Monday, October 21, 2013

Ojukwu Da Rawar Da Ya Taka A Juyin Mulkin Janairun 1966


OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN MULKIN JANAIRUN 1966!!! (2)
Munanan abubuwa sun ci gaba da faruwa a Arewa, kamar kama daliban jami’ar A.B.U yan kabilar Ibo da akayi da makamai suka ce an aiko masu ne daga gida dan su farwa 'yan Arewa. Aka kara kama wani Ibo da bom zai jefa a Lugard Hall lokacin taron manyan Arewa. Aka kama wasu Ibo suma da bom zasu saka a Hamdala Hotel da babbar gadar Barnawa/Narayi, irin wannan mummunan nufi da muguwar niyya ta Ibo sun taimaka wajen tsanar inyamurai a daukacin jihohin Arewa.

Wancan tsaro da Allah ya baiwa mutanen Arewa ya firgita Ibo soai, ganin duk yunkurinsu bai kai ga gaci ba, Allah yana bankada asirinsu sai suka fara guduwa zuwa yankunansu na kudu maso Gabas. Ganin haka, suka fara koro ‘yan Arewa daga yankunansu, da haka ta faru sai suma ‘yan Arewa suka fara kora su gida can kudu. Wasu kuma ba korar su akayi ba, suna tunanin sojojin Ibo zasu kara sabon juyin mulki ne tun da an kashe Ironsi, don haka bai kamata su kasance a Arewa ba. Wasu kuma na zargin Arewa da shigo da makamai daga kashashen larabawa don yin jihadi. Wasu kuma jin haushi suke don ware wani sashi a bangaren shari’a aka ce na musulmi ne. Sannan wasu ayyuka da manyan su sukayi da suka san baza’a hakura ba, sun taimaka. Misali bayan kashe Laftanar Kanal Largema, janyo gawar sa sukayi daga bene kamar mushen kare daga benen Ikoyi Hotel dake Lagos. Sir Abubakar Tafawa Balewa kuma giyar burkutu Manjo Donatus Okafor ya bashi, yace masa idan yasha zasu kyale shi. Da sauran cin fuska da suka dinga yiwa manyan Arewa a lokacin kafin su karkashesu.

Wadannan dalilai ma sun taimaka ga hijirar Inyamurai daga yankunan Arewa. Yayin wancan guje-guje ‘yan Arewa na sayen kadarorin Inyamurai da suke guduwa, amma a yankin su na kudu babu wani mai sayen komai na dan Arewa. Sai dai ka dauko abin ka, idan ba na dauka bane kamar gida ko fili, ya zama ganima, haka suka wasashe manyan kadarorin da 'yan Arewa suka mallaka a yankunansu. Da abu ya lafa har kudin hayar gida da shaguna wasu Inyamurai sun iske an tara masu a Arewa, saboda Mutumin Arewa bai gaji zalunci ba. Hakan ta baiwa Ojukwu wanda ya rasu a 11 ga Nuwanban 2011 aka rufe shi a watan Mayun 2012 bayan gagarumin biki don zolayar ‘yan Arewa bisa jagorancin shugaba kasa Goodluck Jonathan da kuma damar da yake nema. Ojukwu Dama shi ne gwamna a jihar gabas, don haka sai yayi ta zuzuta lamarin inda yake cewa Ibo duk inda suke kar suyi tsammanin samun kariya ga rayuka da dukiyoyin su in dai ba a gabas suke ba. Ma’ana su koma gabas can ne za’a kare mutuncin su. Sai suka manta cewa yankin da yake zagi a yau can aka haife shi (har da Azikwe). Yayi ta kalamai dai irin na Nzeogwu mai cewa sunyi juyi ne don kabilanci da wariyar da ake nunawa ga sauran ‘yan kasa. Alhali sun biye wa son zuciya ne suka rabe da kabilanci. Domin duk wanda ya binciki tarihi zai fahimci zeogwu, Okafor da Ironsi sun samu tagomashi ne daga mutanen Arewa ne suka zama abin da suka zama kasancewar su haifaffu a yankin ne (banda Ironsi). Domin shi kansa Ironsi bai cancanci zama shugaban sojoji ba a lokacin Zakariyya Maimalari ne ya dace, amma Tafawa Balewa ya dankawa Ironsi duk dan a zauna lafiya, wannan abin da ya faru sai da ya so ya jawo baraka a tsakanin 'yan Arewa domin su sardauna sai da suka ja hankalin Tafawa Balewa akan Illar danka wannan muhimmin mukami ga Ironsi, Sardauna ya gawa Balewa cewa shi kenan ka kashemu! Haka kuwa akayi.

A 1965 kididdiga ta nuna cewa kashi 4 cikin 100 na mutanen Arewa ke rike da manyan mukaman gwamnatin tarayya. Zuwa 1966 kuma sama da kashi 25 cikin 100 na manyan ma’aikatan gwamnati a jihar Arewa mutanen kudu ne, mafiya rinjayen su yan kabilar Ibo. Ba’a maganar kananan ma’aikata. Bamu iya rike namu ba da har wani zai ce mun karbe masa na sa. Bisa la’akari da wadannan tabbatattun bayanai, wa ya jefa inyamurai cikin mawuyacin hali, idan ba Ojukwu ba?

Wani tsohon kwamishinan sadarwa na jihar Anambara zamanin gwamnatin Chinwoke Nbadinaju mai suna Prince Emeka Nkwocha ya baiyana Ojukwu kamar haka: Ojukwu mutun ne mai son rikici, da son a-sani tun yana matashi. Mutum ne da ya tashi cikin gata a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da talauci, hakan yayi tasiri a rayuwar sa. Don haka yakasance dan agwagwa, wanda baya bi sai dai abi shi. Sojoji Ibo da yawa sun zargi Ojukwu da kin taimakon Nzeogwu don bai baiyana shi a shugaban gwamnati ba, don haka ya tafi Biafra don jagorantar yan tawaye… Mujallar The Week 11 October 2004.

Zamu ci gaba In Sha Allah.

Sunday, October 20, 2013

Abin Da Ya Faru A Ghadir Khum

ABIN DA YA FARU A GHADIR KHUM

Daga Yasir Ramadan Gwale

Da farko yana da kyau al'umma su sani cewar Ahlussunnah sun yarda da dukkan wasu ingantattun Hadisai da suka nuna falala ko daraja ta Ali Ibn Abi-Talib (RADIYALLAHU ANHU). Ko kusa duk wasu maganganu da 'yan Shia'ah suke yadawa akan Ahlussunnah ba gaskiya bane, Ahlussunnah su ne mutanan da suka fi nuna kauna ta hakika ga Sayyadina Ali fiye da 'yan Shi'ah da suka kware masa baya shi da 'ya 'yansa Hasan da Husain. Ahlussunnah basu baiwa Ali Ibn Abi-Talib RA wani matsayi sama da wanda ingantattun Hadisai suka tabbatar masa da shi ba, dan haka ne ma, Ahlussunnah basa daukaka darajar Sayyadina RA akan Abubakar RA da Umar RA da Usman RA, wadannan gaggan Sahabbai suna da daraja sama da ta Sayyadina Ali RA kamar yadda ya zo a ingatattun Hadisai. Darajar da Sayyadina Abubakar RA yake da ita ko kusa bata tauye irin Darajar da Ali Ibn Abi-Talib RA yake da ita ba. Dukkan Ahlussunnah sun tafi akan cewa Ali-Ibn Abi-Talib shi ne Khalifan Manzon Allah na hudu bayan Abubakar da Umar da kuma Uthman Yardar Allah ta kara tabbata a garesu.

A lokacin da Manzon Allah SAW ya yi hajjin da ake kira Hajjin Ban-kwana a shekara ta 10 bayan Hijra. Ya aiki Ali Ibn Abi-Talib Yaman domin ya karbo Zakkah daga hannun Mutanan Yaman a wannan lokaci, bayan da Ali RA ya karbo Zakkar ne, sai wasu daga cikin Sahabbai suka nemi ya basu wani kaso daga cikin kason Dukiyar da ya karbo a Yaman, anan ne Ali ya sanar musu cewar ba shi da ikon yin tasarrufi akan wannan dukiya har sai Manzon Allah SAW ya zo. Bayan da Ali RA ya karbi wannan dukiya ta Zakkah ya hadu da Manzon Allah a Makkah bayan kammala aikin Hajji, inda suka tafi tare da Manzon Allah SAW dan komawa Madina, akan hanya ne Sahabban suka baiwa Manzon Allah Labarin abin da ya faru na hansu dukiya da Sayyadina Ali ya yi, shi ne Manzon Allah SAW ya yado zango a wani waje ko tafki da ake kira GHADIR KHUM inda ya yi Khuduba ya yabi Sayyadina Ali Ibn ABi-Talib RA a wannan Khuduba da ya yi, ya kuma wanke shi daga zargin da wasu daga cikin Sahabbai suka yi masa na kin basu wani sashi na dukiyar da suka nema.

A cikin Khudubar da Manzon Allah SAW ya gabatar ya yabawa irin namijin kokarin da Sayyadina Ali RA ya yi, wanda wannan yabo ko shakka babu karin daraja ce da Ahlussunnah basa inkarinta a wajen Sayyadina Ali RA inda Manzon Allah ya ce:
”من كنت مولاه فعلي مولاه، اللهم وال من والاه وعاد من عاداه وانصر من نصره واخذل من خذله”
Abin da yake nufi shi ne, Duk wanda Manzon Allah SAW ya jibinci al'amarinsa, to Ali ma ya jibanci al'amarinsa; Ya Allah ka jibinci wanda ya jibince shi, ka ki wanda ya ki shi; Ka tozarta wanda ya tozarta shi! Wannan Hadisi kusan, yana daga cikin Hadisin da ya fi yin fice a wajen 'yan Shiah, suna kambashi matukar kambamawa. Haka kuma, Wasu daga cikin Malaman Sunnah sun inganta wannan Hadisi na Ghadir Khum, sai dai, akwai sukar sahihancin gaba dayan maganar Hadisin, gabar farko ta wannan Hadisi bisa maganganu na Adalci ta inagnta daga Manzon Allah wato "DUK WANDA MANZON ALLAH YAKE MAJIBINCINSA TO ALI MA MAJIBINCINSA NE" Wannan ita ce maganar da ta tabbata daga Manzon Allah, Amma sauran gaba ta biyu da ta uku Sheikhul Islam Ibn Taymiyya RAHIMAHULLA ya rauninsu, cewar basu inganta. Amma sheikh Muhammad Nasiruddeen Al-Albani ya inganta gabar magana ta biyu bisa dogara da riwayoyin Sahabban da suka ruwaito ta sama da guda 20. Amma gabar maganar ta uku bisa Ijma'I wannan ko kusa bata inganta daga Manzon Allah SAW ba.

