MECECE MAFITAR HALIN DA AREWA TA KE CIKI?
Batun halin da Arewa ta ke ciki na zubewar mutunci
da kima da haiba da kamala da koma baya ta fannin tattalin arziki da
sukurkucewar Ilimi da lalacewar makarantu da kiwon lafiyar da asibitai suka
zama tamkar makabartu da al’amuran tsaro da suka jagwalgwale suka hana kowa
walwala da jin dadi, kusa wadannan da ma wasu sun damu duk wani dan AREWA mai
kishi babba ne ko karami, mace ce ko Namiji. Yau a Arewa babu wani wanda zaka
titsiye ka tambayeshi halin da ake ciki ya yi maka hamdala da godiya da wannan
hali da muke ciki, sai dai fa idan tantagaryar makiyin Arewa ne makiyin
Najeriya wanda baya son cigaban Arewa da Najeriya. Halin da muke cikin ya wuce
duk yadda ake zato, domin wani abin ma idan mutum yaji sai yaji kamar ba
gaskiya bane, ba wai kawai lalacewa Arewa ta yi ba, a’a komawa baya take a
sukwane, Kamar Misalin motace ka baiwa dan koyo kuma ya sanya giyar reverse
yana gudun tsiya, shakka babu dole ya yi barna, ba wai motar kadai zai
mammokada ya lallauya tayoyin ba har da
duk abinda ya samu akan hanya sai ya bangajeshi mai gyaruwa ya gyaru wanda ya
mutu ya mutu kenan; to kamar misalin irin haka Arewa take a yanzu, a halin da
muke ciki.
Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta addabi
samarinmu maza da mata, Ilimin makarantun hukuma ya tabarbare makarantun
gwamnati sun zama garken jahilai, malaman babu ilimi, daliban babu ilimi
gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da sauran al’umma da ake kira
“community” a turance kowa ya kame hannunsa daga lalacewar ilimi anyi ko
in’kula, kowa ya gwammace idan zai iya ya dauki dansa ya kaishi makarantar
kudi, wanda kuma bashi da karfi alal-larurati ‘ya ‘yansa suke karatu a
makarantun gwamnati ba dan ransa yana so ba, sai dan bashi da yadda zai yi.
Irin wannan mawuyacin halin hannu baka hannu kwarya, ya sanya da dama
dagacikinmu suka fara yanke tsammani daga Ubangiji, wasu suka bazama neman yaki
halal yaki haram, Mutane burinsu su tara
dukiya babu ruwansu da tsarkinta.
Yanzu a Arewa yaro da babba, mace da Namiji, almajiri
da wanda ba al’majiri ba, mai gata da mara gata, mai mulki da wanda ake mulka;
Kusan kowa neman damar dan uwansa yake, ta ina zai samu dama ya kwashe
kafufuwan duk wanda Allah ya dorawa kaddarar fitar rabo. Cuta da cutarwa ta
zama ruwan dare gama duniya, babu malamai babu jahili, masu hankali da marasa
hankali kowa neman hanyar cuta yake, yan kasuwa da masu sari, leburori da
iyayan gidansu; daman ma’aikatan gwamnati ya zamar musu tamkar halaliya yin
almundahana da kayan hukuma, a sace duk abinda zai iya satuwa, tundaga masu
gadi har oga kwata-kwata duk wanda ya samu abin dauka indai na hukuma ne, to
gaban kansa yake ya dauka, tamkar wanda ubansa ya mutu ya bar masa gado shi
kadai, a sace man jannareto, a sace fanka a saci tabarma da darduma, wani abinma
bai kai a sace shi ba, amma saboda tsabar mutuwar zuciya, sai ma’aikata su
dinga satar abinda ko kadan ba zai amfanesu ba, illa kawai wani tunani da ya
dade da yin tsiro a zukatan al’umma na cewa “raba arne da makami ibada ne” dan
haka ake ganin kayan hukuma kamar ganima.
Wannan yanayin shi ne wani irin mawuyacin lokaci da
Arewa bata taba mafarkin samun kanta a cikin irinsa ba. Magabatan shugabanninmu
sun barmana kyakkyawan abin gado, sun gina harsashin samun ingantacciyar
rayuwar wadan da zasu zo baya, sun samar mana da Gidan jaridar NNN da gidan
Radio Najeriya Kaduna, da kamfanonin murza auduga na Arewa da Babban Bankin
Arewa da makarantun tundaga kwalejoji da jami’o’I da makarantun koyon sana’a,
da makarantun horas da malamai da sauransu da dama, amma basu yi sa’ar samun
hannu na gari da zai iya alkinta su ba, wannan duk wanda ya san Arewa ya san
halin da ta ke ciki zai iya bayar da shaida akan haka. To amma hakikanin
gaskiya tafiya tayi tafiya, tura ta kai bango, lokaci ya yi da za’a zauna zama
na gaskiya a kalli halin da muke ciki dan dawo da martabarmu da aka yi mana
shaida da ita tun a baya.
