Wednesday, June 4, 2014

WAZIRIN KANO: Mai martaba Sarkin Kano Ya Nuna Dattako!

WAZIRIN KANO: MAI MARTABA SARKIN KANO YA NUNA DATTAKO!

Kwana hudu bayan da Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dakta Ado Abdullahi Bayero ya nada sabon Wazirin kano bayan rasuwar Sheikh Isa Waziri, turka turka ta kaure tsakanin fadar mai martaba Sarki da fadar Gwamnatin Kano, inda ta bakin mataimakin Gwamna Abdullahi Ganduje, gwamnati ta bayar da sanarwar kin amincewa da nadin da mai martaba Sarki ya yiwa Sheikh Nassir Nassir Muhammad a matsayin sabon wazirin Kano, ta kuma umarci fadar maimartaba Sarki akan ta warware wannan nadi da ta yiwa Sheikh Nassir a cewar Gwamnati al'umma basu yi na'am da nadin na Waziri da aka yiwa Sheikh Nassir ba.

Wannan shi ne karo na farko da sa'insa irin wannan ta faru a bainar jama'a tsakanin Masarauta da Gwamnati. Sananne ne a tsarin Mulki cewar gwamnati tana gaba da masarauta a sha'anin iko da gudanar da al'amuran mulki na al'umma. Duk da cewa wannan nadi da maimartaba Sari ya yi, hakkinsa ne ya nada duk wanda yaga dama a matsayinsa Wazirinsa a cikin fadarsa. kamar yadda ya tabbata a tarihi, a lokacin Sarkin Kano Alu Dan Abdullahi Maje-Karofi aka fara nada wannan sarauta ta wazirin Kano, kuma ya nada wannan sarauta ne ga mafi kusanci da shi, kuma daman bisa ga al'ada a lokacin akan kira dukkan wani wanda yake da kusanci da Sarki kuma Shakuwarsu da Sarki ta bayyana da sunan Wazirin Sarki, ance a lokacin Sarki yafi shakuwa da Dansa kuma Galadiman kano Abdullahi a lokacin da haka Sarki ya nada sh Wazirin Kano kuma Galadiman Kano, tundaga wannan lokacin aka fara ayyana Wazirin kano.

 haka kuma, zamanin Sarki Alu ya nada wansa Ahmadu Mai Shahada a matsayin Wazirin Kano. haka nan, bayan shudewarsa Sarki Abbas ya nada Audu-Lele dan gidan tafidan kano Muhammadu maje-takai a matsayin Wazirin kano; bayan da turawan Mulki suka tunkude  ne tare da dukkan hakimansa da manyan fada suka nada wani bawan Sarki mai suna Dan-Rimi Ala-Bar Sarki a matsayin sabon Wazirin Kano; daga nan ne kuma Sarki ya cire wannan bawa ya nada wani malamin Addini mai suna Gidado a matsayin sabon Wazirin Kano; bayan rasuwar Malam Gidado ne kuma Sarkin Kano Abdullahi Bayero ya so ya nada wani Shehin Malami mai suna Sulemanu wanda shi ne Ma'ajin kano kuma aminin Sarki ne a matsayin sabon Waziri amma jama'ar gari suka nuna rashin gamsuwa da yunkurin nadin Malam Sulaimanu da Sarki yake son yi a matsayin sabon Wazirin Kano, a lokacin ne Mai Babban Daki Mariyatu Mai-Harara ta sanya Sarki janye wannan nadin da ya yi niyyar yi, a dan haka sai ya sauyawa Sulaimanu Sarauta inda ya nada shi Walin Kano kuma ya damka dukkan ayyukan waziri a hannunsa.

A dan haka ne, mai Martaba Sarki a lokacin ya fasa nada Wazirin Kano har kusan tsawon Shekaru 23 babu Wazirin Kano. Wannan a takaice yana nuna cewar sarautar WAZIRIN KANO Sarauta ce Wadda Sarki yake nada ta ga Aminansa wadan da suke ko dai limamai ko kuma Malamai masu ilimi. A saboda haka idan Mai-martaba Sarki ya nada Sheikh Nassir da aka fi sani da DAN CHAKARE a matsayin Wazirin Kano Sarki bai yi wani abu na kauce ka'ida ba, domin a al'adar nadin Sarautar Sarki na da ikon nada wanda yaga dama.

Duk da cewar Mai Martaba Sarki Allah ya kara masa Lafiya, yana da masaniyar cewar hakkinsa ne ya nada wanda yaga dama a matsayin Waziri amma ya yarda ya sarayar da wannan hakki nasa dan samun dorewar zaman lafiya tsakanin fadar Gwamnati da Masarauta, babu ko shakka Mai Martaba Sarki ya nuna Dattako a janye wannan nadi da ya yi.

ME YA SA MUTANE BASA SON DAN CHAKARE A MATSAYIN WAZIRIN KANO? Wannan shi ne abinda zamu duba a rubutu na gaba In Sha Allah. muna fatan Allah ya kwantar da wannan kura da ta taso tsakanin gwamnati da Masarautar kano. Allah ya taimaki Sarki ya karawa Sarki lafiya.

YASIR RAMADAN GWALE
04-06-2014

No comments:

Post a Comment