Yasir Ramadan Gwale |
TUNATARWA:
A bara bayan na yi wanka zan saka kayan Sallah dan zuwa Masallacin Idi,
kawai sai naji sakon Text ya shigo wayata, har zan saka kaya na, sai
wata zuciyar ta ce na duba sakon, ko da na duba sai naga Sakon Nassir
Danbatta ne yake tunasar da ni addu'ar sanya sababbin kaya. Hakika
wannan tunasarwa ta yi amfani a gareni a lokacin, domin da taimakon
sakonsa ne na tuna addu'ar sanya sabbin tufafi, watakila da bai turo ba
haka nan zan sanya kaya na ba tare da wata addu'ah ba. Manzon Allah ya
yi gaskiya, Ya ce ku tunasar domin tunasarwa tana amfanar Muminai.
Yasir Ramadan Gwale
14-10-13
No comments:
Post a Comment