YOBE: Labarin da muka samu a yau, na cewa, an kuma zuwa makarantar kwanan dalibai 'yan sakandare a jihar Yobe an kashe su, abin ya matukar tayar mana da hankali. Har yanzu babu wani rahoton bincike da muka ji ko muka gani akan kisan da aka yi a Oktoban bara na dalibai sama da 50 da aka kashe a garin Mamudo a yoben, sai kuma ga wannan a sakandaren Gwamnatin Tarayya. Ba shakka Tura ta kai bango, angama kuremu, ba zai yuwu kullum ana yin haka ba, abin yana tafiya babu wani daukar mataki daga jiha ko tarayya al'amura suna wuce babu wani mataki na zahiri da ake dauka dan kawo karshen wadannan hare-hare na babu gaira babu dalili ba, muna murna da farin ciki zaman lafiya ya dawo a Yobe ashe da sauran rina a kaba.
Wane irin hali, iyaye zasu shiga a kawo musu labarin cewar wasu 'yan Bindiga sun je cikin dare sun kashe musu yara, an yiwa wasu yankan rago wasu an kona su da ransu! Subhanallah, Ina wadan da alhakinsu ne kula da wannan amanar ta yaran? Ina Hukuma? Lallai wannan al'amari ya kamata indai da gaske yinsa ake yi ya zo karshe. Kuma wajibin hukumomi ne su biya diyyar rayukan da aka rasa wannan Negligence ne na hukuma.
Shugabanni suji tsoron Allah, kullum rayuka na salwanta babu wani mataki da ake bi na bin kadu, jinin al'umma ya zama ba shi da wata kima, wallahi Allah ba zai kyale wannan al'amari ba. Dole a dauki mataki na karshe dan sanya aminci da nutsuwa a zukatan al'ummar da ake shugabanta.
Su kuma, masu aikata wannan ta'addanci, su sani Allah da gaske akwai shi, batun cewa yana nan yana jiran kowa a madakata, gaskiya ne ba tatsuniya bace. Babu wani mahaluki da zai yi saura a duniya face mai riska ta riskeshi, ya yarda ko bai yarda ba, ya shirya ko bai shirya ba. Kowa kuma zaiga sakamakon abinda ya aikata. Wanda ya aikata alkhairi zaiga alheri, wanda ya yi sharri ya kashe mutane ya mayar da yara marayu, ya raba mata da mazajensu ya raba tsakanin dangi, wallahi Azabar Allah na nan na jiransu.
Lokacin da Sahabbai suka shiga cikin tsanani sun tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam cewa YAUSHE NE NASARAR ALLAH ZATA ZO? Manzon Allah ya kwantar musu da hankali cewa Nasara na nan gaba garesu. Lallai mu sani nasarar Allah a kusa take, Allah da muke kira yana jinmu dan ba kurma bane ba makaho bane, yana ji yana ganin abinda ake yi mana. Ya Allah bamu yanke tsammani daga gareka ba, Ya Allah ka Amintar da mu a gariruwanmu, Allah ka jikan wadannan Dalibai ka yafe musu. Wadan da suka aikata musu wannan ta'addanci Allah ka dandana musu azaba sama da wadda suka yi idan sun kasance kangararru ba masu shiryuwa ba.
25-02-2014
No comments:
Post a Comment