Ala-ayyihal, a bayyane yake cewar wannan Hadisi ya fadi falala dangane da Sayyadina Ali RA wanda ko kusa Ahlussunnah basa yin suka ko Inkarin dukkan wata daraja ko falala ta Sayyadina Ali da Manzon Allah SAW ya tabbatar masa. Inda zaka fahimci rashin gaskiya da rashin Adalci na Mabiya addinin Shi'ah masu bautar son zuciya shi ne, su sun yarda da dukkan wasu Hadisai da suka zo a cikin Litattafan Ahlussunnah da suka nuna falala da daraja ta Sayyadina Ali amma kuma suna kore duk wani Hadisi day a nuna Falalar sauran Sahabbai Musamman Abubakar da Umar da Uthman Allah ya kara yarda a garesu. Dan haka kada kaji wani mamaki idan dan Shi'ah ya kafa maka hujja da Hadisin Bukhari ko Musulim akan Sayyadina Ali. Amma inda gizo yake sakar shi ne basa yarda da dukkan wasu Hadisan da suka nuna falalar Abubakar da Umar da Uthman Yardar Allah ta kara tabbata a garesu; wanda a wajen Ahlussunnah falalarsu da darajarsu tana tafiya ne bi-da-bi wato Daga Abubakar sai Umar Sai Uthman sai Ali Yardar Allah ta kara tabbata a garesu baki daya.

Dan haka, Ahlussunnah suna son Sayyadina Ali RA suna kaunarsa suna jibintarsa, hasalima duk wata soyayya da su masu bautar son zuciya 'yan Shiah da suke nunawa ga Sayyadina Ali zaka samu ba gaskiya bace, domin sun fifita dansa Husain akansa, wannan kuma shi yake nuna irin wuce gona da irin na masu addinin Shi'ah, da kuma rashin sanin addinin Musulunci gabaki dayansa, da jahilci da sauya gaskiya duk suntabbata a garesu.

A wannan lokacin ne, musamman 18 ga wannan wata na Zul-Hajji lokacin da Manzon Allah ya yi wannan Kuhbah a Ghadir, 'yan Shia'ah suka mayar da wannan rana wani lokacin biki, da kide-kide da wake-wake da futsara kala-kala, suna kuma ta yada maganganu na karya cewa wannan Hadisi ya nuna cewar Sayyadina Ali shi ne Khalifa bayan Manzon Allah SAW, wanda yada wannan magana kamar tuhuma ce kai tsaye ga Sayyadina Ali, domin idan ka ce Ali RA shi ne Khalifah bayan Manzon Allah, me ya sa shi Sayyadina Ali ya san cewar Manzon Allah ya ayyana shi a matsayin khalifa bayansa kuma ya yi Mubaya'ah ga Abubakar da Umar da Uthman Yardar Allah ta tabbata a garesu! Kaga wannan karara ya nuna cewar Tuhumar Sayyadina ALi suke da cewar ya sabawa Umarnin Manzon Allah akan Khalifanci, amma ya yi Muba'ah ga Abubakar da Umar da Uthman sannan Khilafa ta zo kansa. Wannan shi ne yake nuna tsantsar Jahlci da kuma nuna karyar 'yan Shiah da suke nuna cewar suna kaunar Sayyadina Ali da iyalan gidansa. Su din makiya ne ga Ahlulbaiti domin babu wadan da suka tozarta Ahlulbaiti kamar ‘yan Shi’ah.

Ojukwu Da Rawar Da Ya Taka A Juyin Mulkin Janairun 1966


OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN MULKIN JANAIRUN 1966.

Fitar da Mujallar ’Kunnen Gari’ bayan dogon nazari da wasu fitattu kuma ‘yan kishin kasa suka yi dan isar da abin da ya dace na ilimi kan yadda lamurran siyasa da zaman takewa ke gudana a Najeriya ganin yadda kafofin wayar da kai suka gaza aikin su ko suka bata aikin musamman a Arewa ya sanya fitar wannan Mujallar dan ta Ilmantar ta kuma zaburar da mutane. Allah ya albarkaci Mujallar ’Kunnen Gari don taci gaba da banbancewa Mutanen Arewa tsantsar gari da ware masu tsaki da ma sururu musamman daga shugabannin su kamar yadda take a duk fitowa tsawon watanni ko ince yan shekaru. Kalaman gwamnan jihar Niger mai dauke da rawanin sardauna masu nuna rashin damuwa da kisan sardaunan da tsame hannun marigayi Ojukwu a lamarin a shekarar data gabata da irin yanayin da Arewa ta tsinci kanta a yau ya sanya ni wannan tambihi. Wadancan kalamai na gwamna Mu'azu Babangida Aliyu (Talban Minna) sun sani tunanin anya shima ba Inyamuri ba ne haifaffen Minna kamar Ojukwu da aka Haifa a Zangeru ta jihar Niger, ba kamar yadda yace a baya ba cewa shi asali basakkwace ne.

Akwai abubuwa da ba dole suyi dadi ga wadanda suka dauki wannan matsaya ba da yakamata mai girma ya sani kafin da bayan kisan sardauna kafin nuna yiwuwar iya koyi ga Ojukwu a tawayen shi. A yadda mai girma ke dauka, Dim, Chukwuemeka Ojukwu yayi bore ne ga gwamnatin tarayyar Najeriya don amfanin ‘yan kabilar Ibo, bisa zargin danniyar da suke fuskanta daga sauran sassan kasa.

Hakika yan Arewa irin su Genaral T.Y Danjuma da Murtala Muhammad da wasu tsiraru daga kudu suka jagoranci kifar da gwamnatin Genaral Aguiy Ironsi wanda Ibo ne a Yulin 1966. Kuma wani abu da yakamata a kara sani shine; Ojukwu mutumin Ironsi ne sosai. Matar Ojukwu ta farko Njideka Ojukwu tace walimar farko da Ikemba na Nnewi yaje da ita, itace ta Ironsi. Kuma har yau akwai zumunci cikin iyalan biyu. Karewama Ironsi ne ya nada Ojukwu gwamnan gabas.

Amma fa wancan mataki da sojan Arewa suka dauka, ba son rai suka bi ba. Ya biwo bayan juyin mulkin 1966 ne da aka karkashe manyan Arewa da masu alaka da kamar Sardauna, Balewa, Birgediya Ademulegan, Kanal Shodeinde, Samual Akintola, Festus Okotie Eboh da sauran su. Da farko sija yan kishin kasa sun dauki hakuri ganin rashin samun cikakkar nasara daga ainihin masu juyin mulkin, amma Karin girma da Ironsi yayi ga makasan mai makon hukunta su ya janyo fitinar. Bayanai sun nuna a sojoji 25 da ya kara ma girma ukku ne kawai daga Arewa daya kuma bayerabe, watau daga jihar yamma. A wannan yanayi, Ibo na Arewaci basu bari mutanen yankin sun huta ba, (cikin izgili) sai suka rika rataye hoton gawar sardauna cikin jinni ga Chukwuma Kaduna a gefe suna cewa “ga babana maganin baban ka”. Wani mawaki mai suna Celestine Ukwu da yaga tsananin damuwa nasa ‘yan Arewa kuka, har wakar nuna jin dadi yayi mai taken “awakai na kuka”.

Wai ‘yan Arewa ne awakai. A can gabas kuwa ganin an kasha sardauna a Kaduna kamar anci yaki ne, sai sukayi ta tsallen murna, in banda kalilan. Daga ‘yan kadan da suka hango daren dake tafe sun hada da wani ma’aikacin difulomasiyyar Najeriya a Amurka watau Bernard Odugwu. A wani littafi nashi mai suna “ no place to hide, crisis and conflicts inside Biafra” yace mutanen mu masu ikirarin kawo sauyi sun tsare manyan Arewa sunyi masu mugun kisa sannan sun kara wa kan su mukamai a soja… to lallai ko ba jima ko ba dade sai irin haka ta faru a kan mu. har ya kawo wani Karin Magana na Shakespare mai cewa uba ba fin uba yayi ba. Duk da zargin da akeyi na cewa Nnmandi Azikiwe na da masaniyar abin da zai faru a wannan rana, amma jin munin abin ya sashi karaya. Domin an jiwo yana cewa “kashe manyan yan siyasa na wani bangaren kasa irin haka da shugabannin sojan su zai iya janyo ma kasa bala’i….

Friday, October 18, 2013

Hattara Dai Musulmin Najeriya!!!


HATTARA DAI MUSULMIN NAJERIYA

Wannan kira ne na gaggawa ga dukkan Musulmi maza da mata a kasarnan, Musamman wakilanmu na majalisar kasa dake Abuja.

Makarantar Horon Soji ta Kaduna da aka fi sani da NDA ta buga a shafin jaridar Daily Trust ta ranar Juma'a 23 ga watan Agusta na wannan Shekarar, sunayan daliban da aka dauka a wannan Makaranta a karo na 65 inda suka bada sunayan daliban da aka dauka a a jihohin Arewa Musulmi kamar haka:

1. Adamawa:
- Muslimai -3
- Kiristoci -10

2. Bauchi:
- Muslimai – 7
- Kiristoci – 7

3. Borno:
- Muslimai – 5
- Kiristoci – 8

4. Gombe:
- Muslimai – 4
- Kiristoci – 10

5. Kaduna:
- Muslimai – 3
- Kiristoci – 11

6. Kebbi:
- Muslimai – 6
- Kiristoci – 7

7. Taraba:
- Muslimai – 3
- Kiristoci – 10

Wannan fa kadan ne daga cikin irin muguwar manakisar da ake shirya mana a Arewa. A jihar Plateau ba'a dauki Musulmi ko guda daya ba. Ina shugabannin Musulmi, da kungiyoyin Musulmi da Malaman addini? Lallai dole mu tashi tsaye mu nuna rashin amincewarmu da wannan cin kashi da ake yi mana.

