RE: BOKO HARAM: Matsalar Boko Haram, matsala ce mai sarkakiya. Da Farko sam ni ban gamsu da matakan da gwamnatoci ke dauka ba na dakile 'yan kungiyar a Jihohin Arewa ba. Domin yau Dan Talaka nawa zai iya shiga Jami'a har ya Kammalata? Dan Talaka nawa zai iya samun aikin Gwamnati ko na Kamfani koma ya iya samun Jari domin ya dogara da kansa? Idan na ga gwamnatoci sun horar da matasa, nakan yi dariya, domin mutumin da baida cikakken ilimi da gogewa da sanin yadda duniya ke sauya launi koda yaushe to yana da wahala ko an ba shi jari da horo ya kulla wani abin kirki.
Wannan yasa a daidai wurin da aka kammala horon, anan wadanda aka horas din ke sayar da kayayyakin aikin da aka ba su, su sai kwayoyi masu sanya maye. Idan mutum ya shiga Arewa maso Gabas, Yankin da ya fi kowane yanki ci baya a Najeriya zai sha mamaki. Babu wata tsiya da gwamnonin ke yiwa Talakawa a yankin sai karya da yaudara. Sai ko hotunansu da gumakansu da suka cika manyan biranen jihohi, da tallace tallace a gidajen Talabijin da Rediyo na ayyukan boge da suka aiwatar, ayyukan da na ha'inci ne da aringizo.
Yau takai 'yan Boko Haram za su shiga Makarantu su harbe Dalibai, su kwashi 'yan mata 'ya' yan musulmi su tafi da su cikin kungurmin dajin Sambisa su dirka masu cikin shege sannan su ce addini suke karewa. Shi ko Dan Arewa, ya takaita tunaninsa cewa Goodluck Jonathan ne ke ba da ummarnin hakan dan biyan bukatarsa. Mutane sun gaza gane cewa, Gwamnatin Tarayya bata isa ta shirya wani makirci mai girma irin wannan ba, domin a sama Musulmi nada wakilci, wanda da wahala a shirya makirci mai girma da zai ci gaba da tasiri kamar abin da ke faruwa ba. To amma zan iya yarda da cewa, wata kila a cikin Jami'an tsaro akwai baragurbi, kamar yadda a cikin gwamnatin ba za a rasa masu assasa wannan ta'asar ba.
Bishir Dauda Katsina
Kamar yadda Bishir ya fada, al'amarin Boko Haram akwai sarkakiya sosai a cikinsa. Zance na gaskiya kowa yasan abin da yake faruwa yafi karfin Boko Haram. Amma su sunce su ne, kuma hukuma ma tace su ne, kuma mu idan muka ce ba su bane babu wasu Dalilai masu karfi da zamu iya cewa ba su din bane, amma a zahiri mun san cewar wannan al'amarin yafi karfin mutanan da aka ce Almajirai ne suna kyamar karatun Boko amma suke sunkurun da aka kasa gane ko kama su. Kamar harin 10 Oktoba 2010 ne da aka kai Eagle Square a Abuja, MEND sunce su ne, amma shugaban kasa ya ce ba su bane, wanda ba shi da wani dalili da zai iya cewa ba su din bane tunda sunyi Ikirari da kansu tun ma kafin faruwar abin.
17-02-2014
No comments:
Post a Comment