RISALA ZUWA GA MAI MARTABA SARKIN KANO MALAM SANUSI LAMIDO SANUSI
Bismillahir Rahmanir Rahim. Ina fara bude wannan Risala da sunan Allah, mai gamammiyar Rahama, mai gamamman jin 'kai, tsira da AmincinSa su 'kara tabbata ga fiyayyan halitta, Manzon tsira cikamakin Annabawa, Annabi Muhammad SAW da alayensa da Sahabbansa masu daraja da wadan da suka biyo bayansu da kyautatawa har yazuwa ranar sakamako. Dukkan wanda Allah ya shiryar da shi shi ne hakikanin shiryayye, wanda duk Allah ya batar babu mai iya shiryar da shi.
Da farko, ina mai yin amfani da wannan dama, wajen kara mika ta'aziyata ga sabon Sarkin Kano Mallam Sanusi Lamido Sanusi, a bisa rasuwar tsohon Sarkin Kano Alh. Ado Abdullahi Bayero, Allah ya jikansa ya gafarta masa, Allah ya kyauta bayansa. Ina kuma kara taya Mai Martaba Sarki murna da kuma alhini; ina taya Mai Martaba Sarki murnar zama sabon Sarkin Kano na 14 a dangin Sullubawa, na 57 a tarihin Masarautar Kano, ina kuma taya Mai Martaba Sarki jimamin abubuwan da suka faru yayin wannan nadi na shigar al'amuran siyasa da boren da wasu fusatattun matasa suke yi, babu shakka wannan abin bai yi dadi ba.
Haka kuma, ina amfani da wannan damar wajen yin kira ga sabon Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi, da ya yi watsi da dukkan al'amuran siyasa da suka faru a yayin wannan nad'in sarauta, ya rungumi al'ummar Kano da kasa baki daya dan samun zaman lafiyarsa da dorewar mulkinsa. Ya Mai Martaba Sarki, hakika shigar al'amuran siyasa cikin wannan abu bai yi mana dadi ba, domin dukkan masu mulkin siyasa wa'adi garesu takaitacce da baya wuce shekaru 8 a yayinda Sarki ke da wa'adin iyakar rayuwarsa.
Ya mai martaba sarki, a dan saboda a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da dorewar Mulkin sarautar jihar Kano, ina kira a gareka da ka rungumi dukkan masu mulkin siyasa daga ko wace jam'iyya suke dan hidimtawa al'umma. Abu ne mai muni, amfanin da 'yan siyasa suka yi da wannan kujera ta sarautar Kano dan biyan bukatunsu na siyasa, wanda a karshe babu wanda za'a bari a cikin al'amarin sai ita masarautar Kano.
Ya Mai Martaba Sarki, adawa ko nuna tirjiya ga gwamnatin tarayya wadda it ace Gwamnatin koli a Najeriya babu abinda zai janyo mana face faduwar daraja da zubewar girma da gurbacewar al'amura, lallai ne, Mai Martaba Sarki ya yiwa Gwamnatin Tarayya da'a da biyayya wajen ciyar da rayuwar al'umma gaba, kin yin hakan babu abinda zai haifar face rashin nasara da rashin biyan bukatu.
Ya isa abin misali yadda marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero ya kame kansa daga shiga al'amuran siyasa da daukar bangare daya, tafiya da kowa tare da rashin nuna bambanci ko wariya na daga cikin sirrin nasarar mai martaba sarkin kano Allah ya kai rahama gareshi.
'Yan siyasa suna yin komai ne dan biyan bukatunsu na siyasa ba tare da la'akari da halin da al'umma ta ke ciki ba. Su wadannan 'yan siyasar da suka shigo cikin wannan al'amari ba sunyi abinda suka yi bane, dan nuna kishi ga al'ummar jihar kano, illah manufarsu ta siyasa ta bakantawa gwamnatin tarayya da suke hamayya da ita rai, tare da cimma nufinsu na siyasa, bayanan da suke fita daga bakunansu sun tabbatar da hakan.
