LOKACI: A cikin dukkan rayuwar halittar
Ubangiji, babu wani abu da Allah SWT ya halitta wanda yake tafiya baya
tsayawa sai lokaci. Hakika Lokaci shi ne abinda yafi komai muhimmanci a
cikin dukkan rayuwar Bani-Adama. A saboda irin Muhimmanci
na lokaci Allah ya buga misalai da dama da lokaci a cikin littafinsa
mai tsarki (QURAN) Haka kuma, a cikin sura ta 103 Allah SWT da kansa ya
yi rantsuwa da lokaci. Wannan kadai ya isa ya nuna mana Muhimmancin
lokaci, da yawan mutane da zasu riski sa'ar karshe a rayuwarsa a tambayi
me suke so a gidan duniya, babu Shakka karin lokaci za su nema.
Sahabbai sun kasance suna yiwa Manzon Allah SAW tambaya game da lokaci
(ALKIYAMA) Allah SWT da kansa ya barwa kansa sanin wannan lokacin.
Hakika, lokaci yana da matuqar Muhimmancin da ya kamata a bashi kowacce
irin kulawa, amma a bayyane ta ke cewar Lokaci bai yi sa'ar iyayan gida
ba, sai dai kadan daga cikinmu da suke girmamashi. An haifemu a cikin
lokaci, zamu mutu a cikin lokaci, Tabbas LOKACI shi ne abinda zai ga
bayan dukkan Bani-Adama gaba dayansu na farkonsu da na karshensu, babu
wani mahaluki da zai iya tsayar da lokaci. MU GIRMAMA LOKACI, MU MUTUNTA
LOKACI, MU ALKINTA LOKACI. Lallai mu sani Lokaci baya jiran kowa, domin
shi matafiyi ne.
Yasir Ramadan Gwale
17-10-13
No comments:
Post a Comment