JAN KUNNE DANGANE DA BATUN MUBARAK BALA
Na bibiyi yadda naga ‘yan uwa da dama suna yin tsinuwa tare da la’anta ga Mubarak Bala a saboda abinda ya faru da shi. Babu shakka wannan kuskure ne mai girma dan wani dan uwa Musulmi yayi abinda yake kuskure ne a dinga aibata shi maimakon yi masa addu’ar shiriya. Alal akalli duk wanda ba zai iya yiwa wannan bawan Allah addu’ar shiriya ba, to kamata ya yi mutum ya kame bakinsa daga fadin mummunar Magana akan shi. Duk cikinmu babu wani wanda yake da garantin shiga Al-Jannah, babu wanda aka rubata masa cewa shi dan al-jannah ne, illa kawai fata da kwadayin Rahamar Allah da muke yi a ko da yaushe. Naji takaicin irin kalaman da wasu suka dinga yi babu linzami kamar su din suna da wata masaniyar cewar an lamunce musu Al-Jannah.
Yana da kyau ‘yan uwa su sani, Annabin Allah Nuhu AlaihisSalam, shi ne Annabin farko da Allah ya aiko zuwa doron duniya domin ya shiryar da mutane zuwa ga hanyar Allah, amma Allah ya kaddara mutane kalilan ne suka yi Imani da Annabi Nuhu AS, daga cikin wadan da ba su yi imani da shi ba har da d’ansa na cikinsa, wannan kuma haka Allah ya hukunta, shiriya tana hannunsa Subhanahu Wata’ala. Namu kawai shi ne isar da sakon ga al’umma Allah kuma shi ne yake juya zukatan bayinsa.
Annabin Allah Lud AS shima daga cikin wadan da ba su yi Imani da shi ba har da matarsa (iyalinsa). Allah shi ne buwayi gagara misali kuma shi ne yake jujjuyawa zukatan bayinsa Subhanahu Wata’ala, haka ya kaddara duk da kafirci da mutakabbiranci irin na Fir’auna amma matarsa ta kasance ‘yar Al-jannah tsarki ya tabbata a gareshi.
Wata rana Manzon Allah SAW yana cikin taron Sahabbai sai aka kawo wani mutum ya sha giya, aka yi masa bulala, bayan wani lokaci aka sake kawo wannan mutum, aka kuma yi masa bulala akan laifin shan giya, an yi masa haka har sau uku, sai wasu daga cikin Sahabbai suka dinga aibatashi akan laifin da yake aikatawa! Manzon Allah SAW yace da su shin zaku taimakawa Shaidan akan dan uwanku ne, ko zaku taimakawa dan uwanku akan Shaidan! Manzon Allah SAW yace da su, idan kuka aibatashi kuka la’ance shi, Shaidan yaci nasara akansa, amma idan kuka yi masa addu’ar fatan shiriya, sai ku taimakeshi yaci Nasara akan Shaidan La’ananne.
Da yawa naga suna tuhumar Iyayan Mubarak Bala cewa laifinsu ne da basu bashi tarbiyya ba. Wanda duk wanda ya jingina laifin zuwa ga iyayansa hakika ya zalunce su, duk wanda yasan Dakta Bala Muhammad tsohon Darakta Janar na hukumar Adaidaita Sahu ta jihar Kano, yasan mutum ne mai cikakkiyar tarbiyya ta addini, mai kuma san dukkan wasu lamaura da suka shafi addinin Musulunci, Bala Muhammad tsohon ma’aikacin gidan Radiyon BBC ne, dan haka mutane su koma su tambayi me ya sa Bala Muhammad ya bar aikin BBC, ya bari ne a saboda kishinsa da kaunarsa da tarbiyya irin ta addinin Musulunci.
A baya-bayan nan kafin zamansa shugaban hukumar Adaidaita Sahu ta jihar Kano. Bala Muhammad mutum ne mai yawan halartar tarukan kungiyoyin addinin Musulunci a ciki da wajen Najeriya, duk wadan da suka yi harkar MSSN a Najeriya zasu shaidi Bala Muhammad da juriya da san taimawa addini ta kowanne fanni. Dan haka zai zama zalinci a zargi Bala Muhammad da cewa bai bawa iyalansa tarbiyya ta Musulunci ba.
Bahaushe yana cewa ka haifi Mutum ne baka haifi halinsa ba. Wannan abu da ya faru da shi kansa Mubarak Bala abu ne da kusan yake sabo a cikin al’ummarmu, ace mutum ya fito irin haka cewa ga wani yayi Ridda a bainar jama’a, sau da dama irin haka kan faru ba tare da ansani ba. Kuma abinda yafi wanda Mubarak Bala ya aikata yana faruwa a cikin birnin Kano.
Ansha samun mabiya wata darika na ikirarin cewa Shehunsu shi ne Allah Wal’Iyazubillah. Wasu da dama kan kira kansu da Alloli, wannan wata tsohuwar shirkace da anjima ana yinta a jihar Kano, duk kuwa da masu yi din suna ikirarin su Musulmai ne, amma zaka ji a lokuta da dama bayanansu ko wakokinsu suna kore samuwar Allah Subhanallah, mutane zasu iya tuna irin wannan da ya faru da wani mawaki wanda ta kai har Khalifa Isyaka Rabiu ya fito ya barrantar da kansu daga kalaman da mawakin yayi na shirka, wanda har yanzu mawakin ba’a jishi ya yi nadamar abinda ya aikata ko ya nuna cewa kuskure ya yi ba.
Dan haka, a halin da muke ciki bin sahihiyar koyarwar addinin Musulunci da ta kunshi Al-Qur’ani da Hadisan Manzon Allah SAW it ace kadai mafita a garemu wajen kaucewa fadawa hanyoyin shaidan La’ananne. Lallai ne mu lizimci wajen da ake yin karatun addini mu kuma lizimci tuntubar Malamai a duk lokacin da wasu al’amura suka shige mana duhu dan samun waraka.
Muna addu’ar Allah ya shiryi wannan bawa nasa Mubarak Bala ya dawo kan hanya madaidaiciya, ya ganar da shi kuskurensa, ya fahimtar dashi addinin Musulunci shi ne addini a wajen Allah. Allah ka shiriyi al’ummarmu shiriya ta addini, Allah ka tabbatar da duga-duganmu wajen yi maka da’a da bauta. Allah ka shiryemu shirin addini.
YASIR RAMADAN GWALE
27-06-2014
No comments:
Post a Comment