Monday, July 29, 2013

SUNA YIWA MANDELA FATAN HALAKA BASU SANI BA!!!


SUNA YIWA MANDELA FATAN HALAKA BASU SANI BA!!!

Allah mai girma da daukaka ya fada a cikin littafinsa mai tsarki cewa duk wanda ya kyautata, shima Allah zai kyautata masa, wannan magana da Allah ya yi gamammiyace ga duk wanda ya kyautata. Idan ya kasance mai Imani ne watakila Allah ya sanya wannan abin ya zama sanadiyar shigarsa Al-Jannah. Haka kuma wanda ya munana kishiyar haka na nan na jiransa. Allah ya ka bamu ikon kyautatawa, ka sanya a kyautata mana.

Bisa hukuncin Allah ya sanya Aljannah babu mai shigarta sai mai Imani. Allah ya tanadi Aljannah dan wadan da suka yi Imani kuma suka bi dokokinsa sau da kafa kuma basu ketare iyaka ba, wajen yi masa bauta, Subhanahu wata'ala. Idan wanda ba musulmi ba ya kyautata ya yi abin kirki da alkhairi bisa hukuntawarsa Subhanahu wata'ala sai ya tsawaita masa rayuwarsa ta duniya ko da kuwa a cikin wahala da tashin hankali yake yinta, domin halin da yake ciki a gidan duniya ya fi masa sauki sama da abinda zai tarar na Narko da Allah ya yi tanadi ga duk wanda basu yi Imani ba. Alhamdulillah bisa wannan ni'ima ta Musulunci.

Nelson Rolihlahla Mandela, dattijo ne mai farin gashi, gabbansa sunyi rauni, shekarunsa sun tafi, yayi ban-kwana da kuruciya da samartakarsa, dan-danon bakinsa ya salance, fatarsa ta yamushe, ganinsa ya ragu, tafiyarsa da maganarsa duk sun canza, ga rashin lafiya da ta ci karfinsa! Ya Salam. Duk wani mutum dan Afurka ko koma ba dan Afurka bane inda yana nan a raye ba shida bukatar a yi masa fassarar waye Mandela. Allah ya jarrabi Mandela da san fafutukar kwatowa bakar-fatar kasarsa 'yancinsu da aka danne aka maida su ba kowa ba a kasarsu ta haihuwa, aka take musu hakki, aka ci zarafinsu, aka wulakanta su. Tarihi zai jima yana shaida irin wannan kokari da Mandela ya yi wajen ganin al'ummar kasarsa da suke rayuwa tare sun samu sa'ida a cikin wannan rayuwa mai cike da kalubale.

Mandela ya sha dauri da muzgunawa watakila har da duka da kyara, duk akan waccan fafutuka tasa. Dauri kam ko huhun goro ba zai nunawa Mandela shan tamka ba, ya kwashe tsawon shekaru a gidan yari a daure laifinsa kawai shine yace bai yarda da muzgunawar tsirarun turawa fararen fata akan mafiya rinjayen bakaken fatar Afurka ta kudu ba. Wannan ta sanya har duniya ta zo karshe mutanan kudancin Ifriqiyya zasu cigaba da nuna jinjina ga wannan dan tahaliki, tare da yi masa fatan alheri, watakila har da yi masa fatan samun kyakykyawar rayuwa bayan mutuwarsa, wanda wannan shine fatan da ba zai taba samu ba, matukar ba yayi Imani da Allah da Manzon Allah bane kafin cikawarsa! Hakika mutum irin Mandela dole ka tausayawa rayuwarsa bayan mutuwarsa, ganin irin yadda ya karar da samartakarsa da kuruciyarsa wajen Bautawa al'ummarsa da fatan ganin sun samu cikakken 'yancin yin walwala kamar sauran jama'a a fadin duniya, zaka tausaya masa ne, saboda ba shida wani rabo a gidan Lahira! Hasbinallahu wani'imal wakeel.

Tun da aka kai Mandela asibiti a 'yan makwannin da suka gabata jama'a da dama a fadin duniyar nan suka kasa kunne su ji cewa Mandela ya rigamu gidan gaskiya; amma cikin hukuntawarsa Rabbul-Izzati bai karbi rayuwar Mandela ba tukuna. 'Yan jarida da dama suka je bakin asibitin da aka kwantar da shi suka kasa suka tsare kowannensu na jiran a ce Mandela ya kwanta dama, dan ya kasance wanda ya riga kowa bayar da labarin, wasu ma har sun fara azarbabin cewar Mandela din tuni ya tunkuyi kasa, amma daga bisani sai rahotanni suce yana numfashi bisa taimakawar Na'u'rori.

Amma dai a bayyane take a garemu cewar wannan rayuwa ta wahala da jinya da Mandela yake ciki itace mafi sauki a gareshi sama da rayuwa bayan Mutuwa da kuma abin da za'a tarar ranar Gobe kiyama. Kaicon rayuwar Mandela! ya sha wahala, an daureshi, an muzguna masa, duk anan gidan duniya, shin tsammaninka idan ya mutu zai samu kyakykyawar rayuwa a gidan lahira? Allah ka sanya mu kasance wadan da kayi tanadin Al-Jannah dominsu.

Yasir Ramadan Gwale
29-072013

No comments:

Post a Comment