Friday, June 6, 2014

Mutum Shida Ne Manya A Kano: Mai Martaba Sarki Ne Babbansu

Marigayi Alh. Ado Abdullahi Bayero
MUTUM SHIDA NE MANYA A KANO: MAI MARTABA SARKI NE BABBANSU

Jihar Kano Allah ya hore mata mutane masu yawa kama daga Malamai da Attajirai da Sarakuna da 'yan Boko da sauransu. A baya-bayan nan Manyan Dattawa 6 ne a Kano wanda ake damawa da su a harkar Sha'anin tafiyar da mulkin al'umma jihar Kano da kasa baki daya, haka kuma, 'yan Siyasa a Matakai na Gwamnatin Tarayya da Jiha da kananan Hukumomi suna jin maganarsu kuma sun isa da kowa a kano akan duk abinda ya shafi al'umma.

Na farko Shi ne, Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero.

Na biyu shi ne, Alh. Aminu Alhassan Dantata.

Na uku shi ne, Khalifa Isiyaka Rabi'u.

Na hudu shi ne, Alh. Yusufu Maitama Sule (Danmasani Kano)

Na biyar shi ne, Alh. Magaji Danbatta.

Na shida shi ne, Alh. Tanko Yakasai.

Idan ana maganar jihar Kano to la shakka babu dattawa kamar wadannan mutanen, su ne wadan da suke da ruwa da tsaki akan dukkan wasu al'amura da suka shafi tafiyar da rayuwar al'umma a jihar Kano da kasa baki daya. wadannan mutane su ne wadan da gwamnati tafi jin maganarsu sama da ta kowa a sha'anin al'umma, Gwamnati na tafiya da su domin samun bakin zaren aiwatar da Shugabancin jama'a lami lafiya.

Babba kuma Jagora, jigo a cikin wadannan jerin Gwano shi ne Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Abdullahi Bayero wanda ya kwanta dama a yau din nan. Babu shakka rasuwar Mai martaba Sarki ta haifar da wani wagegen gibi a jihar Kano. Samun dama irin wadda Mai martaba Sarki ya samu ta tsawon Shekaru da tsahon wa'adin Mulki kalilan ne daga cikin mutane suke samu.

Babu shakka dukkan wanda zai biyo bayan Mai Martaba Sarkin Kano, a matsayin sabon Sarki zai hadu da kalubale mai yawa wajen tafiyar da al'amuran jama'a kamar yadda Sarki ya yi. Sanin duk mutumin Kano ne, Mai Martaba Sarki mutum ne da ya yi nasa kuma yayi na jama'a, mutum mai kaunar jama'a, mai kiyaye ka'ida, mai bin doka, ba shida kwadayi, mai kula da lokaci, mai son yara da tausaya musu, mai cika alkawari. Lallai anyi rashi babba, Allah ya jikan Sarki ya gafarta masa ya sa Al-Jannah ce makomarsa, kurakuransa Allah ya yafe masa. Allah ya zaba mana madadinsa wanda zai dora daga inda ya tsaya da gaskiya da adalci da rikon Amana da tausayi da jin kai. Allah ya ka jikan sauran musulmi a duk inda suke.

YASIR RAMADAN GWALE
06-06-2014

No comments:

Post a Comment