NAMAN SALLAH: Mugunta Ce Ko Keta?
|
Naman Sallah |
NAMAN SALLAH: MUGUNTA CE KO KETA?
Sau da dama na kan yi mamaki irin yadda muke ta kiran addini a baki!
Bayan addini ya nuna mana 'yan uwantaka da zumunci da taimakekeniya da
kaunar juna da kusanto da juna kusa. A Mafiya yawancin maganganunmu da
suka shafi addini sun fi yawa a bakunanmu, musamman abubuwan da muke
ganin an zalunce mu, abubuwan da mu ya kamata mu aiwatar, mu nuna
kyakkyawar koyarwar addini bamu cika kulawa ba, mun fi kauri wajen cewa
Shugabanni suna zaluntarmu, bama ganin abubuwan da muke tsakanin
junanmu na cin dunduniya, da gulma da munafurci da kyashi da kyeta a
matsayin wani laifi, muna take laifin da muke aikatawa junanmu muna
hango wanda ake aikata mana.
Abin mamaki ne kwarai da gaske a
ce mutane sun soya naman SALLAH suna ta ci suna gudawa, cikinsu yana
murdawa, amma makotansu da dama basu da naman da za su ci. Malam Saluhu
wani Ladani ne wani lokaci ya gayamin cewar wallahi Haka aka yi Sallah
aka gama ko kanshin nama bai ji ba, dan
kawai kasancewarsa ba shi da iyaye a inda yake, babu kuma wanda ya damu
ya kawo masa nama ya dan lasa. Sai na kasa gane wai mugunta ce ko kyeta
ce ta ke sanyamu mu ajiye nama mu kadai da Iyalanmu muna ci muna ta
tsuga zawayi, amma haka nan muke ta afawa a cikkunanmu.
Alhamdulillah, wasu jama'a da dama sukan yi yanka su rabawa jama'a nama,
amma galibi abin da suke ajiyewa a gidajensu suna ci su kadai da
iyalansu ya yi yawa matuqa. Ya 'yan uwa masu girma, lallai sai mun
nunawa junanmu soyayya da kauna ta hanyar nuna kyakykyawar mu'amala da
taimakekeniya, irin dan naman da muke kakkasawa a faranti muke rabawa,
bayan mun ciccika kwallaye da soyayyan nama, ya yi kadan. Wani bawan
Allah ya shaidamin cewa yana yanka Saniya da raguna biyu, amma nama a
gidansa baya wuce mako guda ya kare, saboda rabarwa da Iyalinsa take yi,
tun yana nuna damuwa har ya fahimci cewa lallai abinda iyalin nasa ta
ke yi shi ne abinda ya kamata a ce mata suna yi. Allah ya shiryemu
shirin addini.
Daga karshe ina tunasar da mu kabbarori ALLAHU
AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILA HA ILALLAH, ALLAHU AKBAR,
ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WALILLAHIL HAMD.
YASIR RAMADAN GWALE
16-10-13
Malam Allah saka ma da alkhairi
ReplyDelete