Monday, July 22, 2013

SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [5]


SHUGABA UMAR HASAN AHMAD AL-BASHIR: ZAKIN AFURKA [5]

Bayan da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya ya yi wata tattaunawa ne akan abinda yake faruwa a Dafur, Kwaryar Majalisar dinkin duniyar karkashin jagorancin Ban ki-Moon suka amince su hada kai da kungiyar kasashen Afurka ta AU domin neman hanyar da za’a tura sojojin kiyaye zaman lafiya a yankin Dafur. A ranar 5 ga watan mayun 2006, aka cimma wannan yarjejeniya tsakanin UN da AU. An amince akan cewar kungiyar kasashen Afurka zasu tura sojojin karo-karo dan aikin da suka kira kiyaye zaman lafiya karkashin kulawar Majalisar dinkin duniya. Inda Majalisar dinkin Duniyar zata bayar da dukkan kudaden da ake bukata wajen aikin, sannan kuma ta nada Mohamed Ibn Chambas dan kasar Ghana a matsayin Manzon musamman da mai taimaka masa Joseph Mutababa dan Rwanda a yankin na Dafur.

Gwamnatin Khartoum itama a nata bangaren ta bayar da hadin kai wajen aikin samar da dawwamammen zaman lafiya. Inda aka samar da katafariyar Sakatariyar United Nation Mission in Dafur (UNAMID), amma ko da aka yi wannan Hadaka tuni anci karfin ‘yan tawayen Dafur, ta yadda baka ganin komai a Dafur sai konannun gine-gine da rusassun wurare. Amma duk da haka aka dinga bayar da rahotannin yakin na cigaba tsakanin Gwamnatin Khartoum da ‘yan tawaye da kuma Janjaweed, wanda wannan ma karya ce tsabage ake shararata domin daurewa ‘yan sa’idon majalisar dinkin duniya gindi su cigaba da kasancewa a yankin na Dafur.

Ashe akwai wata kudundunanniyar manufa ta Majalisar dankin duniya wanda kowa yasan Amurka da kasashen Turai ke sarrafa akalarta. Abin da suka yi kuwa shine tuni kafin turo masu aikin zaman lafiya da bayar da kayan agaji da suka hada da barguna da garin fulawa da sabulu da man girki, sun turo wasu turawa wadan da suka iya Magana da larabci, aka kuma warwatsa su cikin yankin na Dafur dan wancan aikin da suka kira na bayar da agaji, amma babban aikin da suka fi mayar da hankali shine “yada addinin kirista a tsakanin mutanan Dafur”, wannan al’amari ni ganau ne akan haka. Domin kuwa turawan sun zo da tarin dubban faya-fayan CD mai kunshe da wa’azin kiristanci cikin harshen larabci inda suka dinga shiga kauyuka suna tara kauyawa suna haska musu wadannan faya-fayai a majigi, tare da rarraba musu kasa-kasan CD na wa’azin kirista da suke dauke da hoton gicciye baro-baro.

Samun wannan labari na kokarin yada addinin kirsta tsakanin mutanan Dafur da sunan cewa ana raba musu kayan agaji da kuma aikin jin kai ya sanya gwamnatin Khartoum ta nemi juyawa al’amarin baya! Domin a karon farko gwamnatin Khartoum ta bayar da umarnin binciken dukkan akwatuna da kwantainonin Majalisar dinkin duniya da aka shigo da su kasar kafin isarsu yankin Dafur, wanda kuma kamar yadda yake a dokar Majalisar dinkin duniya dukkan wasu kaya na UN ba’a bincikensu ko menenen kuwa, amma shugaba Bashir yayi mursisi yace ko Ban Ki-Moon ne yazo Sudan sai an caje shi, ba wai kayan UN ba, wannan al’amari bai yiwa majalisar Dinkin duniya dadi ba, musamman kasashen Turai da Amurka, a dalilin haka aka dinga maida wasu kayan inda suka fito wasu kuma Gwamnatin Khartoum ta hana musu isa yankin na Dafur.

Daga bisani abin ya rincabe inda Shugaba Bashir yace shi fa daga yanzu kungiyar tarayyar Afurka kadai zai yarda da ita a yankin Dafur, inda yace ya baiwa Majalisar dinkin duniya wasu awanni su tattara yanasu-yanasu su fice su bar Sudan. Nan dai ana wannan sabatta juyatta ne Majalisar Dinkin duniya suka bullo da wata dabara ta tattara neman taimako domin sake gina yankin Dafur da yaki ya dai-daita a cewarsu. Anan aka yi amfani da kasashen Larabawa wajen rarrashin shugaba Bashir inda ya yarda da wannan bukata, ya kuma baiwa majalisar ta dinkin duniya iznin sake bude Ofishinsu a Sudan, amma dai dokar binciken kayansu bai janye taba.
Daman kuma kamar yadda gaskiyar lamari take shine Dukkan wata harka ta Diplomasiyya harka ce da take kunshe da munafurci fal cikinta, abu ne da za’a dinga yi cikin nuku-nuku da kumbiya-kumbiya da kin bayyana gaskiyar lamura yadda suke, sai dai a boye, kuma kowa na cin dunduniyar kowa.

A watan Nuwamban 2010 aka cimma yarjejeniyar tara taimakon da za’a sake gina yankin na Dafur a birnin Doha na kasar Qatar inda shi kansa Sarkin Qatar ya kasance na gaba-gaba wajen nemo wannan taimako. Inda ya karbi alhakin karbar bankuncin duk wani taro da za’a yi a Doha domin yadda za’a tattara wannan taimako. Majalisar dinkin duniya da AU da kuma Arab League da Gwamnatin Qatar da Gwamnatin Khartoum suka zauna domin shirya yadda tsarin abin zai kasance. Da sunce baza su mika taimakon zuwa ga gwamnatin Khartoum ba, da suna ji tsoron mika taimakon da aka samu zuwa wajen gwamnatin Khartoum dan gudun kada a karkata akalar kudin ba yadda aka tsara ba. Inda ita kuma gwamnatin Khartoum ta shata layi akan cewa zata bari a sake gina yankin amma bisa sharuddan banda giggina wuraren da ta haramta kamar dandulan shakatawa da zai dinga kunsar jama’a mata da maza da mashaya da gidajen kallon fina-finai da sauransu, sai dai samar da famfunan tuka-tuka da hanyoyi da dakunan shan-magani da sauransu. An amince da hakan, amma kamar yadda muka fada duk wasu harkoki na Diplomasiyya karyace da yaudara da cin dunduniya a cikinta shi ya sa ita kanta gwamnatin Khartoum din bata tsaya ta zuba ido a samo kudi azo ayi mata abinda aka ga dama ba, a gefe guda kuma suma manyan kasashen da suke son ganin bayan Shugaba Bashir suna ta nasu aikin na ganin yadda za’a ciyo logarsa, a kwashe masa kafafu ba tare da ya ankare ba. Akwai wani batu mai muhimmanci sshine na yadda aka yi amfani da ICC wajen kama shugaba Bashir da laifukan yaki. . . . . . . . . . . . . Insha Allahu zan cigaba.

Yasir Ramadan Gwale
22-07-2013

No comments:

Post a Comment