Yasir Ramadan Gwale
18-10-13

Thursday, October 17, 2013

Wa Ye Masoyin Manzon Allah SAW?


WAYE MASOYIN MANZON ALLAH?

Kaunar Manzon Allah SAW shi ne yi masa cikakkiyar da'a da biyayya ba tare da tuhuma ko titsiye akan duk abinda ya zo da shi ba Salallahu Alaihi Wasallam. Sahabban Manzon Allah SAW su ne manyan abokansa, Almajiransa, Aminansa, Majibintansa masu kaunarsa SAW kauna ta hakika, sun yi masa cikakkiyar biyayya irin biyayyar da babu wani mahaluki da ake yiwa ita a fadin duniyar nan. Bisa tsarin addinin Musulunci na ADALCI da kyautata zato, baka taba ji a tsakanin Sahabbai an kira wani da sunan cewar shi ne "MASOYIN MANZON ALLAH BA" ko shakka babu ana kyautata zaton cewar duk wani Musulmi ya fifita soyayyar Manzon Allah SAW akan kansa, balle wani mahaluki.

A dazu da rana muka samu labarin rasuwar wani Mawaki a cikin Birnin Kano da ake cewa yana wakokin yabon Annabi SAW. Wannan mawaki yana wakokin yabon Annabi ne da kida da busa sarewa da jita da sauran kayan kide-kide wadan da suka sabawa koyarwar Manzon Allah SAW, wanda yin hakan sabawa hakikanin koyarwar Manzon Allah SAW ne, muna yi masa uzurin watakila ya aikata hakan bisa rashin sani. Allah ya yafe masa kurakuransa.

Abinda ya biyo bayan rasuwar wannan bawan Allah shi ne, irin yadda muka ji ko muka ga wasu na daukaka shi da sunan cewa "MASOYIN MANZON ALLAH" shin akwai wani Musulmi na hakika da ba masoyin Manzon Allah bane? Masu yin wannan kiran shin suna nufin cewar shi wannan mawaki ya fi su kaunar Manzon Allah ne? Idan ka ce wane Masoyin Manzon Allah ne, to kamar kana cewar duk wanda ba shi ba to ba masoyin Manzon Allah bane. Haka idan ka ce Musulmi sune masoyan Manzon Allah, dan haka duk wani wanda ba Musulmi ba to ba masoyin Manzon Allah bane, wannan babu wanda zai zarge ka da yin kuskure.

Akwai wani marubuci bature Kirista, wanda ya rubuta wani littafi mai suna FITATTUN MUTANE 100 a duniya, a cikin mutum dari da ya zana, Manzon Allah SAW shi ne na farkonsu, ya kuma yi kalamai na yabo sosai akan Manzon Allah SAW, Shi kenan wannan sai ya bayu a garemu cewar wannan marubuci masoyin Manzon Allah ne, alhali bai yi imani da addinin da Manzon Allah ya zo da shi ba. Lallai soyayyar Manzon Allah SAW ba furta kalamai ko rera waka bane, soyayyar da zaka yiwa Manzon Allah ta amfaneka a Lahira ita ce yi masa cikakkiyar da'a da biyayya da Sallalamawa dukkan koyarwarsa da ta sahabbansa shi ne abina zai tsiratar da mutum a ranar gobe kiyama. Allah ya yi dadin tsira a gareshi Salallahu Alaihi Wasallam da Alayensa da Sahabbansa da wadan da suka bi tafarkinsu da kyautatawa har ya zuwa ranar sakamako.

Allah ka jikan Musulmi, wadan da suke kwance marasa lafiya gida da asibita Allah ya basu lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
17-10-13

Sana'a

Kudi

SANA'A: Wani sata yake ya ciyar da kansa da iyalinsa, wani ya yi faskare, wani ya yi karya ya samu abin duniya, wani Halal yake nema bil-hakki da gaskiya, wani kuma ya sani sarai Haram yake ci amma bai damu ba. Wasu da dama babu ruwansu ko Halal ko Haram indai zasu samu basa bambancewa, da yawa sai sun sha wahala suke samun abinda za su rufawa kansu asiri, wasu suna shan wahala ne wajen neman halal, wasu kuma Haram suke nema kuma suna shan matukar wahala wajen nemanta, amma haka nan suke ciyar da da kansu da ita; wasu kuma suna samun Halal kamar tsinkowa suke a Bishiya babu wata wahala da suke sha. ALLAH KENAN BUWAYI GAGARA MISALI, DA YA AJIYE KOWA A INDA YAKE. AMMA SHAKKA BABU ALKALAMIN DA BAYA RUBUTA KUSKURE YANA RUBUTA AYYUKAN KOWA. KOWA ZAI KARBI LITTAFINSA YAGA SAKAMAKON ABINDA YA AIKA. WASU ZASU DINGA CEWA LIMANIL HAZAL KITAB LA YU-GHADIRU SAGHIRATAN WALA KABIRATAN. (Wannan wane irin littafi ne da bai bar komai ba sai da ya taskance! Inna Lillahi Wa'Inna Ilaihi Raji'un) Lallai mu yi dukkan mai yuwuwa wajen ganin mun nemi halal a cikin sana'o'inmu da ayyukanmu, Manzon Allah SAW yace duk tsokar naman da ta tsiro da Haram babu Shakka wuta ce mafi cancanta da ita. Wannan ya rage ga masu cin Haram su ci da yawa ko su ci kadan, Tabbas maganar Manzon Allah SAW gaskiya ce. Masu neman Halal kuwa su cigaba da Hakuri, komai wuya komai tsanani, Allah yana san masu hakuri.
Yasir Ramadan Gwale
17-10-13

Wednesday, October 16, 2013

Lokaci

 
Lokaci
LOKACI: A cikin dukkan rayuwar halittar Ubangiji, babu wani abu da Allah SWT ya halitta wanda yake tafiya baya tsayawa sai lokaci. Hakika Lokaci shi ne abinda yafi komai muhimmanci a cikin dukkan rayuwar Bani-Adama. A saboda irin Muhimmanci na lokaci Allah ya buga misalai da dama da lokaci a cikin littafinsa mai tsarki (QURAN) Haka kuma, a cikin sura ta 103 Allah SWT da kansa ya yi rantsuwa da lokaci. Wannan kadai ya isa ya nuna mana Muhimmancin lokaci, da yawan mutane da zasu riski sa'ar karshe a rayuwarsa a tambayi me suke so a gidan duniya, babu Shakka karin lokaci za su nema. Sahabbai sun kasance suna yiwa Manzon Allah SAW tambaya game da lokaci (ALKIYAMA) Allah SWT da kansa ya barwa kansa sanin wannan lokacin. Hakika, lokaci yana da matuqar Muhimmancin da ya kamata a bashi kowacce irin kulawa, amma a bayyane ta ke cewar Lokaci bai yi sa'ar iyayan gida ba, sai dai kadan daga cikinmu da suke girmamashi. An haifemu a cikin lokaci, zamu mutu a cikin lokaci, Tabbas LOKACI shi ne abinda zai ga bayan dukkan Bani-Adama gaba dayansu na farkonsu da na karshensu, babu wani mahaluki da zai iya tsayar da lokaci. MU GIRMAMA LOKACI, MU MUTUNTA LOKACI, MU ALKINTA LOKACI. Lallai mu sani Lokaci baya jiran kowa, domin shi matafiyi ne.

Yasir Ramadan Gwale
17-10-13

Sallar Eid-al-adha


Comrade Yasir Ramadab Gwale tare da Muhammad Aminu Bin Inuwa Galadanci bayan kammala Sallar Idi a masallacin idi na jami'ar Ifriqiyya a jiya Talata.

15-10-13

NAMAN SALLAH: Mugunta Ce Ko Keta?

Naman Sallah

NAMAN SALLAH: MUGUNTA CE KO KETA?

Sau da dama na kan yi mamaki irin yadda muke ta kiran addini a baki! Bayan addini ya nuna mana 'yan uwantaka da zumunci da taimakekeniya da kaunar juna da kusanto da juna kusa. A Mafiya yawancin maganganunmu da suka shafi addini sun fi yawa a bakunanmu, musamman abubuwan da muke ganin an zalunce mu, abubuwan da mu ya kamata mu aiwatar, mu nuna kyakkyawar koyarwar addini bamu cika kulawa ba, mun fi kauri wajen cewa Shugabanni suna zaluntarmu, bama ganin abubuwan da muke tsakanin junanmu na cin dunduniya, da gulma da munafurci da kyashi da kyeta a matsayin wani laifi, muna take laifin da muke aikatawa junanmu muna hango wanda ake aikata mana.

Abin mamaki ne kwarai da gaske a ce mutane sun soya naman SALLAH suna ta ci suna gudawa, cikinsu yana murdawa, amma makotansu da dama basu da naman da za su ci. Malam Saluhu wani Ladani ne wani lokaci ya gayamin cewar wallahi Haka aka yi Sallah aka gama ko kanshin nama bai ji ba, dan kawai kasancewarsa ba shi da iyaye a inda yake, babu kuma wanda ya damu ya kawo masa nama ya dan lasa. Sai na kasa gane wai mugunta ce ko kyeta ce ta ke sanyamu mu ajiye nama mu kadai da Iyalanmu muna ci muna ta tsuga zawayi, amma haka nan muke ta afawa a cikkunanmu.

Alhamdulillah, wasu jama'a da dama sukan yi yanka su rabawa jama'a nama, amma galibi abin da suke ajiyewa a gidajensu suna ci su kadai da iyalansu ya yi yawa matuqa. Ya 'yan uwa masu girma, lallai sai mun nunawa junanmu soyayya da kauna ta hanyar nuna kyakykyawar mu'amala da taimakekeniya, irin dan naman da muke kakkasawa a faranti muke rabawa, bayan mun ciccika kwallaye da soyayyan nama, ya yi kadan. Wani bawan Allah ya shaidamin cewa yana yanka Saniya da raguna biyu, amma nama a gidansa baya wuce mako guda ya kare, saboda rabarwa da Iyalinsa take yi, tun yana nuna damuwa har ya fahimci cewa lallai abinda iyalin nasa ta ke yi shi ne abinda ya kamata a ce mata suna yi. Allah ya shiryemu shirin addini.

