Wednesday, February 19, 2014

Idan An Doki Jaki, A Doki Mangala


IDAN AN DOKI JAKI, A DOKI MANGALA

Idan mun doki Jaki mu bugi Mangala. Mukan zargi Shugabannin Arewa sau da dama akan halin da muke ciki, amma, mu kan kyale Shugabanni wadan da muka zaba da hannunmu wajen tafiyar da al'amuranmu da jagorantarmu. Muna yawan kalubalantar Shugabannin da su ne suka nada kansu ba mu ne muka zabe su ba. Duk wanda ya sha inuwar gemu ai bai kai ya makogaro ba, Shugabannin da muka zaba kuma suke karbar Dirkeken Albashi da sunan Shugabanninmu su ne a hakku da zamu tuhuma akan dukkan wasu al'amura da suke same mu.

Muna da Gwamnonin da muka zaba, muna da 'yan Majalisar dattijai da na wakilai wadannan duk mun zabesu da kuri'unmu, kuma ana biyansu albashi mai tsoka akan zaben da muka yi musu. Lallai su ya kamata mu mayar da karfin tuhumarmu akansu, ba wai wadan da su Ikirari kawai suke cewa su ne shugabannin Arewa ba, wadan da ba suda Dansanda ko Soja ba suda Babban Bankin Kasa ba su da ikon yin abinda suka ga dama.

Lallai muna cikin wani hali, da yakamata mu turke Shugabanninmu wadan da muka zaba, akan su yi mana bayanin meya sa muke cikin halin da muke ciki, amma suka kasa daukan matakin kawo karshen al'amuran da suke faruwa na sukurkucewar tsaro da salwantar rayuka babu gaira babu dalili.

Maganar da Gwamnan Borno Kashim Shettima ya yi cewa idan akwai kayan aiki a wajen jami'an tsaro, za'a fatattaki masu tayar da Hankalin nan a cikin kwana 30! Wannan babbar magana ce, amma har yanzu mun tsuke tunaninmu cewar CAN ce ke mana wannan aikin, mun zuba ido muna jiran Kaddarar Ubangiji. Dole mu farka mu san abinda muke yi, mu kuma san su waye ya kamata mu kalubalanta dangane da halin da muke ciki.

Yasir Ramadan Gwale 
19-02-2014

No comments:

Post a Comment