OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN
MULKIN JANAIRUN 1966.
Fitar da Mujallar ’Kunnen Gari’ bayan dogon nazari da
wasu fitattu kuma ‘yan kishin kasa suka yi dan isar da abin da ya dace na ilimi
kan yadda lamurran siyasa da zaman takewa ke gudana a Najeriya ganin yadda kafofin wayar da kai suka gaza
aikin su ko suka bata aikin musamman a Arewa ya sanya fitar wannan Mujallar dan
ta Ilmantar ta kuma zaburar da mutane. Allah ya albarkaci Mujallar ’Kunnen Gari
don taci gaba da banbancewa Mutanen Arewa tsantsar gari da ware masu tsaki da
ma sururu musamman daga shugabannin su kamar yadda take a duk fitowa tsawon
watanni ko ince yan shekaru. Kalaman gwamnan jihar Niger mai dauke da rawanin sardauna
masu nuna rashin damuwa da kisan sardaunan da tsame hannun marigayi Ojukwu a
lamarin a shekarar data gabata da irin yanayin da Arewa ta tsinci kanta a yau
ya sanya ni wannan tambihi. Wadancan kalamai na gwamna Mu'azu Babangida Aliyu
(Talban Minna) sun sani tunanin anya shima ba Inyamuri ba ne haifaffen Minna
kamar Ojukwu da aka Haifa a Zangeru ta jihar Niger ,
ba kamar yadda yace a baya ba cewa shi asali basakkwace ne.
Akwai abubuwa da ba dole suyi dadi ga wadanda suka
dauki wannan matsaya ba da yakamata mai girma ya sani kafin da bayan kisan
sardauna kafin nuna yiwuwar iya koyi ga Ojukwu a tawayen shi. A yadda mai girma
ke dauka, Dim, Chukwuemeka Ojukwu yayi bore ne ga gwamnatin tarayyar Najeriya
don amfanin ‘yan kabilar Ibo, bisa zargin danniyar da suke fuskanta daga sauran
sassan kasa.
Hakika yan Arewa irin su Genaral T.Y Danjuma da
Murtala Muhammad da wasu tsiraru daga kudu suka jagoranci kifar da gwamnatin
Genaral Aguiy Ironsi wanda Ibo ne a Yulin 1966. Kuma wani abu da yakamata a
kara sani shine; Ojukwu mutumin Ironsi ne sosai. Matar Ojukwu ta farko Njideka
Ojukwu tace walimar farko da Ikemba na Nnewi yaje da ita, itace ta Ironsi. Kuma
har yau akwai zumunci cikin iyalan biyu. Karewama Ironsi ne ya nada Ojukwu
gwamnan gabas.
Amma fa wancan mataki da sojan Arewa suka dauka, ba
son rai suka bi ba. Ya biwo bayan juyin mulkin 1966 ne da aka karkashe manyan
Arewa da masu alaka da kamar Sardauna, Balewa, Birgediya Ademulegan, Kanal
Shodeinde, Samual Akintola, Festus Okotie Eboh da sauran su. Da farko sija yan
kishin kasa sun dauki hakuri ganin rashin samun cikakkar nasara daga ainihin
masu juyin mulkin, amma Karin girma da Ironsi yayi ga makasan mai makon hukunta
su ya janyo fitinar. Bayanai sun nuna a sojoji 25 da ya kara ma girma ukku ne
kawai daga Arewa daya kuma bayerabe, watau daga jihar yamma. A wannan yanayi,
Ibo na Arewaci basu bari
mutanen yankin sun huta ba, (cikin izgili) sai suka rika rataye hoton gawar
sardauna cikin jinni ga Chukwuma Kaduna a gefe suna cewa “ga babana maganin
baban ka”. Wani mawaki mai suna Celestine Ukwu da yaga tsananin damuwa nasa
‘yan Arewa kuka, har wakar nuna jin dadi yayi mai taken “awakai na kuka”.
Wai ‘yan Arewa ne awakai. A can gabas kuwa ganin an
kasha sardauna a Kaduna
kamar anci yaki ne, sai sukayi ta tsallen murna, in banda kalilan. Daga ‘yan
kadan da suka hango daren dake tafe sun hada da wani ma’aikacin difulomasiyyar
Najeriya a Amurka watau Bernard Odugwu. A wani littafi nashi mai suna “ no
place to hide, crisis and conflicts inside Biafra” yace mutanen mu masu
ikirarin kawo sauyi sun tsare manyan Arewa sunyi masu mugun kisa sannan sun
kara wa kan su mukamai a soja… to lallai ko ba
jima ko ba dade sai irin haka ta faru a kan
mu. har ya kawo wani Karin Magana na Shakespare mai cewa uba ba fin uba yayi
ba. Duk da zargin da akeyi na cewa Nnmandi Azikiwe na da masaniyar abin da zai
faru a wannan rana, amma jin munin abin ya sashi karaya. Domin an jiwo yana
cewa “kashe manyan yan siyasa na wani bangaren kasa irin haka da shugabannin
sojan su zai iya janyo ma kasa bala’i….
No comments:
Post a Comment