Daga karshe ina tunasar da mu kabbarori ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA ILA HA ILALLAH, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR WALILLAHIL HAMD.

YASIR RAMADAN GWALE
16-10-13

Tuesday, October 15, 2013

BARKA DA SALLAH

Ifriqiyya Eid Ground Khartoum, Sudan


BARKA DA SALLAH

Ina yiwa daukacin 'yan uwa da abokan arziki Barka Da Sallah, Allah ya karbi dukkan Ibadunmu na wannan shekarar mai karewa, ya yafe mana kurakuran da muka gabatar muna sani ko mun gafala, Ya Allah kada ka kama mu da laifukan kawukanmu, Ya Allah kai mai afuwa ne kana son Afuwa, Allah ka yi mana afuwa.

ALLAH YA MAIMAITA MANA CIKIN NI'IMA DA KOSHIN LAFIYA DA KARUWAR IMANI. WANNAN ITA CE KWALLIYAR SALLAR TAWA FARAR SHADDA DA BAKIN TAKALMI DA JAR DARA IRIN WADDA NA SABA SAWA, HAKIKA ZAINAB TA GANI TA KUMA YABA, DAN HAKA KUWA YANZU KASUWA TA FARA CI.

Monday, October 14, 2013

Tunatarwa

Yasir Ramadan Gwale

TUNATARWA: A bara bayan na yi wanka zan saka kayan Sallah dan zuwa Masallacin Idi, kawai sai naji sakon Text ya shigo wayata, har zan saka kaya na, sai wata zuciyar ta ce na duba sakon, ko da na duba sai naga Sakon Nassir Danbatta ne yake tunasar da ni addu'ar sanya sababbin kaya. Hakika wannan tunasarwa ta yi amfani a gareni a lokacin, domin da taimakon sakonsa ne na tuna addu'ar sanya sabbin tufafi, watakila da bai turo ba haka nan zan sanya kaya na ba tare da wata addu'ah ba. Manzon Allah ya yi gaskiya, Ya ce ku tunasar domin tunasarwa tana amfanar Muminai.

Yasir Ramadan Gwale
14-10-13

Arafah

Dubun-dubatar Alhazai

Dutsen Arafah

ARFAH: Manzan Allah SWA ya ce mafi alkhairin addu'ah a wajen Allah SWA ita ce wadda aka yi a cikin wannan rana ta 9 ga zul haj, Alhazai suna filin Arfah suna gudanar da Ibadah da addu'o'i da karatun Qur'ani da neman gafara da sauran ayyukan Ibada, a yayin da wadan da suke gida suke raya yinin wannan rana da Azumi da zikiri da karatun Qur'ani da kyauta da Sadaka da kuma sadar da zumunci. Yana da kyau a wannan yini mu yawaita addu'ah ga kawukanmu da al'ummarmu da kasarmu da kuma shugabanninmu. Lallai mu yi kokarin kyautatawa 'yan uwanmu mu ciyar da marasa galihu, mu yi sadaka, mu yawaita addu'o'i a koda yaushe a cikin wannan yini mai albarka. Allah ya karbi Azumin da muke, Allah ya bamu ladan da ya alkawartawa masu Azumtar wannan rana. Alhazanmu kuma Allah yasa su yi Hajji karbabbe. Allahumma Taqabbal Minna Salihal A'amaluna.
 Yasir Ramadan Gwale
14-10-13

Sakon Barka Da Sallah Daga Yasir Ramadan Gwale Da Zainab Gwale


BUKUKUWAN SALLAH DA BARKA DA SALLAH

Da dama daga cikinmu sun dauka lokacin bikin Sallah wani lokacin ne na walwala da jin dadi da gwangwajewa da ciye-ciye da ziyarce-ziyarce. Wannan ko shakka babu abu ne mai kyau a ci a sha a yi hani'an a lokacin bukukuwan Sallah, a kuma kai ziyara zuwa ga 'yan uwa da abokan arziki a sadar da zumunci; amma ya tabbata a Sunnah cewa lokutan Bikin Sallah lokutane ne na zikirin Allah bayan ci da sha, Manzon Allah SAW yace a yawaita ambaton Allah a cikin kwanakin "ayyamut tashreeq", ana son a yawaita yin kabbara, ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR LA'ILA HA'ILALLAH ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR WALILLAHIL HAMD, zai ai ta maimai ta wadannan kabbarori ne a cikin wadannan kwanaki ba wai iyakar ranar Idi ko a Masallacin Idi kawai wani zai dinga fada wasu na maimaitawa ba, ana son kowa ya shagala da yin wannan Zikiri yana jiyar da kansa, wadan da kuma suka mance babu laifi a daukaka murya dan tunasar da su, kamar yadda ya tabbata a aikin Sahabbai.

Mu ambaci Allah ambato mai yawa, mu nemi yafiyarsa akan laifukanmu wadan da muka sani da wadan da ba mu sani ba. Haka kuma, a guji aikata laifukan sabo a yayi shagulgulan sallah, kamar cakuduwa maza da mata a gidajen shakatawa, a kuma lura da kaikawon yara kanana, idan anga yara na zarya a wajen mai sai da taba sigari lallai a hanzarta daukar matakin da ya dace, dan yara da dama sukan koyi zukar taba sigari a lokacin bukukuwan Sallah. 'Yan mata kuma yana da kyau a fito cikin shiga ta mutunci dan kare mutunci da martaba.

Allah ya sa ayi Sallah tare da Bukukuwan Idi Lafiya, a kuma yi hankali da cin nama babu kakkautawa, domin ance likitoci na yajin aiki.

A madadin Yasir Ramadan Gwale da Zainab Gwale muke ce muku BARKA DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA TA BADIN BADADA YA KUMA KARBI IBADUNMU.


Signed
Yasir Ramadan Gwale
14-10-13

Sunday, October 13, 2013

Mecece Mafitar Halin Da Arewa Ke Ciki?

MECECE MAFITAR HALIN DA AREWA TA KE CIKI?

Batun halin da Arewa ta ke ciki na zubewar mutunci da kima da haiba da kamala da koma baya ta fannin tattalin arziki da sukurkucewar Ilimi da lalacewar makarantu da kiwon lafiyar da asibitai suka zama tamkar makabartu da al’amuran tsaro da suka jagwalgwale suka hana kowa walwala da jin dadi, kusa wadannan da ma wasu sun damu duk wani dan AREWA mai kishi babba ne ko karami, mace ce ko Namiji. Yau a Arewa babu wani wanda zaka titsiye ka tambayeshi halin da ake ciki ya yi maka hamdala da godiya da wannan hali da muke ciki, sai dai fa idan tantagaryar makiyin Arewa ne makiyin Najeriya wanda baya son cigaban Arewa da Najeriya. Halin da muke cikin ya wuce duk yadda ake zato, domin wani abin ma idan mutum yaji sai yaji kamar ba gaskiya bane, ba wai kawai lalacewa Arewa ta yi ba, a’a komawa baya take a sukwane, Kamar Misalin motace ka baiwa dan koyo kuma ya sanya giyar reverse yana gudun tsiya, shakka babu dole ya yi barna, ba wai motar kadai zai mammokada ya lallauya tayoyin  ba har da duk abinda ya samu akan hanya sai ya bangajeshi mai gyaruwa ya gyaru wanda ya mutu ya mutu kenan; to kamar misalin irin haka Arewa take a yanzu, a halin da muke ciki.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta addabi samarinmu maza da mata, Ilimin makarantun hukuma ya tabarbare makarantun gwamnati sun zama garken jahilai, malaman babu ilimi, daliban babu ilimi gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da sauran al’umma da ake kira “community” a turance kowa ya kame hannunsa daga lalacewar ilimi anyi ko in’kula, kowa ya gwammace idan zai iya ya dauki dansa ya kaishi makarantar kudi, wanda kuma bashi da karfi alal-larurati ‘ya ‘yansa suke karatu a makarantun gwamnati ba dan ransa yana so ba, sai dan bashi da yadda zai yi. Irin wannan mawuyacin halin hannu baka hannu kwarya, ya sanya da dama dagacikinmu suka fara yanke tsammani daga Ubangiji, wasu suka bazama neman yaki halal yaki haram, Mutane burinsu su tara dukiya babu ruwansu da tsarkinta.

Yanzu a Arewa yaro da babba, mace da Namiji, almajiri da wanda ba al’majiri ba, mai gata da mara gata, mai mulki da wanda ake mulka; Kusan kowa neman damar dan uwansa yake, ta ina zai samu dama ya kwashe kafufuwan duk wanda Allah ya dorawa kaddarar fitar rabo. Cuta da cutarwa ta zama ruwan dare gama duniya, babu malamai babu jahili, masu hankali da marasa hankali kowa neman hanyar cuta yake, yan kasuwa da masu sari, leburori da iyayan gidansu; daman ma’aikatan gwamnati ya zamar musu tamkar halaliya yin almundahana da kayan hukuma, a sace duk abinda zai iya satuwa, tundaga masu gadi har oga kwata-kwata duk wanda ya samu abin dauka indai na hukuma ne, to gaban kansa yake ya dauka, tamkar wanda ubansa ya mutu ya bar masa gado shi kadai, a sace man jannareto, a sace fanka a saci tabarma da darduma, wani abinma bai kai a sace shi ba, amma saboda tsabar mutuwar zuciya, sai ma’aikata su dinga satar abinda ko kadan ba zai amfanesu ba, illa kawai wani tunani da ya dade da yin tsiro a zukatan al’umma na cewa “raba arne da makami ibada ne” dan haka ake ganin kayan hukuma kamar ganima.

