Sunday, February 2, 2014

Sheikh Auwal Adam Albani Zaria: Kullu Man Alaiha Faan!

SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI: KULLU MAN ALAIHA FAAN

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga gareshi muke, kuma gareshi zamu koma Subhanahu Wata'ala. 'Dazu da safenna dan uwa Malam Aminu Sani Musa ya kirani a waya yake yi min ta'aziya. Yasir ya hakuri? Ya tambayeni, hakika gaba na ya fadi, duk da na amsa masa da godiya tare da jiran bayanin dalilin ta'aziyar. Ya sanar da ni cewar wasu 'yan binduga 'yan ta'adda miyagu azzalumai fajirai fasikai zindikai tambadaddu sun kashe Malaminmu Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria! Hakika na ji kaduwa ainun da wannan bakin labari. Na yi masa addu'ar fatan samun rahama a wajen ubangiji.

Babu shakka, Sheikh Adam Albani ya rasu a tafarkin da muke fatan Allah ya dauki rayuwarmu akai. Wannan tafarki da muke kai, hakika an kashe Annabawa da Siddikai da salihan bayi, ba dan sun aikata wani laifi ba, sai dan sun bi tafarkin da Manzon Allah ya zo da shi. Wadan da suke yin wannan kisa, dangi da tsatso ne na wadan can miyagu azzalumai na farko da suke kashe mutanan kirki akan hanyar Allah. Wadan da suke yin wannan kisan, su sani cewa, barazanar kisa da tsoratarwa ba zai bata dusashe sautin gaskiya ba, sautin gaskiya sai ya daga yayi sama yana madaukaki, ko da kafurai da munafukai sun ki.

Ya 'yan uwa, yana da kyau mu tuna cewa, An kashe Sayyadina Umar Bin Khattab an kashe Usman Bin Affan an kashe Aliyu Abul Hasnain, an kashe manyan bayin Allah duk akan wannan tafarki. Irin  Wannan kisa da ake yiwa manyan bayin Allah wanda ya gangaro har kan Malamanmu na wannan zamanin, wani alkhairi ne wanda sai zababbu daga cikin bayin Allah suke tafiya ta wannan hanya. Kisan da aka yiwa Malam Adam Albani a daren jiya babu shakka ya tuna mana mutuwar Marigayi Sheikh Jaafar Adam, duk sun rasu akan wannan tafarki. Wadannan masu kisan ba zasu taba dainawa ba, domin mabiyan shaidan ne, dan Manzon Allah yayi ishara da hakan, a karshen zamani fadace-fadace da kisan babu gaira babu dalilai zai yawaita. Amma, su sani da sannu ajali zai riski kowannenmu ko mai daren dadewa, babu ko shakka akan cewa mutuwarmu ita ke yi mana gadin rayukanmu, lokacin da wa'adi ya yi, wayo da dabara ba zasu taba zama abin dogaro ba.

A saboda haka, yana da kyau mu sani, wannan kuma ba zai taba zama dalili na cewar mu zauna kara zube ana yi mana irin wannan kisan gillah ba. Ya zama dole mu tashi mu kawo karshen wannan al'amari, mu ne zamu baiwa Malamanmu kariya da garuruwanmu da dukiyoyinmu tare da taimakon Allah. Lallai ne dukkan hukumomin tsaron da abin ya shafa su tashi haikan wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, wajibin gwamnati ne ta Tarayya da ta Jiha su kare martaba da jinin al'ummar da suke shugabanta.

Muna tunawa, miyagu Azzalumai cewar, tunda Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya bar duniya, babu wani mahaluki da zai yi saura a raye. Kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa kamar yadda Sheikh Albani tuni ya dandana nasa, babu wanda zai rage face mai riska ta riske shi. Manyan 'yan Ta'adda na da can da na wannan zamanin sun dandana zafin mutuwa kuma suna ganin sakamakon abinda suka aikata. Ina suke da dama da suka kashe mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba? A ranar Badar da aka kashe Manyan kafurai sai da Manzon Allah SAW ya tsaya a bakin rijiyar da aka zuba gawarwakin Mushrikai ya tambayesu Ya Utbah Ibn Rabi'ah! Ya Shaiba Ibn Rabi'ah shin kun sami alkawarin Allah gaskiya ne! Haka nan suma wadan da suka biyo tafarkinsu zasu samu alkawarin Allah gaskiya ne.

Ina mai amfani da wannan dama wajen taya 'yan uwana dubban jama'a dake ciki da wajen Najeriya ta'aziya da Alhinin wannan gagarumin rashi da mukai, wanda irinsa ne karo na biyu da ya faru garemu ta irin wannan hanya a wannan lokacin. Allah ya jikan Sheikh Adam Albani Zariya da Iyalinsa da Dansa, Allah ka karbesu a matsayin Shahidai, Allah ka daukaka darajarsu. Allah ka jikan Musulmi da duk inda suke. Babu shakka duk inda aka samu babban rashi irin na Malamai dole zukata su kadu hankula su dugunzuma idanu su raurawa, amma mu tuna idan akwai wani rashi da zai dugunzumar da mu shin akwai rashin da ya kai na Manzon Allah SAW? Ya Allah ka kashemu akan wannan tafarki.

Yasir Ramadan Gwale 
02-02-2014

No comments:

Post a Comment