Friday, February 14, 2014

Me Kae Yi A Afurka Ta Tsakiya Idan Ba ta'addanci Ba!


ME AKE YI A AFURKA TA TSAKIYA IDAN BA TA'ADDANCI BA!

Hakika irin abin da na gani ana nunawa na ta'addanci ban taba ganin irinsa ba a kasar Afurka ta tsakiya. A lokacin da na kalli wani Bidiyo na wani da ake kira MAD DOG yana cin naman mutum hankalina ya yi matukar tashi, abinda nake ji ana cewa wasu na cin naman mutum; sai gashi na gani. Abin ya bani tsoro sosai, babu shakka irin abinda ke faruwa a kasar ya zarce dukkan nau'in ta'addanci. Abin kuma yana faruwa akan idanun jami'an tsaron da aka jijjibge a kasar dan kawo zaman lafiya. Saboda kawai Musulmi ne ake kashewa, ana wawashe gidajensu, ana kone gidjensu tare da rugurguza masallatansu.

Abin mamaki lokacin da Kungiyar Saleka mai rinjayen Musulmi take fatattakar shugaba Bozizi mafi yawancin 'yan kasar sunyi murna da farinciki, duk kuwa da sanin cewar galibin 'yan kungiyar Musulmi ne. Bayan darewarsa shugabancin riko Michal Djotodia, su, 'yan kasar wai ba su dauka Musulmi bane, ana ganin yaje Masallacin juma'a shi kenan hankalin jama'a ya tashi, sai kuma 'yan Anti-balaka dake da makamai suka farwa Musulmi; sai tashin hankali; sai kashe-kashe; sai kone-kone da sace-sace.

A kasar Tchadi kasashen yankin suka tursasawa Shugaba Djotodia sauka daga shugabancin da samun zaman lafiya, da yake shima ba mai son tashin hankali bane ya bi ra'ayin 'yan kasar ya sauka, dan samar da zaman lafiya. 

Faransa ta bayar da soji 1600 tarayyar Afurka ta bada soji 4000 tarayyar Turai tayi alkawarin soji 1000 amma duk suna gani 'yan Jarida suna yada irin yadda ake kashe Musulmi sai dai kawai surutun da su Ban-ki Moon suke yi. Ina Amerika ko duriyarta baka ji tunda ta yi alkawarin taimakawa da kudi. 

Amma a Kwango da Sudan ta Kudu saboda kiristoci ke kashe junansu nan da nan ana lura da abinda ke zuwa yana komowa. Ana ta kokarin yadda za'a sasanta. Babu shakka Allah shi ne gatan Musulmi a duk inda suke, duk wasu masu ihu da ikirarin 'yancin dan adam makaryata ne, tunda gashi nan ba wai danne hakkin Musulmi aka yi ba, namansu danye ake ci duniya tana gani. Amma Allah baya gyangyadi bare bacci, daman kuma ya fada a cikin Sura ta 29 aya ta 2 cewa tsammaninku dan kunyi imani ba zamu jarrabeku ba! Hakika an jarrabi Musulmin Afurka ta tsakiya. Muna rokon Allah ya kai musu mafita da Dauki ta inda basu zata ba.

YASIR RAMADAN GWALE 
14-02-2014

No comments:

Post a Comment