Wednesday, February 26, 2014

Shin Wa Ye Zai Yiwa Shugaban Kasa Wa'azi?


SHIN WA YE ZAI YIWA SHUGABAN KASA WA'AZI?

Na tambayi kaina, cewa, anya kuwa an taba yiwa Shugaban kasa Wa'azi, ya ji zancen Allah? Lallai Annabi Ibrahim Alaihis-Salam da kansa ya je ya yiwa Nimrud (Lamarudu) Wa'azi ya gaya masa zancen Ubangiji; Annabi Musa Alaihis-Salam ya yiwa Fir'auna Wa'azi ya gaya masa sakon Allah; Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam da kansa ya dinga bin Mushrikai yana yi musu wa'azi yana gaya musu sakon Ubangiji, da dama suka ji zancen Allah kuma suka yi Imani; Shekhu Usmanu Bin Fodiyo ya dinga bin fadar Sarakunan Arewa yana yi musu wa'azi yana gaya musu sakon Ubangiji, Allah kuma ya sanya da dama suka karbi wannan kira da Shehu Umsanu ya yi musu, suka yi Imani da Allah da ManzonSa SAW, shi ya sa har duniya ta tashi ba za'a daina ambaton Shehu Usmanu ba a kasarnan.

Lokacin da naga sanarwa cewar, Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ne babban bako a wajen Wa'azin Izala da za'a yi a Legas, na ji dadi kwarai, domin nasan za'a gayawa Shugaban kasa Sakon Ubangiji, kuma za'a karanta masa Al-Qur'ani ya saurara. Amma daga baya Murna ta ta koma ciki, kasancewar Shugaban bai samu halartar Wa'azin ba, saboda wasu Uzurori da aka ce sun hana shi zuwa. Ina kuma fatan nan gaba Kungiyar Izala zasu sake gayyatar Shugaban Kasa wajen Wa'azi su gaya masa sakon Ubangiji. Na taba jin cewar Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya taba zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna da kansa ya yiwa tsohon Gwamna Patrick Yakowa wa'azi ya karanta masa Al-Qur'ani ya saurara, ya isar masa da sakon Ubangiji, ance Yakowa yaji dadin wa'azin yayi godiya ga Sheikh Gumi, domin yace shi ne karon farko da aka taba zuwa aka yi masa wa'azi, aka karanta masa Al-Qur'ani, duk da cewa Allah bai nufi Yakowa da yin Imani da Allah da Manzon Allah ba.

Lallai, muna bukatar a samu wasu malamai masu tsoron Allah, su je har fadar Shugaban kasa su yi masa wa'azi su gaya masa sakon Ubangiji su karanta masa Al-Qur'ani, su gaya masa Allah mai Rahama ne da Jinkai ga Talikai, kuma Mai tsananin Azaba ne ga wadan da suka kangare suka ki yin Imani alhali sakonSa ya je garesu. Lallai, muna fatan samun irin wadannan Malamai, kamar yadda na taba jin cewa Sheikh Muhammad Ibn Uthman ya taba zuwa har Gidan Gwamnati a Umuahia ya yiwa tsohon Gwmnan Jihar Orji Orzu Kalu Wa'azi ya gaya masa sakon Allah, kuma Gwamnan shima ya yi Murna da jin dadin wa'azin, wannan ce ma ta sanya ya zo har Kano lokacin wata karamar Sallah aka yi Bikin Sallah tare da shi har ya halarci Kallon hawan Daba, muna fatan Allah ya buda Kirjinsa ya karbi sakon Ubangiji.

Yana da kyau Malamai su dinga zuwa wajen Masu Mulki suna yi musu wa'azi suna gaya musu sakon Ubangiji, kamar yadda Annabawan Allah suka yi. Turawa suka dinga ratsa Teku suna keta Dazuka suna yawon yada Addinin Kiristanci, Shin irin wadan can Turawan sun fimu son Shiga Al-Jannah ne? Lallai mu ne a Hakku da shiga Al-Jannah ba su ba, munyi Imani da cewar duk wanda ya yi Imani da Allah da Manzon Allah SAW kuma ya mutu akan haka, zai samu rahamar Allah. Ya ALLLAH ka shiryi Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan ka sanya haske na Imani a zuciyarsa. Allah ka sa ya fahimci irin hakkin da yake kansa na kare rayukan al'ummar Najeriya. Allah ka shirya Shugabanninmu Gaba daya, ka azurtamu da Shugabanni na gari Adalai.

YASIR RAMADAN GWALE 
26-02-2014

No comments:

Post a Comment