A lokacin zaben 2011, Gwamnan jihar Nassarawa Aliyu Akwe Doma ya sanya sarakunan jihar a cikin al'amuran siyasa wanda hakan ya janyo musu zubewar kima da daraja da jefa su cikin wulakanci da kaskanci, sai da takai an fasa motar da Sarkin lafiya yake ciki, aka janyo rawaninsa ya fadi kasa, a dalilin halin da gwamnan jihar ya sanya shi na nuna adawarsa karara ga jam'iyyar Adawa ta Buhari, inda gwamnan ya umarce su da kada su sake su karbi tawagar Buhari da zata zo yakin neman zabe cikin fadarsu, wannan al'amari bai yi musu kyau ba, akan biyayyar da suka nunawa Gwamna ta yadda suka sanya kansu a cikin sha'anin siyasa, yanzu dai gwamna y agama wa'adinsa ya tafi su kuma suna nan a matsayin sarakuna, wanda wannan ba komai zai janyo ba sai da na-sani.
Ya Mai Martaba Sarki, kada ka saka kanka a cikin wani yanayi irin wannan, ta yadda Gwamnatin Kano da ke hamayya da gwamnatin tarayya zata sanyaka cikin sha'aninsu na siyasa, sanya kai cikin wannan al'amari babban koma baya ne ga masarautar Kano da kuma al'ummar kano, Mai Martaba Sarki uban kowa ne, dan siyasa da wanda ba d'an siyasa ba, talakawa da masu kudi. Kaucewa shiga sha'anin siyasa shi ne abinda zaifi zamarwa Mai Martaba Sarki alheri da mutunci a idan duniya. Sanin kanmu ne, shugabanni na siyasa sune a gaba, sune wadan da suke da Kotu da 'yan sanda da kuma uwa uba dukiyar al'umma ke karkashin kulawarsu, lallai tafiya tare dasu wajen ciyar da al'umma gaba shi ne yafi komai muhimmanci ga Mai Martaba sabon Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi, rashin hakan kuma ba zai haifar da d'a mai ido ba.
A dan haka, wannan ba yana nufin Sarkin Kano ya je ya kwantawa gwamnati ta taka shi irin yadda taga dama ba. Yana da kyau, Mai Martaba Sarki ya hada kai da gwamnati wajen ciyar da al'ummar kano gaba. Ita gwamnati ba zata taba kame hannu wani mahaluki ya zamar mata karfen kafa a sha'anin tafiyar da gwamnati ko Mulkinta ba! Ya isa abin misali, Sardaunan Sokoto tsohon Firimiyan Jihar Arewa, wanda shi ne mutanan Arewa suka rika a matsayin shugaba na kurkusa mafi Adalci a mulkinsa, amma kuma a gefe guda shi ne ya kawar da rawanin sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
Mun ga yadda al'amuran siyasa suka mamaye Sarautar Sarkin Musulmi Dasuki wadan da basu yi dad'i ba, haka kuma, munga yadda siyasa ta shiga tayi awan gaba da Mai Martaba Sarkin Gwandu Almustapha Haruna Jakwalo, wadannan dukkansu siyasa ce ta shiga ta damalmala al'amuran sarautarsu ta nemi zubar da kimar masarautunsu.
Dan haka, kame kai daga shiga harkokin siyasa ga Mai Martaba Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi tare da rungumar kowa, shi ne abinda zai fi zama alheri a tsawon wa'adinsa, kuma zaifi jawo masa kima da mutunci a idan duk wata gwamnati da zata zo ta tafi, idan muka bari sarauta ta koma kamar mulkin siyasa, to haiba da muhibba da kwarjini na sarakuna ya gama zubewa kasa warwas, haka kuma masarautar Kano alkibla ce ta sauran dukkan masarautu da ke fadin tarayyar Najeriya.
Wadannan fitintinu da ke faruwa da wadan da ke shirin faruwa Allah ya tsagaita su, Allah ya kawar mana da dukkan wani abin 'ki da Alla-wadai. Ina kara jaddadawa Mai Martaba Sarki uban kowa ne ba tare da la'akari da siyasar da mutum ke bi ba. Allah ya taimaki Masarautar Kano da sauran masarautun Najeriya baki daya, Allah ya tabbatar mana da dawwamammen zaman lafiya. Allah ya warware wannan sabatta juyatta da ke faruwa.
11-06-2014
No comments:
Post a Comment