Wannan yanayin shi ne wani irin mawuyacin lokaci da Arewa bata taba mafarkin samun kanta a cikin irinsa ba. Magabatan shugabanninmu sun barmana kyakkyawan abin gado, sun gina harsashin samun ingantacciyar rayuwar wadan da zasu zo baya, sun samar mana da Gidan jaridar NNN da gidan Radio Najeriya Kaduna, da kamfanonin murza auduga na Arewa da Babban Bankin Arewa da makarantun tundaga kwalejoji da jami’o’I da makarantun koyon sana’a, da makarantun horas da malamai da sauransu da dama, amma basu yi sa’ar samun hannu na gari da zai iya alkinta su ba, wannan duk wanda ya san Arewa ya san halin da ta ke ciki zai iya bayar da shaida akan haka. To amma hakikanin gaskiya tafiya tayi tafiya, tura ta kai bango, lokaci ya yi da za’a zauna zama na gaskiya a kalli halin da muke ciki dan dawo da martabarmu da aka yi mana shaida da ita tun a baya.

Haka kuma, lokaci ya yi da zamu ja layi akan dukkan wasu laifuka da muke ta zargin kawukanmu da aikatawa, tunda halin da muke ciki ya shafi kowa da kowa, babu wanda yake walwal cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kusakurai an riga anyisu manya da kanana, dan haka, abinda ya kamata mu maida hnaklai shi ne kokarin nemo mafita da bakin zaren halin da muke ciki. Shugabannin baya da kuma wadan da suka nannada kansu Shugabancin Arewa a yanzu duk sunyi abinda zasu iya, wadan da suka tafka ta’adi da wadan da suka yi abin kirki duk sunyi, kuma anga abin da kowa ya yi, Allah ya sakawa kowa da gwargwadon abin day a aikata, idan khairan khairn, idan sharran sharran.

Wata rana Shehu Jaha ya aiki diyarsa ta debo masa ruwa a tulu, sai ya yi mata kashedin kada ta sake ta fasa masa tulu, idan kuwa ta fasa to zasu gauraya, har ta kama hanya ta tafi sai Shehu ya kirata ya tsinko tsumagiya ya shashshauda mata, wani abokinsa ya ce haba Shehu yaya ka gargadeta kar ta fasa, bayan kuma bata fasa ba ka doketa. Sai Sheshu ya kada baki yace, babu amfanin na doketa a lokacin da ta riga ta fasa tulu, domin dukan ba zai sanya tulu ya dawo ba. Kamar misalin haka ne na irin halin da muke ciki, yawan zargin junanmu da laifin halin da muke ciki babu abinda zai kara, illa kara wagegen gibi a tsakaninmu, tunda matsaloli dai ana cikinsu tsamo-tsamo, batun ko laifin su wane ne ko ba laifin su wane bane, duk ya kamata mu wuce wajen, batun da ya kamata mu maida hankali shi ne ta yaya zamu fito daga cikin wannan halin da muke ciki shi ne abinda dukkanmu ya kamata mu maida hankali akai.

Dukkanmu dole mu ji tsoron Allah a cikin al’amuranmu, mu sanya gaskiya da amana a cikin mu’amalolinmu, shugabanni su zama adalai a ajiye komai a inda ya dace, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa, babu wasu mutane daga Ingila ko Faransa ko Amerika da za su zo su fitar dam u daga cikin halin da muke ciki, mune muka san kanmu, muka san halin da muke ciki, muka san irin azaba da radadin da muka shiga ciki, ya zama tilar mu hada karfi da karfe wajen fito da sahihan hanyoyi da zasu amfani ‘yan bayanmu masu zuwa nan gaba. Mu shata layi kamar yadda na fada, ko da bamu yafe irin satar da ‘yan uwanmu suka dibga ba, to mu dakatar da abin haka, kudin hukuma ba na uban kowa bane, na dukkanmu ne, idan mun alkinta dukiyarmu kanmu muka alknta, idan mun barnatar kanmu da jikokinmu muka yiwa illa.

Ya zama dole da Masu mulkinmu na Siyasa wadan da hakkin jagorancinmu yake a hannunsu, da shugabanni masu rike da sarautu, da malamai da kungiyoyi mu samar da wata Hadaka da zata fitar da mu daga cikin halin da muke ciki. Kamar yadda aka samu hadewar jam’iyyu dan kawai ga gaci da samun nasara, muma dole sai mun hade kanmu mun hade kungiyoyinmu, sannan mu samu nasarar fita daga cikin wannan mawuyacin halin da muke ciki. Akasin haka, babu abinda zai yi mana illa kara jefa mu cikin bakin ciki da damuwa da ba za su iya yi mana maganin halin da muke ciki ba, idan banda kara nesanta mud a juna. Dole mu dawo da ‘yan uwantaka tsakaninmu da kaunar juna, da taimakekeniya, mu cire kyashi, mu daina hassada, mu yiwa kanmu tarbiyyar hakuri da halin ‘yan uwanmu, mu kuma yi hakuri da halin talauci da kuma baiwa mawadatanmu uzuri. Ya Allah ka karkato da hankulanmu gaba daya mu fahimci juna dan ciyar da Arewa da Addininmu gaba, Allah ka taimakemu ba dan halinmu ba, ba dan munanan ayyukan da wasu daga cikinmu suka aikata ba. Allah ka taimakemu ka sa wannan shi ne lokacin da zamu yi ban-kwana da dukkan irin sarkakiyar da muke ciki da wahalar rayuwa. Allah ya taimaki Arewa da Najeriya baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
 13-10-13

SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: Babban Mai Zunubi Ne!!!


SHUGABA GOODLUCK JONATHAN: Babban Mai Zunubi Ne!!!

Hakika shugaban kasa Goodluck Jonathan ya shafawa fuskarsa toka, inda karara ya fito yake yakar Musulmi ta sunkuru da kuma bayyane. Irin yadda shugaban kasa yake amfani da addini yake yakar Musulmi a AREWA da KUDU MASO YAMMA abin ya kai innanaha, domin har ta kai cewar ko kunya baya ji wajen nuna kiyayyarsa ga Musulmi da Musulunci a kusannan dukkan rabon mukamai na gwamnatin tarayya, da kuma bayar da damarmaki ga 'yan kasa, inda babu kunya babu tsoron Allah shugaban yake ware Musulmi tare da nuna fifiko ga kiristoci na kudu da na Arewa. Kamar yadda ya faru a baya, kowa yaga yadda Shugaban Sojojin Najeriya Brigadier General Ihejirika ya zabge dukkan manyan sojoji Musulmi daga dukkan manyan mukamai, ya maye gurbinsu da kiristoci gaba ki daya, wannan karon ba wai 'yan Arewa kawai aka taba har da Yarabawa 'yan kudu Musulmi, abin da ya tabbatar da cewar shugaban karara Musulunci da Musulmi ne baya so a dukkan harkokin gudanar da gwamnatin wannan kasa.

Sanin kowa ne cewa yankin Kudu maso yammacin Najeriya inda Yarabawa suke da rinjaye, kuma Musulmi sune suke daukar kaso mafi yawa na al'ummar yarabawa, amma babu wani Minister ko mai baiwa shugaban kasa Shawara Musulmi da Goodluck ya dauka daga yankin, duk wani nade-naden da zai yi a wannan yankin KIRISTA yake nadawa babu kunya babu tsoron Allah. Kowa yana ji yana gani, amma anyi shiru, kowa baya son ace yana amfani da Addini dan kar ya raba kan kasa, amma shi shugaban yana yin gabansa gadi wajen cin dunduniyar Musulmi da kwashe musu kafafu, tare da amfani da kungiyar CAN suna ta kuwwar Iblis cewar ana nunawa kiristoci bambanci.

Kwatsam kuma sai muka ji rahoton cewar sojojin da ake dauka a makarantar horon soja ta Kaduna NDA nanma ankwashe kafafun musulmi warwas. Inda bayanai suka nuna cewar a cikin daliban da aka dauka a Kaduna 14 guda 11 duk kiristoci ne guda 3 ne kacal Musulmi, haka jihar Adamawa inda aka dauki dalibai 13 amma 11 duk kirista 2 ne kacal Musulmi, a Taraba ma haka aka yi kamar yadda aka yi a Adamawa inda 2 ne kacal Musulmi sauran 11 duk kirista ne, a jihar Plateau kuwa duk 13 gaba daya kirista aka dauka babu Musulmi ko daya. Wannan fa shine irin misalin rashin adalcin da shugaban kasa yake nuna mana ba tare da tsoro ko kunyar abinda zai je ya zo ba.

Haka kuma, kowa yana ganin yadda aka zuba mana sojoji galibinsu Kiristoci a musamman jihohin Adamawa, Borno da Yobe da sunan dokar ta baci suna ta yi mana kisan babu gaira babu dalili. Kiri-kiri ga sojoji da uniform suna aikata kisan kai ga talakawa bayin Allah da basu san hawa ba balle sauka sai a kauda kai a ce wai 'yan ta'adda ne suka yi mana wannan aika-aikar. Ya zama dole mu fito mu kalaubalanci wannan mummunan zunubin da shugaban kasa yake tafkawa. Najeriya kasarmu ce mu duka, mu bamu ce a dauki hakkin wani a bamu ba, amma ya zama dole, wajibi, tilas a bamu namu hakkin, kuma dole a ringa daukar ma'aikata gwargwadon adadin al'ummar da suke a Najeriya, wannan abin da shugaban kasa yake wallahi summa tallahi matakaine na yiwa Musulmi mummunar illa, koma anyi angama.

Muna da labarin irin abin da Shugaban Kamaru Poul Biya yayi wajen kakkabe hannun duk wasu Musulmi daga samun wasu manyan mukamai na soji da 'yan sanda da kwastam da sauran mukamai na siyasa. Irin wannan abin da Biya ya yi wallahi shi wannan shugaban namu yake aiwatarwa, amma abin mamaki duk mun zura ido muna ji muna gani ana yi mana wa-kaci wa-tashi. Lallai mu hadu mu hada karfi da karfe wajen ganin mun ce bamu yarda da wannan cin-kashi da wariya da ake nuna mana ba. Irin wannan zunubi da Shugaban kasa yake aikatawa babu inda zai kai kasarnan sai ramin halaka da da-nasani. Tabbas idan bamu tashi mun farka ba, to nan gaba mu da 'ya 'yanmu wallahi sai dai karfin Imaninmu ya kwacemu a hannun abokan gabarmu. ALLAH YA KIYAYE.

