LABARIN AUREN ALH. ISYAKU DA AMARYARSA NABILA MAI
SHEKARU 15!
Watana rana a jami’ar Bayero muna zaune da yamma
bayan an tashi daga karatun Hadisi wanda Dr. Ahmad (Qala-Haddasana) yake
gabatarwa, a Majalisar su Alhaji Isyaku ne na samu wannan labari, dalilin
tattauna wannan al’amari kuwa ya biyo bayan wani Hadisi da Malamin ya karanta
akan Aure da zamantakewar Iyali, inda Malam yayi dogon sharhi akan hadisin tare
da kawo misalai masu yawa dangane da halin da rayuwar aure take ciki a kasar
Hausa, da kuma irin yanayin yadda rayuwar yara ‘yan matan wannan zamanin take.
Bayan da muka zauna ne ake sake tattauna wannan batu
na yara kanana, sai aka bijiro da labarin auren Alhaji Isyaku da Nabila ‘yar
Alh. Muhammad Ahmad. Wata rana, Alhaji Isyaku suna hira da abokinsa Alhaji
Muhammad sai yake bashi labarin cewar shi yana burin auren yarinya mai kananan
shekaru dan yana son gwada bata tarbiyya irin wadda yake so ba wadda aka dora
ta a gidansu ba, Alh. Isyaku ya baiwa abokinsa labarin tare da dalilai masu
kwari da yake son yin wannan aure; ashe maganganun sun shiga kunnen Alh.
Muhammad sosai da gaske, yana gama bashi labarin kawai sai yace da shi “to
indai haka ne me zai hana ka auri Nabila ‘yar wajena” Nanfa Isyaku yayi jugum
yana tunanin irin yadda abokinsa yayi saurin martaba wannan ra’ayi nasa, ba
tare da wani bata lokaci ba suka amince dan kulla wannan aure. Alhaji Muhammad yace
ina zaton shekarun Nabila ko dai 14 ko 15 bazata wuce haka ba.
Nan da nan, bayan Alh. Muhammad
ya koma gida ya kirawo diyarsa Nabila yayi mata huduba akan yadda al’amuran
wannan rayuwa suke da maganganu na dattako masu ratsa zukata, bai bayyana mata
hukuncin abinda suka yanke shi da abokinsa ba, sannan ya kira mahaifiyarta ya
sanar mata irin hukuncin da ya yankewa ‘yarsa; da farko mahaifiyar Nabila ta
nuna rashin amincewarta da wannan aure, amma daga bisani Alh. Muhammad ya shawo
kanta cikin hikimar Magana da bata labarin yadda al’amura suka dagwalgwale a
wannan zamanin, ya kuma tabbatar mata da cewa Nabila zata cigaba da karatu a
gidan mijinta, idanma tana tsoron karatun yarinyar zai yanke.
Alh. Isyaku shi kuma yana da Matan aure guda biyu da
‘ya ‘ya mata cikinsu kuwa har da wadda ta shiga Jami’a. shima a nasa bangaren
ya sanar da matansa cewar zai kara aure ya kuma gaya musu shekarun yarinyar
inda matansa suka hade masa kai akan cewa sam ba zai auro musu ‘yar cikinsu ba
a matsayin KISHIYARSU, nan dai yayi barazana irin tasa ya kuma tabbatar musu da
cewar ba gida daya Nabila zata zauna da su ba, domin samun saukin kishi, haka
nan dai suma suka saduda. Ba tare da dibar wani lokaci ba aka daura wannan aure
da mutane sukai ta tsegumi akansa.
Bayan an gama aure amarya ta tare a sabon gidan da
mijinta ya gina mata. Kamar yadda yake bisa ga al’ada, idan ango zai kashe
daren farko da iyalinsa yakan yi dan cefane na kayan dadi ya shiga da su dakin
amarya, shima haka Alhaji Isyaku yayi inda ya hadowa Amraya DANASHA, ya kuma
kunna kai cikin dakin amaryarsa, bayan da ya shiga ne ya nemi su yi alwala su
yi sallah domin godewa Allah akan wannan aure nasu, suka yi sallah kuwa, suka
fara cin kayan dadi Bankararrun kaji ne da lemuka da ‘ya ‘yan itatuwa iri-iri.
