Tuesday, June 3, 2014

Matsalar Boko Haram!!!

BOKO HARAM: Da yawa daga cikin 'yan Arewa sun gamsu cewa matsalar Boko Haram ba zata zo karshe ba sai nan da 2015 idan dan Arewa "musulmi" ya zama shugaban kasa. Shi ya sa da dama suke ganin kyashin a tallafawa wannan gwamnati ta magance matsalar a rage salwantar rayuka da dukiyoyi, sun gwammace a yi ta kashe mutane daga nan har zuwa lokacin zabe, alabashshi idan namu ya samu sai a sake sabon lale. Maganganun mutane da yawa sun nuna haka. Bayan haka kuma, da karfi da yaji wasu suka ki yarda su fahimci gaskiyar wannan al'amari, ta yadda daga zarar mutum ya yi magana kan shawo matsalar sai a fara kallon waye shi dan wace jam'iyya ne, alhali kuma ga jama'a na ta rasa rayukansu dare da rana, kasuwanni na komawa kufai, yara na komawa marayu, mata na komawa zawarawa yanzu dai mu kalli yadda Jihar borno ta koma kamar Mogadishu!

Duk da maganar da Gwamnan jihar Borno Kashem Shettima ya yi na cewa wadannan 'yan Ta'addan na Boko Haram yaransu ne na Kanuri 'yan jihar Borno amma har yanzu wasu da suka yiwa lamarin nisa sun ki yarda su fahimci gaskiyar magana akan BH. Kwatsam kuma sai gashi dan majalsar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Bama, Ngala da Kalabalge Abdulrahman Terab ya sake tabbatar da cewar wadannan yaran da suke kai hare-haren nan babu ko tantama yaransu ne na jihar Borno! Wannan ita ce magana ta gaskiya, daga lokacin da muka tsaya cikin tsanaki muka fahimci gaskiyar al'amari dangane da BH to a lokacin muka sanya dambar magance matsalar, amma muddin aka cigaba da kauda kai a gareta ana alakanta laifin da wasu mutanen daban to zamu jima bamu fita daga cikin wannan matsaar ba, domin ba dan Arewa ba ko Sa Ahmadu Bello ne zai dawo ya zama Shugaban Kasa a 2015 haka nan matsalar zata cigaba da yaduwa, Allah ya kiyaye.

Allah ya sakawa Gen. Buhari da alheri, duk da kasancewarsa dan Adawa na wannan gwamnati amma ya yi bayani na gaskiya akan cewar dole a hada hannu da karfe a taimakawa Gwamnati wajen kawo karshen wannan matsalar ta BH a yankin Arewa maso gabas. Lallai gwamnati ita kadai ba zata iya kawo karshe wannan al'amari ba, har sai al'umma ta hadu gabaki daya wajen yakar lamarin, yau ko gwamnati ce ke da hannu a lamarin matukar al'umma sun tashi tsaye da gaske to sai sun kawo karshen abin.

Na fahimci wasu 'yan siyasa da dama musamman daga Arewa basa son wannan gwamnati ta shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ta kawo karshen lamarin dan suna ganin Gwamnatin zata samu wani credit da su basa bukatar ta samu saboda siyasa, a dan haka wasu ke kafar ungulu dan dakile samun nasarar yakar 'yan ta'addar, Allah shi ne masani. Amma lallai mu sani cewar, kullum kwanan duniya al'ummarmu ne suke rasa rayukansu a sanadiyar wannan rikici da aka sanya siyasa dumu-dumu a cikinsa.

A nata bangaren kuma, gwamnati ya kamata ta ji tsoron Allah ta bi hanyoyi na gaskiya wajen kawo karshen wannan al'amari. Allah ya kawo mana karshen wannan tashin hankali.

YASIR RAMADAN GWALE
03-06-2014

No comments:

Post a Comment