SHIEKH (DR.) ABDULHAIY YUSUF: ALLAH BAYA TOZARTA MAI
GASKIYA
Sheikh Dr. Abdulhaiy Yusuf, wani hamshakin Malamin Sunnah
ne dan asalin kasar Sudan
mazaunin kasar Abu-Dhabi a yankin Larabawa. Sheikh Abdulhaiy Allah ya hore masa
karatun Al-Qur'ani, ya haddace Qur'ani da dukkan ruwayoyin (Kira’o’i)
Al-Qur'ani guda bakwai, yana iya karanta al-qur'ani da dayan bakwan Kira’o’insa
cikin Tajwidi da murya mai dadin saurare. Allah ya sanya masa takawa da kankan da kai, ga
rayuwarsa cike take da abubuwan koyi. An tambayi AbdulHaiy Yusuf cewa ko ya
haddace Litattafan Kutub-As-Sitta bai amsa cewa ya haddace su ba, amma kuma
yace duk hadisin da ka kawo masa sai ya fada maka a cikin babin da hadisin yake
da maruwaicinsa da tarihin sahabin da ya ruwaito hadisin. Hasbinallahu
Wani'imal wakeel! Wannan wata baiwa ce da Allah yake baiwa wasu mutane kalilan
daga cikin al'umma, kuma wannan Tawalu’u ne irin na Shiekh AbdulHaih Yusuf.
A kasar Abu-Dhabi da Sheikh Abdulhaiy yake limanci a
wani katafaren Masallaci, wani muhimmin al-amari ya auku. Domin daya daga cikin
manyan sarakunan kasar ne ya rasu kuma ya bar dumbin dukiya mai tarin yawa,
bayan rasuwar Basarken ne, Iyalan sarautar kasar ta Abu-Dhabi suka kira Sheikh
AbdulHaiy akan ya raba Gado amma bisa tsarin yadda suka tsara, anan shehun
Malami AbdulHaiy ya sanar da su cewar Shi gado Allah ne ya rabashi da kansa,
dan haka babu yadda shi a karankansa zai raba gado sabanin yadda Allah ya raba.
Anan aka yi kiki-kaka, sarakuna suka nemi Sheikh Abdulhaiy
ya bi tsarin da suka raba gadon wajen tabbatarwa da jama'a. Ya amsa musu da
cewar idan har kun san kun raba kayanku to babu bukatar ku zo wajena, domin kun
riga kun gama
raba gadonku kuma meye nawa a ciki.
A ranar wata juma'a Sheikh AbdulHaiy Yusuf yayi wata
Khudba a masallacinsa, cewar yana samun matsin lamba daga hukumomin kasar akan
rabon gado na son rai da ake son yayi, ya kuma tabbatar da cewar ba zai yi
wannan rashin gaskiya ba. Gama Hudubarsa ke da wuya aka bashi awanni kasa da 48
akan ya fice ya bar kasar an koreshi, Allahu akbar.
Allah gatan bawansa, Sheikh AbdulHaiy Yusuf ya kama
Hanya zuwa kasarsa ta SUDAN.
Dawowarsa ke da wuya, wani hamshakin Attaijiri daga kasar Abu-Dhabi ya zo ya
same shi, ya ce masa ya fadi inda duk yake son a gina masa masallaci a ko ina
ne shi mutumin zai gina daga Dalar Amerika daya har zuwa Dalar Amerika Miliyan
Goma! Ya Salam! Kaji hukuncin Ubangiji, da yadda al’amarin rike gaskiya yake
daukaka mutum.
Wannan attajiri ya ginawa Sheikh AbdulHaiy Yusuf
wani katafaren Masallaci a birnin Khartoum,
Masallaci mai hawa uku, an kawata masallacin yadda yayi daidai da dukkan wasu
manyan masallatai na duniya, sannan ya gina masa wani katafaren gida mai hawa
uku, da sabbin motoci na alfarma domin duk dan Shiekh ya cigaba da da’awar yada
Addinin Allah. Yanzu haka Shikeh AbdulHaiy yana daga cikin Manyan Malaman
Sunnah kuma jagoran Ahlussunnah a kasar ta Sudan.
Haka al’amarin gaskiya yake idan ka tsaya a gareta
baka bi son zuciya ba Sai Allah ya daukaka ka ta sanadiyarta. Ya Allah ka bamu
ikon tsayawa akan gaskiya komai tsanani.
Yasir Ramadan Gwale
26-07-2013
No comments:
Post a Comment