Ana haka, bayan sun yi hani’an, sai Alhaji Isyaku ya
shiga batu babu kakkautawa, inda ya dauki dogon lokaci yana yiwa Amarya
nasihohi da kuma jan hankalinta a matsayin sabuwar matar aure da zata shiga
wata sabuwar rayuwa ta musamman. Bayan da ya gama yi mata wannan Nasiha ne, a
tunanin Alh. Iysaku ita Nabila yarinya ce yana da kyau a barta ta d’an samu
sakewa, kafin ta fara sabawa. Kawai ya cire babbar rigarsa ya gyara wajen da
suka ci abinci, amarya na kan gado ta sunkuyar
da kai, sannan ya dauki Pillow ya ajiye a kasa kan kafet, ya kashe fitila ya kwanta, ya bar
Amarya a saman gado ita kadai!
Can bayan wani lokaci Alhaji idonsa biyu, yana jin
lokacin da Amarya ta tashi sadaf-sadaf ta d’an kintsa, a zatonsa kunya take ji
shi ya sa take sand’a, dan haka sai ya yi lamo kamar yayi barci, yace yana ji
tazo kansa tana lekawa taji ko barci yake, bayan wani kankanin lokaci kawai sai
jin yarinya yayi ta zo ta kwanta a kusa da shi kamar mage! Nan
zuciyarsa ta raya masa anfa zo wajen… amma duk da haka sai yayi kamar yayi
barci, kawai, sai ji yayi an fara kunce masa tazugen wando . . . . . . . . . .
. . . . . . .! Alhaji Isyaku yace hankalinsa ya tashi matuqa, domin Nabila bata
ji kunyar cewa shi abokin mahaifinta bane, kuma shi yana kallonta yarinya
karama kamar da sauranta wajen fahimtar yadda al’amuran aure suke, ashe
tunaninsa ba gaskiya bane.
Inda hankalinsa ya tashi, shi ne, tunaninsa yana da
yara ‘yan mata guda uku wadan da duk sun girmi Nabila a shekaru, nan fa ya kasa
samun sukuni, yana ta sake-saken yadda al’amuran wannan zamani suka kasance
haka, yace idan har Nabila yarinyar da bata wuce shekaru 15 ba zata kasa jure
dare guda na tarewarta ina ga sauran ‘ya ‘yana su Karima da Shamsiya da Salma
da take Jami’ah! Lallai abin ya bashi tsoro ainun.
Wa shegari da ya je gidan sauran matansa, ya kirasu
akan cewar ya basu watanni uku su shirya bikin ‘ya ‘yansu uku. Sannan ya kira
yaransa yake sanar musu cewa ya basu takaitaccen lokaci kowacce a cikinsu ta
fitar da mijin aure, idan kuma ba haka ba kuwa, to su sani acikin abokansa
akwai masu son kara aure!
Ya mai karatu wannan labarin fa ba shaci fadi bane,
haka abin ya kasance, illa iyaka kawai sunan mutanan da na sauya. Mu kalli
yadda al’amarin Alhaji Isyaku da Nabila ya wakana, sannan kuma mu duba batun da
ake na cewa WAI kada ka aurar da ‘yarka sai ta haura shekaru 18 da haihuwa.
Lallai da sake! Ai laururar da zata sanya ka ki aurar da ‘yarka a kananan
shekaru shine rashin samun miji, amma indai ta samu to aurar da ita shine
babban abinda ya dace. Allah ka shiryemu ka shirya mana zurriyarmu da
al’ummarmu baki daya.
Yasir Ramadan Gwale
24-07-2013
No comments:
Post a Comment