Wednesday, June 11, 2014

Chiroman Kano: Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero


CHIROMAN KANO: ALHAJI SUNUSI LAMIDO ADO BAYERO!

Mai Martaba Sarkin Kano Mai rasuwa, ya haifi babban dansa Sunusi wanda aka yiwa alkunya da Lamido yana da shekaru 26 a duniya. An haifi Sunisi a shekarar 1956 a unguwar Chiranchi a yankin karamar hukumar Gwale inda nan ne inda Marigayi Sarki ya fara zama da iyalinsa, kuma nan ne inda Chiroman yake zaune da iyalinsa yanzu haka. Babban dan Sarki Sunusi Ado Bayero ya yi karatu kamar sauran yaran al'umma da karatun Alkur'ani, inda daga nan aka kaishi Makarantar Firamare ta Kwana dake garin Rano a shekarar 1963, shekarar da mahaifinsa ya zama Sarki, sannan ya kammala a shekarar 1969 inda daga nan ya wuce Kwalejin Rumfa, inda nan mai Martaba Sarkin Kano Alh. Ado Bayero ya yi lokacin tana Middle School, inda ya kammala a shekarar 1973 inda daga nan ya wuce zuwa Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Birnin Kudu inda ya samu shahadar kammala karatun Sakandire a shekarar 1975.

Bayan da Sunusi ya kammala karatun Sakandire ne ya nuna sha'awar koyon harshen Faransanci inda ya yi Diploma akan harshen Faranshi ya kuma kammala da sakamako mai daraja a kasar Faransa. Bayan ya dawo daga kasar Faransa ne ya shiga Kwalejin share fagen shiga jam'iah ta kano CAS, daga nan yayi babbar Diploma a sha'anin aikin Lauya a Institute of Administration dake Kwango a Zaria daga nan kuma ya samu shiga Jami'ar Ahmadu Bello Zaria inda ya yi digiri akan aikin Lauya ya kammala a shekarar 1983 ya kuma halarci makarantar horon lauyoyi ta kasa a 1984 yayi hidimar kasa a jihar Kaduna inda ya koyar a Kaduna Politechnic daga nan kuma ya yi ayyuka a matakai da dama har ya kai mukamin Director, kafin daga bisani a shekarar 1990 Mai Martaba Sarki ya nadashi Sarautar Dan Ruwatan Kano.

Daga nan Sunusi ya cigaba da aikinsa kuma yana rike da Sarautar gargajiya. Ya yi aiki a ma'aikatar Shari'ah ta Kano ya zama Legal Adbaiza a Kano Investment, daga nan likkafa ta cigaba ya kai har matsayin Famanan Sakatare a Ma'aikatar Yada Labarai ta jihar Kano tundaga 1996 har zuwa 2002. Ya kafa kamfanin aikin Lauya na Lamido & Co. Daga nan kuma ya samu sauye-sauyen Sarauta inda ya zama Tafidan Kano ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, daga bisani kuma ya zama Chiroman Kano Hakimin Gwale, sarautar da yake rike da ita har zuwa rasuwar Mai Martaba Sarki a ranar 06 ga watan shida 2014. 

08-06-2014

No comments:

Post a Comment