YASIR RAMADAN GWALE
13-1013

Friday, October 11, 2013

SHEIKH (Dr.) MANSUR IBRAHIM SOKOTO: Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

 
SHEIKH (Dr.) MANSUR IBRAHIM SOKOTO: Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

Idan akwai wani Malamin Sunnah wanda kai tsaye zaka ce 'yan Shiah suna kwana da tararrabin bankado irin abinda miyagun litattafansu suka kunsa dan ankarar da al'ummar Musulmi illa da mugunya da ke tattare da wannan ADDINI na Shiah to kai tsaye zaka iya cewa shi ne Dr. Mansur Sokoto. Hakika, Malam Mansur Sokoto ya yiwa Addinin Allah hidima wajen bankado irin miyagun aqidun 'yan Shiah dan Ilmantar da al'umma da nuna musu irin mugun hadarin da yake tattare da 'yan Shiah da kuma shi'anci, Malam ya kutsa cikin tafka-tafkan litattafan 'yan Shiah da suke dauke da guba mai karya garkuwa da lalata tsiga da lakar jikin Imani na hakika, Imani na kadaita ALLAH da Bauta da cikakken Tauhidi.

Manya manyan litattafan Shiah, musamman littafinsu mafi tsarki da girma, wato AL-KAFI wanda daya daga cikin miyagun Malamansu wanda akayi a tsakanin karni na 3 zuwa na 4 wato KULAINI, wannan littafi shi ne mafi girman littafi a wajen 'yan Shia na da da na yanzu, sababbinsu da tsofaffinsu; kuma Shi ne mafi girman wani littafi da ya kunshi sharri da kararirayi da makirci da kutunguila da tufka da warwar akan Sahabban Manzon Allah tsarki ya tabbata a garesu, Malam Mansur ya kutsa cikinsa, inda ya tsiraita kusan kafatanin hujjojin da suke rakitowa daga cikin wannan littafi suke takama da dagawa da su.

Malam Mansur Sokoto ya shahara wajen bayyanawa al'ummar Manzon ALLAH SAW cewa duk inda kaga 'yan Shiah a duniya sun siffanta da wasu suffofi guda uku, wadannan suffofi sune JAHILCI, MAKARYATA NE sannan kuma MASU CANZA GASKIYA NE, wadannan su ne manyan siffofin da zaka iya gane duk inda dan Shiah yake. Dan Shiah duk girman rawaninsa da girman Alkyabbarsa sai ka same shi da irin wadannan siffofi manyansu da kananansu, na farkonsu da na karshensu. Alhamdulillah, da daman al'umma sun fahimci 'yan Shiah yanzu, domin kullum wadannan siffofi kara bayyana suke yi a garesu.

Tarihi bai gushe ba yana tabbatar da duk wasu maganganu da aka fada akan 'yan Shiah, domin tarihi ya shaide su da yin karya, da batar da sawun gaskiya, da canza hakikanin gaskiyar lamura zuwa wasu abubuwan daban, kuma su din mutane ne masu kambama wani abu da bai kai ya kawo ba, dan rudar da al'ummar Musulmi,Kuma tarihi ya shaidesu wajen dakushe gaskiya, da nuna rashin kimarta da rashin bata muhimmanci. Duk wannan abubuwa ne da suke a zahiri wanda tarihi ya shaidi 'yan Shiah da su.

Malam Mansur Sokoto hakika, mutum ne mai saukin kai da taqawa da kamun kai, ga kula da zumunci, duk wanda ya san Malam Mansur Sokoto ya sanshi da zumunci da kaunar 'yan uwa Ahlussunnah. Malam Mansur Sokoto ya yi hidima ainun wajen bayyana miyagun Aqidun Shiah ya kuma rubutu kasidu da litattafai da dama akan haka, Kasidun da ya rubutu a cikin turancin Ingilishi da Hausa ba za su lissafu ba. Haka kuma, ya rubuta litattafai da dama dan bayyanawa al'umma su waye 'yan Shiah, kadan daga cikin muhimman ayyukan da Dr. Mansur ya yi akwai fassara katafaren littafin nan na Ibn Taymiyya na Min-Hajis-Sunnah zuwa Harshen Hausa wanda ya zuwa yanzu babu wani Littafin Hausa da aka taba bugawa da yakai girmansa duk fadin kasarnan, akwai da dama daga cikin litattafan Malam da suka dade a hannun al'umma suna karantawa kamar KUBUTACCEN KARBALA, KADDARA TA RIGA FATA, SU WAYE MASOYAN AHLULBAITI da sauransu da dama, wadan da ba'a kai ga bugawa ba.

Hakika a wannan zaminin da muke ciki musamman a Najeriya ta Arewa idan akwai wani Zararren Takobi da yake yawon a saman kan 'yan Shiah suka firgita suka dimauce suka rasa ina gabas take to la-shakka shi ne Malam Mansur Sokoto. Allah ya taimaki Malam, ya sanyawa rayuwarsa Albarka, ya tsawaita rayuwarsa dan amfanar Addinin Musulunci. Allah ya sanya masa Albarka a cikin zurriyarsa da dukkan lamuransa baki daya. Na tabbata wannan ban fadi komai akan Malam Mansur Sokoto ba, da dama idan sun samu dama zasu yiwa al'umma cikakken bayani sama da wanda na rubuta akan irin hidimar da wannan Bawan Allah ya yiwa Sunnah.

YASIR RAMADAN GWALE
11-10-13

Thursday, October 10, 2013


MUNA KIRA GA GWAMNATIN KANO TA GAGGAUTA KORAR ALI BABA FAGGE

Kalaman da aka ruwaito Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge yana yi akan Malaman Addini cin fuska ne ba wai ga Malaman Addini ba har da Gwamnatin Kano. Hakika damuwa ta kai damuwa, a ce daya daga cikin Mashawartan Gwamna wanda ya kamata yafi kowa taka tsan-tsan da kokarin bin Addini sau da kafa shi ne yake furta irin wadannan munana kalamai masu zubar da kima da mutunci da haiba, wannan abin kaico ne, abin assha ne, abin Alla-wadai ne. Bayanai sun nuna cewar ba wannan ba ne karon farko da shi wannan mutum ya taba yin irin wannan gagarumar katobara ba, a baya ma ya taba yin maganganu masu kama da haka, rahotanni sun same mu cewar Hukumar Hisbah karkashin Jagorancin Mal.Aminu Ibrahim Daurawa ta ja hankalin wannan mutum akan abinda ya fada kuma har ya nuna damuwarsa akan kuskuren da ya yi, da nuna cewa a gafarce shi sharrin shaidan ne.

Abin mamaki sai gashi a jiya ya sake maimaita irin kalaman da ya yi, har ma yana kama sunan kwamandan Hisbar a matsayin daya daga cikin wadan da yake kira da su dinga sayan fina-finan Hausa dan karin samun gogewa wajen yada da'awa. Wannan cikakken rashin mutunci ne da nuna kaiwa maqura wajen nuna dan isakanci da tsageranci da jahilci da gidadanci da kidahumanci da toshewar kwakwalwa. Haka kuma, wadannan kalamai tamkar ya kwancewa gidansu da danginsu zani ne a kasuwa cewar basu bashi wata tarbiyya ta Islama da duk d'a nagari yake samu daga Iyayansa ba.

Lallai muna kira ga Mai girma Gwamna Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ba tare da wata-wata ba ya fito ya nesanta kansa da wadannan munana kalamai na mai bashi shawara ta fuskar Addini, kuma ya gaggauta sallamarsa daga wannan mukami. Dan mutum irin wannan da yake maganganu da suka yi kama da na mai tabin hankali bai kamata a ce shi ne zai baiwa Gwamnati shawara a Addinance ba. Muna nuna bakin cikinmu da damuwarmu da kaiconmu akn wadannan miyagun kalamai da wannan mutumin ya yi. Allah ya raba wannan Gwamnati da mutane irinsu Ali Baba miyagu fandararru masu kafurcewa gaskiya.

Muna yi masa addu'ar Allah ya shirye shi. Amma tabbas wadan nan kalamai zasu jima suna yi mana ciwo a duk sadda muka tuna su.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

Wanne Ne Maganin Musulunci Wanne Na Kafurci?

WANNE NE MAGANIN MUSLUNCI WANNE NA KAFURCI?

Allah SWA bai halicci wata cuta ba face sai da ya halicci maganinta kamar yadda Malamai suka gaya mana. Manzon Allah SWA da kansa ya yi bayanin wasu cututtuka kuma ya yi bayanin maganinsu, haka kuma, Manzon Allah ya bayar da wasu addu'o'i a matsayin garkuwa ta musamman ga wasu cututtuka. Cuta ma'anarta tana da fadi, rashin lafiyar jiki cutane, rashin lafiyar Imani ma cutane, shafar aljanu da dangoginsa duk cutane, dan haka duk wadannan cututtuka babu wata cuta da aka ce ta Musulunci ce ko ta kafurci, kamar yadda Musulmi zai iya kamuwa da kowacce irin cuta haka ma wanda ba Musulmi ba zai iya kamuwa da kowacce irin cuta. Sai dai fa irin garkuwar da manzon Allah SAW ya baiwa Musulmi kamar Azkar na safe da yamma, da Hailala da Salati da karatun al-qur'ani, da sauransu wannan garkuwa ne ga Musulmi.

A saboda haka, babu wani maganin wata cuta da mutum zai ware ya alakanta shi da Musulunci ya nuna duk wanda ba shi ba na kafurci ne, ko da kuwa idan ansha za'a samu sauki. Shaidan ya yi magana manzon Allah SWA ya ce abinda ya fada gaskiya ne, amma shi din makaryaci ne, dan haka ko kafiri ya yi magani sai ka dauki maganin ka barshi da kafurcinsa. Malamai sunyi bayanin cewar duk wani magani da binciken Likitoci ya tabbatar da cewar yana maganin cuta kaza to Wannan maganin ya halatta Musulmi ya yi amfani da shi, matukar ba ayi amfani da wasu sinadarai da suka sabawa Musulunci ba, kamar Alhanzir da sauransu.