Haka kuma, lokaci ya yi da zamu ja layi akan dukkan
wasu laifuka da muke ta zargin kawukanmu da aikatawa, tunda halin da muke ciki
ya shafi kowa da kowa, babu wanda yake walwal cikin jin dadi da kwanciyar
hankali, kusakurai an riga anyisu manya da kanana, dan haka, abinda ya kamata
mu maida hnaklai shi ne kokarin nemo mafita da bakin zaren halin da muke ciki.
Shugabannin baya da kuma wadan da suka nannada kansu Shugabancin Arewa a yanzu
duk sunyi abinda zasu iya, wadan da suka tafka ta’adi da wadan da suka yi abin
kirki duk sunyi, kuma anga abin da kowa ya yi, Allah ya sakawa kowa da
gwargwadon abin day a aikata, idan khairan khairn, idan sharran sharran.
Wata rana Shehu Jaha ya aiki diyarsa ta debo masa
ruwa a tulu, sai ya yi mata kashedin kada ta sake ta fasa masa tulu, idan kuwa
ta fasa to zasu gauraya, har ta kama hanya ta tafi sai Shehu ya kirata ya
tsinko tsumagiya ya shashshauda mata, wani abokinsa ya ce haba Shehu yaya ka
gargadeta kar ta fasa, bayan kuma bata fasa ba ka doketa. Sai Sheshu ya kada
baki yace, babu amfanin na doketa a lokacin da ta riga ta fasa tulu, domin dukan ba zai sanya
tulu ya dawo ba. Kamar misalin haka ne na irin halin da muke ciki, yawan zargin
junanmu da laifin halin da muke ciki babu abinda zai kara, illa kara wagegen
gibi a tsakaninmu, tunda matsaloli dai ana cikinsu tsamo-tsamo, batun ko laifin
su wane ne ko ba laifin su wane bane, duk ya kamata mu wuce wajen, batun da ya
kamata mu maida hankali shi ne ta yaya zamu fito daga cikin wannan halin da
muke ciki shi ne abinda dukkanmu ya kamata mu maida hankali akai.
Dukkanmu dole mu ji tsoron Allah a cikin
al’amuranmu, mu sanya gaskiya da amana a cikin mu’amalolinmu, shugabanni su
zama adalai a ajiye komai a inda ya dace, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa,
babu wasu mutane daga Ingila ko Faransa ko Amerika da za su zo su fitar dam u
daga cikin halin da muke ciki, mune muka san kanmu, muka san halin da muke
ciki, muka san irin azaba da radadin da muka shiga ciki, ya zama tilar mu hada
karfi da karfe wajen fito da sahihan hanyoyi da zasu amfani ‘yan bayanmu masu
zuwa nan gaba. Mu shata layi kamar yadda na fada, ko da bamu yafe irin satar da
‘yan uwanmu suka dibga ba, to mu dakatar da abin haka, kudin hukuma ba na uban
kowa bane, na dukkanmu ne, idan mun alkinta dukiyarmu kanmu muka alknta, idan
mun barnatar kanmu da jikokinmu muka yiwa illa.
Ya zama dole da Masu mulkinmu na Siyasa wadan da
hakkin jagorancinmu yake a hannunsu, da shugabanni masu rike da sarautu, da
malamai da kungiyoyi mu samar da wata Hadaka da zata fitar da mu daga cikin
halin da muke ciki. Kamar yadda aka samu hadewar jam’iyyu dan kawai ga gaci da
samun nasara, muma dole sai mun hade kanmu mun hade kungiyoyinmu, sannan mu
samu nasarar fita daga cikin wannan mawuyacin halin da muke ciki. Akasin haka,
babu abinda zai yi mana illa kara jefa mu cikin bakin ciki da damuwa da ba za
su iya yi mana maganin halin da muke ciki ba, idan banda kara nesanta mud a
juna. Dole mu dawo da ‘yan uwantaka tsakaninmu da kaunar juna, da
taimakekeniya, mu cire kyashi, mu daina hassada, mu yiwa kanmu tarbiyyar hakuri
da halin ‘yan uwanmu, mu kuma yi hakuri da halin talauci da kuma baiwa
mawadatanmu uzuri. Ya Allah ka karkato da hankulanmu gaba daya mu fahimci juna
dan ciyar da Arewa da Addininmu gaba, Allah ka taimakemu ba dan halinmu ba, ba
dan munanan ayyukan da wasu daga cikinmu suka aikata ba. Allah ka taimakemu ka
sa wannan shi ne lokacin da zamu yi ban-kwana da dukkan irin sarkakiyar da muke
ciki da wahalar rayuwa. Allah ya taimaki Arewa da Najeriya baki daya.
Yasir Ramadan Gwale
13-10-13
No comments:
Post a Comment