RIDDA A SUDAN DA KANO
A jiya muka ji labarin matarnan da ta yi ridda ta bar addinin Musulunci a kasar Sudan cewa ta haihu a gidan kaso inda kuma kotu ta bayar da umarnin a saketa bayan da matar Mariam Ibrahim Yahya ta daukaka kara akan hukuncin da kotun farko ta yanke mata na haddin kisa ta hanyar rataya. Ita dai Mariam Yahya Ibrahim ta auri mijinta Daniel Wani dan kasar Amurka, inda daga bisani ta bar Musulunci ta koma Kiristanci bayan da suka yi aure. Har ya zuwa jiya da ta shafe kwanaki 21 a gidan yari ana tsare da ita, Mariam bata gamsu ta sauya addini daga kiristanci ta dawo Musulunci ba ta cigaba da kafewa akan addinin Kirista.
Kwatsam kuma, a wani labari mai kama da wannan, sai muka ji a Kano ma wani matashi Mubarak Bala ya yi ridda ya bar Musulunci, duk da bayanan da suka fito sun nuna cewar shi Mubarak Bala ya nuna bai yadda da samuwar ubangiji ba ne, Wal Iydhu Billah! Lallai wannan abu ne mai tayar da hankali ace mutane suna fita daga Musulunci suna komawa kiristanci a garuruwan da suke da kusan Musulmi dari bisa dari.
Sanin kowa ne Sudan kasa ce ta Musulunci kamar yadda Kano gari ne na Musulunci amma ace irin haka ta faru wadannan mutane sun bar Musulunci a garin Musulunci. Ba shakka akwai tashin hankali a cikin batun.
Dan haka, Addinin Musulunci ya yi tanadi akan wadan da suka bar Musulunci suka koma wani addinin daban, Malamai zasu yi bayanin irin hukuncinsu, musamman shi Mubarak Bala In Sha Allah, haka kuma wajibin hukumomi ne su tabbatar da zartar musu da hukuncin da yake kansa a Musulunce.
A gefe guda kuma, daga cikin munafukan kungiyoyin Shaidan dake kasashen Turai da Amurka sun samu dama ta yin abida suke so wajen nuna dole a baiwa kowa 'yancin yin addinin da yaga dama, wanda ko muma a Najeriya kundin tsarin Mulkinmu ya yi tanadin baiwa kowa damar yin addinin da yaga dama, amma dai babu shakka idan har Mubarak Bala bai dawo daga wancan tunani ba, dole a jingine kundin tsarin Mulki a yi masa hukuncin da Musulunci ya tanada. Allah ya shiryi al'ummarmu.
YASIR RAMADAN GWALE
25-06-2014

No comments:
Post a Comment