Yana da kyau al'umma su fadaka, kada wasu masu tallar magani su dinga yaudararsu da cewa magani kaza na MUSULUNCI ne, sabaninsa kuma na kafurci ne. Da yawan masu tallar irin wadannan magunguna akan samu marasa tsoron Allah su dinga fadawa Mutane zuma da man zaitun da habbatus Sauda da dangoginsu sune maganin Musulunci sabaninsu kuma maganin Nasara ne, eh Musulunci bai hana yin amfani da maganin Nasara ba. Duk wanda ya fada maka haka ya yaudareka, kamar yadda zuma take magani haka bincike na likita ya tabbatar da cewa Kafenol da dangogin Maganin Bature suna yin magani.

Babban kuskure ne mutane su dauka akwai wani kantin saida Magani ISLAMIC CHEMIST, duk wani dakin sayar da magani matukar an gwada maganinsu an samu sauki to shima Islamic chemist ne, ko da kuwa wanda ba musulmi bane ya yi maganin. Kamar yadda na fada a baya, cuta bata da alaka da addini haka shima magani. Kirista zai iya amfani da Man-zaitun ya sha ya samu sauki, kamar yadda Musulmi zai iya amfani da Paracetamol ya sha dan ya samu sauki, babu inda aka ce ya sabawa addini dan ya sha maganin bature.

Yana da kyau mutane su yi tattalin lafiyarsu. Duk mara lafiya kamata ya yi a kaishi asibiti likitoci su gwada shi su san ciwon da yake damunsa, da kuma irin maganin da ya dace da shi, amma wasu kanyi kuskure kawai daga ciwo ya kama su sai su samu irin wadannan masu magungunan su yi ta dafka musu wasu abubuwa da ka iya tsananta ciwon da yake damunsu a matsayin magani, tunda babu wasu gwaje-gwaje na kimiyya da suka yi wajen gane cutar da kuma maganin da ya dace da ita. Haka kuma, mafi yawan irin wadannan magungunan dace ne kawai, domin wani yana iya shan hulba da Habbatus Sauda su yi masa magani wani kuma su tsananta cuta a gareshi. Wasu marasa tsoron Allah sai su fake da yiwa mutane wa'azi da fadin Allah ya ce Annabi yace, daga karshe kuma su b'uge da tallar magani da tallata hajojinsu.

Duk maganin da binciken kimiyyar likitoci ya gano cewa yana magani ya halatta a yi amfani da shi, matukar ba zai cutar ba, ko kuma baya dauke da wani abu da Musulunci ya haramta kamar giya, dan haka, kada kawai dan kana fama da ciwon "sugar" wani ya ce kaje ka yi ta shan Hulba da zaitun da sauransu ba tare da ya gudanar da kwakwaran bincike na kimiyya akanka ba. Eh gaskiya ne Hulba da sauransu duk suna maganin cututtuka, amma ba daidai bane wasu su dinga Yaudarar mutane da sunan cewa Magani kaza shi ne na Musulunci koma bayansa kuma na kafurci ne. Da maganin Bature da sauran zuma da Hulda da na 'yar me ganya duk sunansu magani, duk wanda bincike ya nuna cewa yana magani to shima ISLAMIC MEDICINE ne idan akwai wani magni da aka kebance da Musulunci. Allah ya sa mu gane.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

Wednesday, October 9, 2013

Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?


Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?

Najeriya ita ce kasa ta biyu a duk fadin nahiyar Afurka da ta yi fice wajen samar da irin tumatur mai kyau. Allah ya bamu albarkar kasar noma da tana iya dacewa da yanayin kowanne irin abin shukawa tun daga 'ya 'yan itace da dangin hatsi da kayan lambu da sauransu. A baya can Najeriya na samar da tumatur wajen tan miliyan 1.14 duk da cewa binciken masana ya nuna cewa Najeriya zata iya samar da fiye da tan Miliyan biyar na tumatur a kowacce shekara, wanda zai iya wadatar da Afurka da wasu kasashen gabas ta tsakiya. Amma kusan yanzu kullum harkar noman tumatur armashin ta raguwa yake yi, kasantuwar babu wasu masana'antu a Arewa da suke sarrafa danyan tumatur dan a zuba shi a cikin gwangwanaye da lodoji da saurin mazubai dan amfanin yau da kullum na harkar girke-girke. Kasantuwar duk kasarnan a Arewa ne aka fi yin amfani da tumatur a sha'anin girke-girke.

Da yawan manoman tumatur da masu kasuwancinsa na yin harkar ne cikin tararrabi da fargabar samun riba ko faduwa kasa warwas. A lokacin da ake tsaka da kakar tumatur a jihohin Arewa zaka ga yadda manoma ke yin roronsa kwando-kwando kai ka ce gaba daya Arewa Tumatur kadai ake nomawa, amma mafiya yawancin Manoman tumatur sun dogara ga kudancin Najeriya ne domin yin kasuwancinsa, mota-mota ake yi  ana daukar tumatur daga Arewa zuwa kudancin Najeriya. Wani abin mamaki shi ne, akwai lokacin da a Arewa zaka nemi jan tumatur sama da kasa ka rasa, gaba ki daya babu shi, kodai sabo bai karaso ba, wanda aka noma a baya kuma tuni aka yi kasashen kudu da shi.

Wadan da harkar tumatur ta yi musu kyau su ne wadan da suka yi sa'ar kai shi kudancin Najeriya ba tare da ya lalace ba. Domin duk mutumin da ya yi rashin sa'ar yin lodin tumatur a dai-dai lokacin da aka samu budewar rana kwal, to sai dai wani ba shi ba, domin kafin a isa ga inda aka nufata tumaturin ya narke ya tsiyaye, da yawan manoman tumatur sun sha tafka asara ta irin wannan hanya, wasu manoman da dama sun zautu wasu ma sun haukace saboda asarar da suka yi ta irin wannan hanyar. Haka kuma, ansha samun sabani ga direbobin daukar tumatur din da manomansa musamman wadan da suka yi rashin sa'a, wasu su loda tumatur din ganin asarar da suka yi su gudu su bar direba da jogoguwa, shi kudinsa bai fito ba, ga kuma dole sai ya nemi inda zai zubar da ragowar rubagen a can kudancin Najeriya.

A baya a Arewa muna da kamfanonin tumatur a IKARA da KURA da kuma DADIN-KOWA amma yanzu duk sun zama kangwaye. Masana'antun sun mutu murus, dan haka dole manoma su nemawa tumatur din da suke nomawa kasuwa a yankin kudancin kasarnan, abin mamaki kasar kudu da basa iya samar da ko da koren tumatur, sune yanzu haka suke da kamfanonuwan tumatur din da galibi ake yin girki da shi a Arewa, Jihohin Legas da Ibadan sune kadai inda suke da kamfanonin sarrafa tumatur, suma basu dogara da kasuwancin da suke daga Arewa ba, domin bayanai sun nuna cewar Najeriya na shigo da markadadden Tumatur din da ba'a sarrafa ba daga Chana na kimanin Naira Biliyan 12 a kowacce shekara. Wanda masana harkar lafiya suka tabbatar da cewa babu wani sahihanci na ingancin nikakken tumatur din da ake shigo da shi Najeriya a cikin dururrukan da suka jima suna galudaya akan ruwa.

Yanzu da masu kudinmu da gwamnatocinmu zasu taimakawa Manoman tumatur da tayar da kamfanonin Kura da Ikara da suka mutu da alal akalla, za'a samarwa da dubban matasa aikin yi. Duk da cewar rahotanni sun tabbatar da cewar Alhaji Aliko Dangote yana yunkurin samar da katafaren kamfanin sarrafa Tumatur a garin Kura, wannn yunkuri idan har yaci nasara hakika babban cigaba ne, kuma wannan zai sanya da yawan manoman tumatur da suka watsar da harkar su koma mata, da kuma samar da karin sabbin manoman tumatur.

Amma saboda rashin kamfanonin da suke sarrafa tumatur din a Arewa, haka nan miliyoyin tumatur suke halaka bayan ankai wasu kudancin kasarnan anyi kasuwancinsu cikin kasada, wasu kuma haka nan manoman kan yayyanka su suke shanyawa akan tituna da rufin gidaje. Allah ya nuna mana lokacin da za'a samar da sabbin kamfanonin sarrafa tumatur da kuma tayar da komadar wadan da suka kwanta dama.

Yasir Ramadan Gwale
09-10-2013

Tuesday, October 8, 2013

Dan Giya


DAN GIYA: Ina zaune naji wasu mutane suna labarin cewar duk dan giya ya fi kowa dacewa da samun matar aure ta kirki. Suka ce zaka samu mafiya yawancin 'yan giya, idan sun sha sun bugu su yi ta yiwa matansu amai suna zazzaginsu amma matan na hakuri, kuma suna nuna soyayya a garesu. Wannan maganar ta shiga kunnena sosai.

Wannan ya tuna min da wata waka da wani mawaki ya raira mai suna ZAMA NA AURE, inda yake cewa "Zama na aure yana da dadi yana da daci . . ." Mawakin ya bayar da wasu labarai guda hudu a cikin wakar tasa, a labari na uku daya bayar ya yi kama da abin da naji wadannan mutanan suna tattaunawa akan dan giya. Ga abinda wakar ta ke cewa:

Zama na Aure Yana da dadi yana da daci maáurata ashe soyayya da dadi…

Shi ko Gambo kunga dan giya ne

Sai can dare zai dawo gida nai

Da rangaji zai shigo gida nai

Ta kasa barci matarsa zaune

Bugu na kofarsa ma dabanne

Ta je ta bude ya yi shigowa

Da ya shigo zai fara hararwa

Ruwa ta debo tai tsabtacewa

Yana ta zaginta da dadawa

Ita ko kwalla take zubarwa

Kullum nasiha take gare shi

Dan ilimi gunta kwai yawan shi

Dan ilimin addini akwai shi

Sannu a sannu a kwan-a-tashi

Ya nutstsu tsaf-tsaf idan ka ganshi

Ya daina shaye ya canza halinshi

Gambo ai soyayya da dadi…..

