DAN
GIYA: Ina zaune naji wasu mutane suna labarin cewar duk dan giya ya fi
kowa dacewa da samun matar aure ta kirki. Suka ce zaka samu mafiya
yawancin 'yan giya, idan sun sha sun bugu su yi ta yiwa matansu amai
suna zazzaginsu amma matan na hakuri, kuma suna nuna soyayya a garesu.
Wannan maganar ta shiga kunnena sosai.
Wannan ya tuna min da wata waka da wani mawaki ya raira mai suna ZAMA NA AURE, inda yake cewa "Zama na aure yana da dadi yana da daci . . ." Mawakin ya bayar da wasu labarai guda hudu a cikin wakar tasa, a labari na uku daya bayar ya yi kama da abin da naji wadannan mutanan suna tattaunawa akan dan giya. Ga abinda wakar ta ke cewa:
Zama na Aure Yana da dadi yana da daci maĆ”urata ashe soyayya da dadi…
Shi ko Gambo kunga dan giya ne
Sai can dare zai dawo gida nai
Da rangaji zai shigo gida nai
Ta kasa barci matarsa zaune
Bugu na kofarsa ma dabanne
Ta je ta bude ya yi shigowa
Da ya shigo zai fara hararwa
Ruwa ta debo tai tsabtacewa
Yana ta zaginta da dadawa
Ita ko kwalla take zubarwa
Kullum nasiha take gare shi
Dan ilimi gunta kwai yawan shi
Dan ilimin addini akwai shi
Sannu a sannu a kwan-a-tashi
Ya nutstsu tsaf-tsaf idan ka ganshi
Ya daina shaye ya canza halinshi
Gambo ai soyayya da dadi…..
Wannan labarin shakka babu ya yi kama da abinda naji wadannan mutane suna tattaunawa. Haka kuma, akwai wani mutum da na sani shi da kansa ya bani labari cewar a lokacin da yake shan giya, matarsa har wanka take yi masa, ya zageta ya fasa mata kaya amma bata damuwa, tana nuna masa soyayya tana masa Wa'azi da Nasiha. AMMA ME YA SA 'YAN GIYA SUKE DACEWA DA MATAN KIRKI?

No comments:
Post a Comment