SABON SARKIN KANO: KADDARA TA RIGA FATA
Ina mai amfani da wannan damar wajen sanar da al'umma musamman wadan da sukai ta turmin sakon Inbox wadan da hannuna yakai garesu da kuma wadan da hannuna bai kai garesu ba, da wadan da suka kirani a yawa tun jiya, cewar ni Yasir Ramadan Gwale ina taya sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi murnar zama sarkin Kano da ya yi a jiya. Allah ya yi masa jagoranci, Allah ya yi riko da hannunsa wajen aiki da daidai.
Babu shakka, zuciyarmu ta kadu, rai ya sosu da muka ji cewar ba Chiroman Kano Alhaji Samusi Lamido Ado Bayero aka zaba ba a matsayin sabon Sarkin Kano. Wannan kuma ba shi ne yake nuna cewa bamu yarda da kaddara ba, ai akan yiwa mutum mutuwa yaji zafi har yayi kuka, daga karshe kuma ya mika lamarinsa ga Allah, kuma Allah ya bashi ladan hakuri, dan Allah shi ne yake hukuntawa. Idan sanmu ne Chiroman Kano ya zama Sabon Sarkin Kano, tunda kuma Allah bai hukunta masa ba, munji mun bi, sami'ina wa'ada'ana.
Allah ya jikan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Allah ya kai rahama gareshi. Ina kuma amfani da wannan damar wajen kara sanar da 'yan uwa kamar yadda Malaminmu Dr. Bashir Aliyu Umar ya sanar a shafinsa cewa, lallai Sabon Sarkin Kano ba dan Shi'ah bane. Ina kuma kira ga daukacin al'ummarmu da su yi hakuri da Abinda ya zo haka ba wanda aka zata ba, a Musulunci biyayya ga Shugabanni wajibi ne ko da kuwa ba akan daidai Shugabannin suke ba, matukar ba umarni suke yi da sabn Allah ba.
Allah ya ja zamanin Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, ina kuma amfani da wannan dama har iala yau wajen yin kira ga sabon Sarkin Kano da ya nada Dakta Bashir Aliyu Umar a Matsayin Sabon Wazirin Kano, ina da yakinin hakan zai sanya Natsuwa a zukatan da dama wadan da suke jifansa da Shi'anci. Allah ya zaunar da kasarmu lafiya, ya zaunar da Kano lafiya, masu bore kuma ayi hakuri a karbi abbinda ya faru a matsayin kaddara. Daman Imani baya cika sai mun yarda da kaddara mai kyau da mara kyau.
Daga Karshe ina mika Ta'aziya ta ta rasuwar tsohon Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ga Mai Girma Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau, ina kuma taya shi murnar nada abokinsa Dan Majen Kano a matsayin sabon Sarkin Kano. Na gode.
09-06-2014
No comments:
Post a Comment