOUHAMMADOU ISOUFAOU MUNA JIRAN KA KA NUNA FUSHI AKAN BATANCIN DA JARIDAR FARANSA TAI AKAN MANZON ALLAH SAW
Shugaban Jimhouriyar Nijar Mouhammadou Isoufou na daya daga cikin
Shugabannin kasashen duniya 50 da suka hadu a birnin Paris a kwanaki
biyu da suka wuce, inda suka nuna alhini tare da nuna cikakken goyan
baya ga uwargijiyarsu Faransa akan abinda suka kira da "Harin
Ta'addanci" da aka kaiwa Jaridar Charlie Hebdo, wacce ta yi batanci ga
Manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW).
Shugaban NIjar Mouhammadou Isoufou ba shi kadai ne shugaban kasar
Musulmi da ya halarci wannan gangami ba, akwai shugaban kasar Mali IBK
da shugaban Palasdinawa Muhamud Abbas Abu Mazine da Sarkin Jordan.
Dukkansu sunyi Allah wadai da abinda akaiwa wannan la'annaniyar Jarida
sun kuma tausayawa kasar Faransa da iyalan wadan da aka hallaka. Sai
gashi a jiya wannan jarida La'ananniya ta kuma yin zanen batanci ga
cikamakin Annabawa Manzon Allah SAW.
Ba shakka, wannan ya zama wajibi ga Shugaba Isoufou da ke zaman kwabci a garemu, muyi kira a gareshi da kakkarfar Murya akan ya fito fili yayi Allah wadai da wannan aikin ta'addanci da wannan Jarida tayi, ko kuma mu lissafashi sahun makiya musulunci, masu yiwa addinin Allah zagon kasa. Wadan da suka fifita martabar Duniya kan ta lahira. Martabar Manzon Allah tafi Martabar kasar Faransa da tarayyar Turai a idan al'ummar Musulmin Kasar NIjar baki daya. Dan haka muna kira ga Shugaba Isoufou da ya fito fili balo-balo yayi Allah wadai da wannan jarida kamar yadda yayi Allah-wadai ga maharan da suka kashe ma'aikatan ta.
Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai. Allah ka rusa wannan Jarida ka hada su da dukkan dangin bala'in duniya da lahira. Allah ka lalatasu ka wargaza sha'aninsu gaba daya.
YASIR RAMADAN GWALE
13-01-2015

No comments:
Post a Comment