Wednesday, October 9, 2013

Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?


Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?

Najeriya ita ce kasa ta biyu a duk fadin nahiyar Afurka da ta yi fice wajen samar da irin tumatur mai kyau. Allah ya bamu albarkar kasar noma da tana iya dacewa da yanayin kowanne irin abin shukawa tun daga 'ya 'yan itace da dangin hatsi da kayan lambu da sauransu. A baya can Najeriya na samar da tumatur wajen tan miliyan 1.14 duk da cewa binciken masana ya nuna cewa Najeriya zata iya samar da fiye da tan Miliyan biyar na tumatur a kowacce shekara, wanda zai iya wadatar da Afurka da wasu kasashen gabas ta tsakiya. Amma kusan yanzu kullum harkar noman tumatur armashin ta raguwa yake yi, kasantuwar babu wasu masana'antu a Arewa da suke sarrafa danyan tumatur dan a zuba shi a cikin gwangwanaye da lodoji da saurin mazubai dan amfanin yau da kullum na harkar girke-girke. Kasantuwar duk kasarnan a Arewa ne aka fi yin amfani da tumatur a sha'anin girke-girke.

Da yawan manoman tumatur da masu kasuwancinsa na yin harkar ne cikin tararrabi da fargabar samun riba ko faduwa kasa warwas. A lokacin da ake tsaka da kakar tumatur a jihohin Arewa zaka ga yadda manoma ke yin roronsa kwando-kwando kai ka ce gaba daya Arewa Tumatur kadai ake nomawa, amma mafiya yawancin Manoman tumatur sun dogara ga kudancin Najeriya ne domin yin kasuwancinsa, mota-mota ake yi  ana daukar tumatur daga Arewa zuwa kudancin Najeriya. Wani abin mamaki shi ne, akwai lokacin da a Arewa zaka nemi jan tumatur sama da kasa ka rasa, gaba ki daya babu shi, kodai sabo bai karaso ba, wanda aka noma a baya kuma tuni aka yi kasashen kudu da shi.

Wadan da harkar tumatur ta yi musu kyau su ne wadan da suka yi sa'ar kai shi kudancin Najeriya ba tare da ya lalace ba. Domin duk mutumin da ya yi rashin sa'ar yin lodin tumatur a dai-dai lokacin da aka samu budewar rana kwal, to sai dai wani ba shi ba, domin kafin a isa ga inda aka nufata tumaturin ya narke ya tsiyaye, da yawan manoman tumatur sun sha tafka asara ta irin wannan hanya, wasu manoman da dama sun zautu wasu ma sun haukace saboda asarar da suka yi ta irin wannan hanyar. Haka kuma, ansha samun sabani ga direbobin daukar tumatur din da manomansa musamman wadan da suka yi rashin sa'a, wasu su loda tumatur din ganin asarar da suka yi su gudu su bar direba da jogoguwa, shi kudinsa bai fito ba, ga kuma dole sai ya nemi inda zai zubar da ragowar rubagen a can kudancin Najeriya.

A baya a Arewa muna da kamfanonin tumatur a IKARA da KURA da kuma DADIN-KOWA amma yanzu duk sun zama kangwaye. Masana'antun sun mutu murus, dan haka dole manoma su nemawa tumatur din da suke nomawa kasuwa a yankin kudancin kasarnan, abin mamaki kasar kudu da basa iya samar da ko da koren tumatur, sune yanzu haka suke da kamfanonuwan tumatur din da galibi ake yin girki da shi a Arewa, Jihohin Legas da Ibadan sune kadai inda suke da kamfanonin sarrafa tumatur, suma basu dogara da kasuwancin da suke daga Arewa ba, domin bayanai sun nuna cewar Najeriya na shigo da markadadden Tumatur din da ba'a sarrafa ba daga Chana na kimanin Naira Biliyan 12 a kowacce shekara. Wanda masana harkar lafiya suka tabbatar da cewa babu wani sahihanci na ingancin nikakken tumatur din da ake shigo da shi Najeriya a cikin dururrukan da suka jima suna galudaya akan ruwa.

Yanzu da masu kudinmu da gwamnatocinmu zasu taimakawa Manoman tumatur da tayar da kamfanonin Kura da Ikara da suka mutu da alal akalla, za'a samarwa da dubban matasa aikin yi. Duk da cewar rahotanni sun tabbatar da cewar Alhaji Aliko Dangote yana yunkurin samar da katafaren kamfanin sarrafa Tumatur a garin Kura, wannn yunkuri idan har yaci nasara hakika babban cigaba ne, kuma wannan zai sanya da yawan manoman tumatur da suka watsar da harkar su koma mata, da kuma samar da karin sabbin manoman tumatur.

Amma saboda rashin kamfanonin da suke sarrafa tumatur din a Arewa, haka nan miliyoyin tumatur suke halaka bayan ankai wasu kudancin kasarnan anyi kasuwancinsu cikin kasada, wasu kuma haka nan manoman kan yayyanka su suke shanyawa akan tituna da rufin gidaje. Allah ya nuna mana lokacin da za'a samar da sabbin kamfanonin sarrafa tumatur da kuma tayar da komadar wadan da suka kwanta dama.

Yasir Ramadan Gwale
09-10-2013

No comments:

Post a Comment