Wannan labarin shakka babu ya yi kama da abinda naji wadannan mutane suna tattaunawa. Haka kuma, akwai wani mutum da na sani shi da kansa ya bani labari cewar a lokacin da yake shan giya, matarsa har wanka take yi masa, ya zageta ya fasa mata kaya amma bata damuwa, tana nuna masa soyayya tana masa Wa'azi da Nasiha. AMMA ME YA SA 'YAN GIYA SUKE DACEWA DA MATAN KIRKI?

Sunday, October 6, 2013

Wani Sabon Salon Tayar Da Tarzoma Da Su Zazzaky Suka Bullo Da Shi

WANI SABON SALON TAYAR DA TARZOMA DA SU ZAZZAKY SUKA BULLO DA SHI

Shugaban 'yan harka El-Zakzaky da mabiyansa, sun bullo da wani sabon salo na tayar da rikici a kasarnan. A yau da yawan shafukan 'yan Shia mabiyan zazzaky sun dunga bayar da sanarwar tayar da fitina, inda suke bayyana cewar 'yan shia za su shiga garin Sokoto a yau, dan haka ana kira ga duk wasu Ahlussunnah da su fito dan kare unguwanninsu, dan su hana 'yan Shia wucewa. Wannan sanarwa 'yan Shi'ah suka dinga bayarwa, dan jan hankalin wasu mutane daga cikin Ahlussunnah marasa kangado dan su fusata su fito dan hana 'yan shi'ar wucewa, inda zasu dinga takalarsu da fada, daman haka suke jira sai su yi amfani da wannan damar wajen tayar da tarzoma, kafafan watsa labari masu kishirwar labarin tashin hankali su yi ta bazawa dan kasar ta hargitse, Allah ya kiyaye.

Zakzaky bai damu da duk wani rikici da zai janyo sanadiyar halakar 'yan shi'ah ba ko su nawa zasu mutu. Domin yasan 'ya 'yansa suna can a kawwame, ya kaisu Amerika suna can suna rawa da su Lady Gaga, a kashe dan uban kowa bai damu ba, dan babu nasa. Idan ka duba yadda Zakzaky ya kira mabiyansa da sunan tattaki a kafa daga nisan duniya su zo inda yake, zaka san dagaske wannan mutumin ba kaunar mutanansa yake ba, a garin tafiya wasu suka dinga mutuwa a hanya, wasu motoci suka dinga markadesu, amma babu abin da ya dameshi saboda babu 'ya 'yansa a ciki.

Ahlussunnah mutane ne masu son zaman lafiya. Baya daga cikin aqidar Sunnah daukar doka a hannu, duk kuwa yadda lamura suka kai ga tabarbarewa matukar akwai hukumomi. Hakkin hukuma ne karewa tare da tsare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa. Tunda 'yan shiah suke yawace-yawacensu a kasarnan, Ahlussunnah basu taba tare musu hanya ba, balle su neme su da tashin hankali wannan ya sabawa manhajin Sunnah, hakki ne na hukumomi su bayar da dama ko su hana ga duk wanda ya fito yana ragaita akan titi da sunan ko ma meye.

An kashe mana Malamin da muke so muke kauna bamu tayar da hankali ba, sai wasu kananan kwari zamu tarewa hanya! Idan da mu masu tashin hankali ne, da jikin uban kowa ya gaya masa lokacin da aka yi mana ta'addanci a ranar 13 ga watan Afrilun 2007 a unguwar dorayi a Kano. Amma saboda mu al'ummah ce mai tsari da bin dokoki, da biyayya ga hukumomi babu wanda muka dungurewa kai, ko kaza bamu buge da sunan daukar fansa ba.

Dan haka duk wasu wadan da suke kiran Ahlussunnah da cewa su fito dan hana 'yan Shiah ragaitarsu su sani wannan sanarwa bata da alaka da Sunnah. Bama daukar doka a hannu mu sanya wani ko mu hana wani yin wani abu, sai dai fa idan abinda yake yi barnace ko fasadi da hukumomi suka ki daukar mataki.

Ko zazzaky ya sani ko bai sani ba, ballantana ma yana sane cewa ana amfani da shi wajen tayar da husuma a kasarnan. Suna son duk yadda za su yi su haifar da yamutsi a kasarnan da za'a yi amfani da shi a kama na kamawa ko a kashe na kashewa, ko ma kasar ta tarwatse. Muna tuna musu fadin Allah ta'ala cewa "WAMAKARU WA MAKRULLAH WALLAHU KHAIRUL MAKIREEN" In Sha Allah duk wani mai burin kawo hayaniya da tashin hankali aniyarsa zata bishi, kuma In Sha Allah sai yaji kunya. Allahumma Alaika Bihim . . . Allah ka kare bayinka na gari a duk inda suke. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale
06-10-2013

Shiekh (Dr.) Bashir Aliyu Umar: Kwararren Malamin Sunnah!!!

SHEIKH (Dr.) BASHIR ALIYU UMAR: KWARARREN MALAMIN SUNNAH!!!

Yana daga cikin baiwar da ALLAH yake yiwa bayinsa kebantattu, shi ne ya hore musu bai ta ilimi. Hakika, Allah ya yiwa Dr. Bashir Aliyyu Umar baiwa ta ilimi a fannoni da dama, bayan kasancewarsa Injiniya ne, kuma kwararren Malamin kimiyyar Hadisi ne. Malam ya karanta Ilimin Hadisi da kimiyyarsa a Jami'ar Musulunci ta Islamic University of Madinah tun daga matakin Degree na farko har zuwa Degree na uku inda Malam ya yi Kimiyyar Hadisi wato (PhD, Hadith Sciences).Allah ya yiwa Malam Bashir hikima da kaifin kwakwalwa, da sanin hukunce-hukuncen da suka shafi Ilimin Fiqhu, Allah ya bashi hazaka, da iya warware mas'aloli cikin hikima da ilimi.

Bayan kasancewar Dr. Bashir kwararren Malamin Sunnah, Malam Marubuci ne na Hausa da Turanci, domin ya rubuta litattafai da dama wasu anbuga su tuntuni wasu kuma ba'a kai ga buga su ba. Malam ya rubuta litattafai da daman gaske kamar The Methodology of Imam Ahmad regarding the inconspicuous weaknesses of hadith narrations, Garkuwar Musulmi ta Addu'o'i daga Alkur'ani da Sunnah; Hausa translation of Hisnul Muslim Min Adhkaaril Kitaab was Sunnah, Na Dr. Sa'eed bin Wahf Al Qahtani, Useful Ways of Leading A Happy Life, Fadakarwa Kan Hukunce-Hukunce da suka kebanci Mata Muminai. Wadannan su ne kadan daga cikin irin dumbin litattafan da Malam Bashir ya rubuta a cikin Ingilishi da Hausa, bayan haka kuma, akwai wasu litattafai da Malam ya rubuta wadan da ba'a kai ga buga su ba kamar: Between the Companions and Members of the Household of the Prophet, may Allah bless him and grant him peace, 55 rules regarding the inconspicouos weaknesses of hadith narrations and their applications among the scholars of hadith (an original work), Takhreej Nusoos 'aml ahlil Madinah fil Muwatta wal Mudawwanah da sauransu da dama.

Malam Bashir kwararre ne wajen sanin Ilimin Aqeedah, ya yi fice sosai a wannan fage, haka kuma masani ne a sauran fannoni Ilimai da dama, kuma masanin siyasar duniya, kuma Masanin Tattalin Arziki Bisa koyarwar Shar'ah, uwa uba kuma Malam Bashir Mahaddacin AlQur'ani ne, Ya Salam! Malam Bashir Mutum ne mai kan-kan da kai ga tawalu'u, yana girmama ilimi yana kuma girmama malamai masu Ilimi. Watarana, wasu al'amura guda biyu sun faru akan idona, Na farko wani ya zowa da Malam Bashir da wata fatawa, amma sai ya tambayi meye ra'ayin abokinsa Dr. Muhd Umar akan wannan fatawa. Abu na biyu kuma, wani ya tambayi ra'ayinsa dangane da kalaman da Barack Obama ya yi a lokacin da ya kai ziyara kasar Masar ga Musulmin duniya, a lokacin Dr. yace mu saurara muji ra'ayinsu Sheikh Dr. Yusuf Qardawi tukuna. Wannan ya kara nunamin irin yadda Malam Bashir yake taka-tsantsan da Ilimi da kuma girmama maganganun Manyan Malamai.

Malam Bashir mutum ne wanda duk mutumin da Mu'amala ta hadasu da shi, sai ya fadi alkhairinsa da kirkinsa, da kaunarsa da jama'a. Mutum ne salihi, Allah ya bashi baiwar iya rike sunayan mutane, Yau zaku yi Mu'amala da Malam, Insha Allah bayan shekara guda idan ka dawo zai ambaci sunanka, bai cika manta suna mutanan da ya yi mu'amala da su ba. Allah ya bashi wannan baiwar.

Sannan kuma, Malam Bashir kusan yana daga cikin mutanen sahun gaba wadan da suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin tabbatar Bankin Musulunci a Najeriya. Da shawarwarinsu da maganganunsu da hangen nesansu wannan alkhairi ya tabbata da dumbin al'ummah ke cin mariya a yanzu. Hakika Malam Bashir yana daga cikin kalilan din mutane da Allah ya yiwa tarin baiwa mai yawa da dumbin hikimomi. Na tabbata idan da za'a tara mutum goma da suka san Malam Bashir zasu yi rubuce-rubuce mabambanta wajen bayanin waye Malam Bashir. Tabbas Dr. Bashir Aliyu Umar kwararren Malamin Sunnah ne a wannan zaminin a Najeriya ta Arewa. Sautinsa bai tsaya iyakar Arewacin Najeriya ba, wajen kira zuwa ga Allah da Tauhidi, sautinsa ya karade kasarnan da sauran kasashen Afurka da Asiya da Gabas ta Tsakiya. Allah ya sakawa Malam Bashir da alheri, ya sanya albarka a cikin rayuwarsa da iliminsa da zurriyarsa. Allah ya yawaita mana irinsu.

Yasir Ramadan Gwale
06-10-2013