Arafah
|
Dubun-dubatar Alhazai |
|
Dutsen Arafah |
ARFAH:
Manzan Allah SWA ya ce mafi alkhairin addu'ah a wajen Allah SWA ita ce
wadda aka yi a cikin wannan rana ta 9 ga zul haj, Alhazai suna filin
Arfah suna gudanar da Ibadah da addu'o'i da karatun Qur'ani da neman
gafara da sauran ayyukan Ibada, a yayin da wadan da suke gida suke raya
yinin wannan rana da Azumi da zikiri da karatun Qur'ani da kyauta da
Sadaka da kuma sadar da zumunci. Yana da kyau a wannan yini mu yawaita
addu'ah ga kawukanmu da al'ummarmu da kasarmu da kuma shugabanninmu.
Lallai mu yi kokarin kyautatawa 'yan uwanmu mu ciyar da marasa galihu,
mu yi sadaka, mu yawaita addu'o'i a koda yaushe a cikin wannan yini mai
albarka. Allah ya karbi Azumin da muke, Allah ya bamu ladan da ya
alkawartawa masu Azumtar wannan rana. Alhazanmu kuma Allah yasa su yi
Hajji karbabbe. Allahumma Taqabbal Minna Salihal A'amaluna.
Yasir Ramadan Gwale
14-10-13
No comments:
Post a Comment