NAKA SHI KE BADA KAI!!!
Naka sai naka, a wani azancin zance da Bahaushe kan yi. Babu shakka abinda Bahaushe ya ce da arziki a garin wasu gara a naku, wannan ya kusa kama da daidai, amma abin fata shi ne a tara arzikin na halal a kuma kashe ta halal. Sau da dama mu 'yan Arewa ko kudu mukan so namu ya samu wani babban mukami a gwamnatin Tarayya tundaga sha'anin Mulki da Tsaro da harkar tattalin arziki da sauransu, ta haka ne kadai muke zaton indararon arziki na iya kwaranyowa zuwa garemu ko ga wasunmu. Ba komai ya sanya da dama yin wannan tunani ko fata ba, face RASHIN ADALCI da ya game ko ina, kasancewar Adalci ya yi karanci a sha'anin tafiyar da mulki, ya sanya yanzu a Najeriya kowa nasa yake fatan ya samu tsakanin Kudu da Arewa ko tsakanin Musulmi da Kirista.
Mun wayi gari, a wani irin mawuyacin lokaci, inda Musulmi basa yin Adalcin da ya kamata akan kansu balle ga wanda ba Musulmi ba, kiristoci basa yin adalci ga Musulmi; haka kuma, 'yan Kudu basa yin Adalci ga 'yan Arewa, suma 'yan Arewan basa yin abinda ya dace ga 'yan kudu. Bisa irin wannan dalili ne ya sanya da dama muke hannu baka hannu kwarya wajen kankane dukkan wasu Madafun iko tsakanin Kudu da Arewa ko tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya. Sau da dama, jama'a, basu cika son ayi adalci a zamantakewa ba, illa a dadada musu ko da za'a cutar da abokin zamansu, babu abinda ya damesu.
A mafi yawancin lokuta, mu 'yan Arewa mukan yi addu'ah da fatan inama ace namu ne ya samu, wasu na yin fatan haka ne dan suna zaton alal akalla zasu samu damar cin moriyar wani arziki wanda nasu yake da ikon tasarrufin akansa. Misali akan hakan, shi ne munyi fatan ace namu ne suka samu Manyan mukamai da suka shafi bangaren harkar Tsaro, dan fatan watakila zamu iya fita daga cikin halin da muke ciki, musamman a yankin Arewa maso Gabas, saboda munyi Imani wadan da suke rike da mukamin a yanzu suna ko in kula da aikinsu, saboda ba al'ummarsu ce ke shiga cikin garari ba, wani abin mamaki akan haka shi ne, bayan rikita rikitar tsaro da ta addabi Arewa maso Gabas, shi ne kuma, wani abin mamaki da ban takaici da kusan ya fi yin kamari a jihar Zamfara sama da kowace jiha, ba komai bane face satar shanu da kashe mutane masu yawan gaske a lokaci guda da kuma ribace mata da kananan yara, da sunan cewa 'yan fashi ne suka aikata.
Wannan abin ya faru a jihar Zamafara ba karo daya ba, ba kuma karo biyu ba. Abin mamaki shi ne shugaban 'Yan Sandan Najeriya gaba daya dan Asalin jihar Zamfara ne, amma duk abinda yake faruwa na daure kai a mahaifarsa yake ta faruwa. Zai zama abin mamaki kwarai da gaske ace 'yan fashi su shiga kauye su kashe mutane 50 ko fiye, su kore shanu wajen dubu goma, amma a kasa ganin koda kurar inda suka shiga balle a kama su! Babu shakka wannan abu ne wanda hankali ba zai dauka ba, babu yadda za'a yi irin wannan shegantakar da sunan fashi da makami amma ace an kasa sanin inda barayin suka shiga da shanun, balle kuma a kama barayin a hukuntasu. Dan Allah wace rana Sufetan 'yan sanda ya yiwa Mahaifarsa a wannan batu?
Irin wannan misalin abin haushin yana da yawa ainun a Arewa. Sau da dama mutanan da muke ganin zasu kare mana martabarmu da mutuncinmu sukan bada mu, ta hanyar yin shakaulatun bangaro da batunmu, babu ruwansu da kulawa da bukatun mutanan da kullum suke yi musu fatan samun wani mukami wanda zasu taimaki al'ummarsu da addininsu da habaka tattalin arzikinsu, tunda yanayin kasar ya nuna cewa babu wani wanda zai iya kare maka mutuncinka da muradunka face sai wanda yake da iko ya kasance naka ne. Duk da haka ba mu yi kasa a guiwa ba, kuma bamu yanke tsammani ba, cewa 'yan Arewa zasu taimakawa yankin Arewa wajen farfadowa nan kusa ko nan gaba. Bama kira ko fatan a dauki hakkin wani a bamu, fatanmu shi ne a yiwa kowane dan kasa Adalci, dan wani wanda baya cikinmu ya samu iko akanmu ya zalunce mu, wannan ba shi ne dalilin da zai bamu damar zalintar wadan da ba mu ba, idan mun sami iko akansu.
Yasir Ramadan Gwale
29-01-2014

No comments:
Post a Comment